Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

a baya. Har lokacin Ummyn na zaune kan sallaya tana lazimi, yanda aka banko k'ofan ko ba'a fad'a ba tasan Mabrookah ce "Ke! Tashi" Ba musu ta mik'e ta koma baya tana kallansu, bincike suka soma ko ina, Mami dai na tsaye tana kallansu. Katifa Mabrookah ta d'aga sai ga sark'a kan katakon gado. Aunty Faty ta saki salati tareda d'auko sark'an tana nunama Mami "Tun ba'aje ko ina ba kin gani koh?, ai k'ila ba shi kenan bah" Kan kace me hawaye ya wanke fuskan Ummy sai kallansu take tana kuka sosai. "Wallahi Mami bani na d'auka ba, bansan yanda akayi yazo nan d'akin ba" Aunty Faty ta sake d'aga katakon gadon sai ga k'aramar b'akin jaka na Abba. Wannan karan Mami ce ta saki salati "Meya kawo jakan Alhaji d'akin nan? Dollar ne a ciki kud'in mutane" Nan ta sake rushewa da kuka ta matso inda Mamin take tana duba jakar "Wallahi tallahi Mami bani na d'au...." Kyawawan Mari guda biyu masu rai da lafiya Mami ta d'auke Ummyn dashi "Allah wadaran ki Ummy, ashe haka kike? Lallai gaskiyar mutane ne da sukace talaka bai iya samun guri bah. Tho wallahi yau zaki bar gidan nan" Ba shiri ta sake fashewa da kuka "Dan Allah kiyi hak'uri Mami, wallahi..." Wani Marin Mabrookah ta d'auketa dashi "Dole kibar gidan nan, dan ba gidan ubanki baneh" Mami tace "Dama ance idan kaga halin yaro to ka duba ta iyayensa, Uwa ko Uba an saba da sata. Kinsan ko dole itama ta koya" Ran Ummy ya sake b'aci ta d'ago tace "Mama na da Babana basa sata, haka nima ban tab'a sa..." Mami ta sake wanketa da mari, duka Mabrookah ta rufeta dashi, ko kad'an Ummy batayi niyan ramawa bah. Koran kare Mami da Aunty Faty suka mata ta fito daga gidan tana kuka sosai, ga dare yayi kusan k'arfe Goma da rabi. Jamal na karyo kwanan layin ya hango Ummy tafe tana kuka, ba shiri yaja birki ya fito dasauri. Ta ganashi ta bi ta wuce yanata kwalla mata kira ko waiwayowa batayi ba sai kuka datake yi. Binta ya soma yi hankalin shi a tashe yana kiran sunanta tareda tambayan abinda ya faru, juyowa tayi a fusace fuskanta ya gani yayi ja abinka da farar fata, gefen kumatun ta duk sun kumbura da shaidar yatsu. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:51 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Banida bakin godiya a gareku Masoyana, kun min komae. Ina alfahari daku kamar yanda kuke alfahari dani, ina matuk'ar sanku kamar yanda kuma kuke sona.* _Wannan shafin tukwuici ce gareku_ ```Sumaiyah Isah (k'awar arzik'i) Aysha Yusuf Aisha zagi Halimatu sa'adiya Meenah shuwa Canan Kabir (My swthrt) Mairo! Maryam sani Nafisah Jibril Yahanasu Bello (Your highness) Abdulhakam Idris Sultan Abba babaye``` _Da sauran wad'anda ban fad'a bah. Duk kuna raina ina sanku sosai.._ Page 28 to 30 Juyowa tayi a fusace fuskanta ya gani yayi ja abinka da farar fata, gefen kumatun ta duk sun kumbura da shaidar yatsu. "Ka rabu dani, bana san ganinka, kun cutar dani, baxan tab'a yafewa bah" "Pls Ummy ki tsaya, fad'amin me aka miki?" Ya rik'o hannunta tana ta k'okarin k'wacewa, fuskanta ya soma dubawa hankalinshi a tashe "Waya mareki?, Tel me pls" Batace mai komai ba, ta fizge da k'arfi ta cigaba da tafiya tana kuka sosai, ba irin rok'on da bai mata ba ko sauraransa batayi ba ta cigaba da yafiya. Haka ya hak'ura ya kyalleta badan ransa yaso ba ya hau mota ya nufi gida. Tafiya tayi mai nisa dak'yar ta samu mai Napeep ya d'auketa zuwa gida. Koda ta isa gida har Mama ta rufe k'ofar gida, bugawa ta soma tana kuka a hankali, Mama ta fito tana tambayan waye, cikin muryan kuka ta amsa mata, jin Ummyn neh yasa ta bud'e kofan da mamaki tana kallan Ummyn "Ummy lafiya da wannan tsohon daren" Kuka ta sake fashewa dashi ta rungume Maman, janta tayi suka shiga cikin gida bayan ta maida k'ofan ta rufe, suna shiga falo Baba ya dogaro sandarsa ya fito "Waye ne yake buga k'ofa, Aa! Kukan wa nakeji" "Kaga Mallan Ummy ce da wannan tsohon daren, sai kuka take ga kuma shatin yatsu a fuskanta" "Mene!" Baba yace yana rarraba ido kamar mai gani Mama ta d'agota tana share mata hawaye "Wai menene kiyi mana bayani mana" Wani sabon kuka ta fashe dashi sannan ta soma basu labari tiryan tiryan, Baba ya saki sallati yace "Ina! Ni shaida ce akan 'yata, baki sata Ummy, kuma nasan tarbiyan dana baki." Sosai ran Mama ya b'aci tace "Share hawayenki, Allah zai saka miki." Shiru Baba yayi ranshi ba dad'i, musamman dayanji Mabrookah da duki Ummyn. Dakyar suka lallabata ta shiga ta kwanta, duk da ba baccin zatayi ba sai kuka datake tayi. A b'angaren Jamal kuwa, yana isa gida ko k'wakwaran parking beyi ba ya shiga cikin gidan, Mami, Mabrookah, Aunty Faty dasu Twins ya samu cirko cirko a falo, ga mamakinsa Twins ya gani suna kuka, ya k'araso falon ransa b'ace yana kallan Mabrookah da alamar tambaya "Meya faru a gidan nan naga Ummy ta fita tana kuka, kuma da shaidar Mari a fuskanta" Aunty Faty ta turbune fuska "Ko zaka rama mata neh? Ai sai ka tsaya kaji abinda ya faru koh kamin kazo ka hayaiyak'o mana" Mami ta aje masa Jakan da aka gani a gabansa bayan ta bud'e dollars d'in dake ciki, ta aje masa sark'an Aunty Faty tace "Abinda muka gani kenan a d'akinta, kai kanka kasan bazan iya zama da b'arauniya a gidana bah" Najma tai saurin cewa "Ya Jamal wallahi Ummy bazata Iya sata bah, ni nasan..." Aunty Faty ta bige mata baki "Tho me kike nufi? Mun mata sharri kenan koh, ke kinsan halin talaka kuwa? Talaka shege neh" Ran Jamal ya k'ara b'aci yace "Mami bai kamata ki d'au wannan hukuncin bah, batare da kinyi bincike bah." "Wani bincike zanyi bayan na gani da idona, mu fa muka ciro kayan nan a d'akin" "Haba Mami, Haba! Wallahi baku kyauta min bah, Meyasa zaku min haka? Yanzu da wani ido zan kalli Iyayen Yarinyan nan. Mami I Love her! Ina santa so na gaske and i want to marry her" Mari Mami ta d'aukeshi dashi, ya dafe wajan tareda zaro ido yana kallanta, sai a lokacin ya tuna abinda ma yace. Aunty Faty ko ba shiri tayi zaman 'yan bori tana kallan Jamal d'in "Jamal a gabana kake fad'an irin wad'an nan maganan? Lallai wuyanka ya isa yanka. Ni! Ni Maimunatu?" Mabrookah ta fashe da kuka itama ta zauna wajan tana tuturje k'afa "Koda yake ba laifinka bane, ni nasan asiri suka maka. Ai duk abinda kakeyi kallanka kawai nakeyi, duk abinda kake musu inajin labari" Ta nunashi da yatsa "Wallahi ka shiga taitayinka, kuma kasani kaida Ummy har abada. Indai ina raye bakada matar data wuce Mabrookah. Wuce ka bani guri" Wani mummunan kallo yabi Mabrookan dashi sannan ya haura sama, Twins suma suka bishi dukansu ransu ba dad'i. Yanda Jamal yaga rana haka yaga dare, burinshi kawai safiya tayi ya tafi gidansu Ummy yaga yanda zasu kwashe. Ana sallan Asubah ya shirya ya fita daga gidan batareda kowa ya sani bah,

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82