Chapter 76
Chapter 76
baice komai saboda b'acin rai, ji yake kamar ya kashe Mabrookah ya huta, hannayensa ya saka a aljihu tare da sakin huci mai zafi. Areefah ta zumb'uro baki "Ai wallahi bazan yarda bah, wallahi ta k'ara maimaita makamancin haka dukan tsiya zan mata" Ran Abba ya b'aci, ya daka ma Areefah tsawa abinda bai tab'a yi bah "Karna k'ara ji" Ta sake shagwab'e fuska ta kauda kai. Suna nan har ta farka daga baccin, sunata mata sannu har abin ya bata kunya ganin harda Abba a wajan da kuma yanda gaba d'aya suka nuna damuwarsu a kanta. Ba kunya Jamal ya zauna kusa da ita ya d'an rab'ata da jikinsa sai k'okarin k'wacewa take ta kasa, shiko gogan ko a jikinsa. Ammi na ganin haka ta mik'e daga kan kujeran datake, "To bari muje gida mudai" Ummy najin haka ta tura baki tana kallan Jamal "Nifa ba inda kemin ciwo dan Allah a sallameni" Bai iya mata musu ba ya mik'e yace ma su Ammi yana zuwa, wajan likitan yaje ya rok'esa ya sallamesu, X-ray aka rubuta musu da kuwa wasu magunguna sannan yace su bari drip d'in dake jikinta ya k'are. Godiya yayi ya koma, yana zuwa ya samu su Ammi sun wuce sai Areefah dake d'akin tanata ma Ummyn hira itako sai dariya take cike da nishad'i, Yanda ta damu da Wife d'insa yasa ta sake samun gurbi a zuciyarsa, ya k'araso ya shaida musu yanda sukayi da likitan. A b'angaren Mabrookah kuwa tana ganin su Ammi sun fita ta fashe da wani matsanancin kuka, sai lokacin kalmar Jamal dayake anbata mata kalmar saki ya dawo mata k'wakwalwarta. Ta sake rushewa da kuka, chan kuma ta mik'e kamar wacce aka tsikara, ta goge hawayenta ta nufi bedroom d'inta dasauri. Drip d'in na k'arewa aka sallamesu suka dawo gida, Ammi dake falon tana jiransu tana jin shigowan motan ta fito dasauri ta rungume Ummyn tana mata sannu, Hannunta ta kama tana cewa "Banasan wani tashin tashina, zo muje d'akina" Jamal ya turo baki gama harda doka k'afa d'aya a k'asa sam ba haka yaso bah, Areefah dake kallansa ta kyalkkyale da dariya ya galla mata harara, ciki sukayi yana binsu a baya har lokacin bai maida bakin bah. Ganin sun haura sama yasa ya zauna a falo yana cika yana batsewa, Kan gado Ammi ta zaunar da ita tana cigaba da mata sannu "Kiyi Hak'uri Jaleelah kinji" Murmushi kawai tayi ta duk'ar dakai k'asa, Ammi ta shiga toilet ta had'a mata ruwa mai d'an zafi ta umarceta taje tayi wanka. Cikin daran nan nan nan da Ummyn Ammi ta dunga yi sai dataga tayi bacci hankalinta ya kwanta. Tana saukowa ta samu Jamal kwance kan 2seater bacci ya d'aukesa, murmushi tayi ta k'arasa ta tab'asa tana cewa "Jamaludeen a nan kake bacci, maza tashi kaje ka kwanta" Ya bud'e ido dakyar "Ammi ina Wife" Duka ta d'aka masa ya bud'e ido dakyau yana muzurai "Maza je ka kwanta, karna dawo na sameka a nan" Ta haura sama ta barshi nan. Da Asubah Abba ya sauko dan tashin Areef zuwa masallaci, a d'akin ya samu Jamal kwance kan Tiles yana bacci abinsa hankali kwance, Mamaki ne k'arara a fuskanshi ya k'arasa ya soma tashinsu, Areef ma yayi mamakin Ganin Jamal d'in a d'akin. Tare suka tafi masallacin su uku. K'arfe takwas na safe duk sun hallara a falon before ayi breakfast, Ummy na zaune k'asa kan carpet kusada k'afar Ammi itada Areefah, Haka Jamal shima zaune kusada Abba, Abba yayi gyaran murya ya soma da cewa "Wannan zaman yakamata ayishi da d'ayar matarka, saidai kafin tazo inaso nayi magana akan abinda ya faru Jiya" Jamal ya duk'ar dakai dan yasan dashi za'ayi, Abba ya juya garesa fusaka ba yabo ba fallasa yace "Da Mabrookah da Jaleelah duk matanka neh, duk sadaki ka biya ka aurosu koh?" Jamal dake gefe ya gyad'a kai kamar kad'angare kansa k'asa "Sam banji dad'in abinda ya faru bah jiya, idan rai ya b'aci bai kamata hankali ya gushe bah. Yakamata ka tsaya kayi alk'alanci kafin ka zartar da hukunci. Anma zartar da hukunci cikin fushi babu abinda yake haifarwa sai danasani" Ya numfasa yace "Baka kyauta ba sam Jamaludeen" Ammi dake gefe tace "Saki nawa ka mata?" Kansa k'asa yace "Biyu!" "What!" Cewar Abba ransa a b'ace "A haka kakesan mu zauna a nan gidan" Ya d'ago idanunsa cike da kwalla yace "Abba dan Allah kayi hak'uri!" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Areefah jeki kiramin Mabrookahn" Ta mik'e tana zunguro baki ta fita, Side din ta shiga ga mamakinta yanda falon yake jiya haka ta samesa, ta tab'e baki "Sai shegen k'azanta" Knocking ta soma a k'ofar bedroom d'in shiru ba amsa tafi minti goma a tsaye taja tsaki ta banko k'ofan ta shiga. Batsa batsa ta samu d'akin kayan wardrobe duk a k'asa da sauran tarkace. Ta taka tana yatsine fuska har Toilet d'in nan ma ta dunga bugawa ba amsa. Har zata fito idanunta suka sauka kan wani Farin takarda mai d'auke da rubutu da aka d'aurama Kwalbar humra. D'auka tayi ta soma karantawa _Kayi ma iyayena k'azafi hankalinka bai kwanta bah, ka..._ Tayi saurin dakatar da karatun ta fita dasauri zuwa d'ayan side d'in. Tana shiga tace "Abba ban ganta ba saidai naga wannan takardan" Ta mik'a masa ya duka na 'yan mintina sannan ya mik'ama Areef yace ya karanta kowa yaji _Kayi ma iyayena k'azafi Hankalinka bai kwanta bah, ka d'auko wasu mutane dan suci dukiyar Abba wai kai Iyayenka, to ka sani alhakin Iyayena bazai tab'a barinka bah. Sannan indai Ummy ce wallahi baku isa ku zauna lafiya bah, badai saboda ita ka sakeni bah? To wallahi baku ba samun Farinciki indai ina raye. Na tafi na bar muku waje ku shak'ata saidai ku jirayi dawowata.A_ Daga Matarka abar sonka Mabrookah. Areef na gama karantawa yaja dogon tsaki "Abba kagani koh? Ni dama wallahi tunda na ganta sam batamin bah" Kasa cewa komai Abba yayi Ammi tace "Areefa kuje keda Ummy sama kuyi breakfast sannan kuyi sauri dan 10 za'a shiga Court gashi 9 yanzu" Ta kama hannun Ummyn suka haura sama zuwa d'akin Ammin, suna shiga Ummy ta zauna bakin gado ta fashe da kuka, Areefah ta zauna kusada ita dasauri tare da dafa kafad'arta "Haba Aunty Ummy ki daina kuka, insha Allahu babu abinda Mabrookah ta isa ta miki wanda Allah bai miki bah" Ta saki murmushin takaici "Nasan Halin Mabrookah sarai akan abinda takeso tana iya komai Areefah" Areefah ta soma share mata hawaye "Oh! Stop crying Allah ya fita" Bata sake cewa komai ba sai kukan data cigaba, Breakfast d'insu Areefah ta d'auko musu, ba yanda batayi akan Ummyn taci ba taki, saima kwanciya datayi wani mugun zazzab'i ja neman rufeta. A falo kuwa su Areefah na haurawa Ammi tace "Gaskiya Alhaji inasan rayuwar d'ana dana matarsa. Banasan abinda zai tab'asu, cikin biyu gaskiya za'a zabi d'aya ko mu zauna dasu ko mu koma gaba d'aya abujan tare" Jamal ya karb'e da cewa "Abba Ammi dan Allah ku gafarceni ku yafemin abinda na muku". Abba yace "Babu komai anma kada hakan ta k'ara faruwa" Shiru ne ya biyo baya, Ammi ta sake cewa "Alhaji bakace komai bah har yanzu" "Ammi dama inso idan kun amince
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82