Skip to content

Chapter 48

Chapter 48

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

Mama taji dad'in zuwansa, hira sukayi sosai kamar ba suruki bah, sai bayan Magriba sannan ya mata sallama ya tafi tanata saka masa Albarka. A masallacin k'ofar gidan ya tsaya yayi sallahn Isha'i sannan ya shiga gidan, yanasa k'afa a k'ofar Falon side d'insu gabansa ya fad'i tunawa da yayi yau Girkin Mabrookah neh. Itakuwa Hajiya Mabrookah yau a shirye take, saboda wani Pills da k'awarta ta bata a makaranta datakai mata complain d'in baya kusantar ta. Ko takan Maganin Aunty Faty batayi ba tunaninta kawai yanda zata zuba masa k'wayar a drink har tasamu yasha. A sanyaye ya shigo ciki da sallama ya soma takawa a hankali yana bin Falon Mabrookah da kallo, rungumesa yaji anyi ta baya ko ba'a fad'a masa ba yasan Mabrookah ce. Sabda baisan rigima a daran yasa ya birkito ta yana mata murmushi "Sannu da zuwa Honey tun dazu nake jiranka" Fuskanta dayasha makeup ya shafa yana cigaba da murmush, peck ta kai masa a kumatu kana wani shu'umin murmushi "Nasan ka gaji, shiyasa ta had'a maka ruwan wanka tun d'azu" Har lokacin ya kasa magana sai binda da ido yake kamar ranar ya soma ganinta, hannunsa taja har sama, Ummy suka samu a falon ta takure waje d'aya da alama tsoro takeji, kallo d'aya ta musu ta kauda kai, janshi Mabrookahn ta cigaba dayi har d'akinsa, ta aje briefcase d'insa akan bedside ta k'arasa inda yake tsaye yana cire agogon hannunsa, mab'allin gaban rigansa ta soma cirewa, sai hanata ba har ta cire ya rage farin singlet, hannu tasa ta cire belt d'in wandonsa, ganin baice komai ba yasa ta samu k'warin guiwa tasa hannu zata cire mab'alli Wandonsa, saurin rik'e hannunta yayi fuskarsa a d'aure "Meye kuma haka Mabrookah, ki bari mana ko nace miki ne bazan iya cirewa bah" Ta shagwab'e fuska ta sake matsowa kusada shi tana d'an murmushi "Kai Yaya, anfa ce yana da kyau mace ta rink'a taimakon jikinta" Guntun tsaki yaja ya matsar da ita gefe ya shiga toilet d'in ya danna key yanata mita cikin ransa. Tana ganin ya shiga ta doka tsalle tana dariya ta fita daga d'akin dasauri, har lokacin Ummy na falon a takure wannan karan hawaye ne ke fita daga idonta. Kallanta Mabrookah tayi ta kwashe da dariya, karairaya ta soma har ta k'arasa inda Ummyn zaune, ta rik'e k'ugu tace "Ke k'aramar 'yar bariki ce. Yau zan nuna miki ke ba komai bace, ki toshe kunnenki da runtse idanunki dan yau zaki sha mamaki" Cike da takaici Ummyn ke kallanta, wani k'ollolon bak'in ciki ya tokare mata mak'oshi, kasa ce mata komai tayi. Mabrookah ta sake kwashewa da dariya ta bar wajan tana rawa tana wak'a a hankali. Sauka tayi ta kwaso abincin data masa ta shiga dashi d'akin. Har lokacin bai fito bah, ta juya ta kalli k'ofar toilet d'in sannan ta ciro tablet d'in da k'awarta ta bata ta bud'e 5alive d'in data kawo ta saka guda uku ta jijiga ta rufe. Ta sake kallan k'ofan sannan ta mik'e dasauri ta fita ta mayar. Koda ta dawo bata tarar da Ummy a falon bah, tayi dariyar mugunta tareda k'wafa "Ke k'aramar mara kunya ce" Taja dogon tsaki ta shiga d'akinsa, zaune ta samesa kan gado daga shi sai towel a waist d'inshi da kuma wani a hannunsa yana tsane ruwan kansa. Cikin tafiyar jan hankali ta k'arasa ta amsa Towel d'in dake hannunsa tana cigaba da tsane masa. Ko uffan baice bah, gaba d'aya hankalinsa na wajan Wife d'insa dan yasan batayi bacci yanzu. K'okarin mik'ewa yake tayi saurin kama hannunsa cikin shagwab'a "Ina zaka kuma Honey gafa abinci na kawo maka" Kallan kulolin yayi tad'an yatsine fuska yace "Am Ok! Nayi attending wani walima kafin nazo" Tad'an turo baki ta d'au cup ta tsiyaya masa 5alive d'in ta mik'a masa "To ga wannan kasha tunda ka k'oshi" Bai mata musu ba ya amsa ya kai bakinsa, saida yasha kusan rabin cup d'in sannan ya aje. Murmushin mugunta tayi ta d'au trayn da fita tana tafe tana dariya k'asa k'asa. Harya mik'e zai shiga zaije wajan Wife d'insa dan itace a ransa. Wani jiri ne ya kamasa ya koma ya zauna dasauri tareda dafe kansa. Mabrookah ce ta shigo cikin wasu fitinanun kaya tana karairaya, kam cinyansa ta zauna tana shagwab'a duk da yanda gabanta ke fad'uwa "Honey yadai" D'agowa yayi ya kalleta har saida ta tsorata ganin yanda idanunsa sukayi ja, rungumota yayi jikinsa ya kwantar da ita kan gadon ya soma aika mata sak'oni masu wuyan fassara, duk abinda yakeyi da zafi zafi yakeyi saboda yanda ya kamu sosai. Mabrookah ba baka ba har kunne, an samu abinda akeso, nidai ina ganin haka nayo waje na basu guri. Ummy tsoro ne ya cikata, ga wani kishi daya dabaibayeta, k'udundune wa tayi cikin bargo ta rufe har kanta. Tsoro ne ya k'ara cikata dan duk sanda ta rufe idanunta b'arayin nan take gani sanda suka harbi Abba. A guje ta fito tana kallan bayanta, kuka ta soma mara sauti ta fito falonta ta kunna switch na wuta tahau kan kujera ta kwanta tana cigaba da kuka tana waiwayen bayanta. Kan 1seater ta koma ta kwanta tasake k'udundunewa tana kuka. A hankali a hankali ta soma jiyo ihun Mabrookah daga d'akin Jamal, wani kukan ta saki mai sauti ta soma wurgi da pillows d'in dake kan kujerun. Ranar batayi bacci bah har saida aka kira sallahn Asubah, dakyar ta mik'e a wajan ta shiga d'akinta ta fad'a toilet tayo alwala. Dakyar ta iya yin sujjada sbda yanda idanunta suka kukumbura. A b'angaren Jamal da Amarya Mabrookah kuwa, wuraren k'arfe uku ya sarara mata, ya fad'a gefenta yana maida numfashi, sam baiyi tunanin zai samu Mabrookahn a budurwa ba sai gashi ya sameta fil a leda. Albarka ya soma saka mata itako sai kukan shagwab'a take masa da k'ara narkewa a jikinsa. Da kansa ya mata wanka ya shiryata tanata masa shagwab'a, shima ya shiga wankan, ya fito ya tada sallah, nafilfili ya soma har aka kira sallan asubah ya sake alwala ya fita masallaci. Bai shigo gidan ba sai k'arfe bakwai da rabi, duk hankalinsa na wajan Wife d'insa, sauri yake yaje gareta tunawa da yayi bai dubata ba daran jiya. A stirecase sukayi kicibus da ita cikin shirin makaranta, fuskanta ya kumbura yayi ja abinda da farar fata. Ta gefensa zata rab'a ta wuce yayi saurin rik'o hannunta "Wife meya sameki a fuska" Kwace hannunta ta soma yi idanunta taf da hawaye "Ka sakeni na wuce, ka kyalleni" Kalmar datake ta fad'a kenan, da mamaki yaketa kallanta, ta fashe masa da kuka "Ni ka sakeni, ka kyalleni" Rungumota yayi jikinsa ta soma kici kicin k'wacewa tana dukansa a k'irji "Pls wife kiyi hak'uri, nasan nayi laifi. I donno what came over me har na dawo ban dubaki bah" Harzuk'a tayi dajin maganansa, wato ita zai rainama wayo, turesa tayi da duk iya k'arfinta ta fashe da kuka ta fita daga side d'in da gudu. Binta yayi yaga tayi side d'in Mami, slow yayi ya sauke ajiyar zuciya ya tsaya daga bakin side d'insa. A bakin k'ofan Side d'in Mamin ta tsaya saida tayi kuka mai isarta sannan ta goge hawayenta ta tura k'ofan ta shiga da sallama. A

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82