Chapter 28
Chapter 28
d'ago yana kallan Abban "Yadai naga kana kallona" "Abba mata kuma?" "Duk abinda kakeso nima ina sonshi my one and only son, tun sanda kace min kanasan Ummy na soma shige da ficen yanda zanyi ka mallaketa a matsayin matarka, munje dasu Alhaji Tahir anma kawun nan ta suka k'i. Shine Jiya da daddare na sake komawa na k'ara tambayan su. Nan sunk'i amincewa har saida na had'a da nuna dukiyata sannan suka aminta" Wani runguma Jamal yama Abba yana dariya "Thank uh! Thank uh!! Thank uh dad. Uh are the best dad ever" Peck yama Abba a kumatu yana mai nuna farincikinsa a fili, dariya Abba ketayi ganin yanda tilon D'an nasa keta murna da farinciki. "Saidai kar kabari su Mamin maka su sani har sai na kamalla wasu shirye shirye danakeyi" "To Abba insha Allahu" Kar kuso kuga yanda Jamal keta d'oki, waya ya d'auko ya soma neman layin Ramadhan cikeda farinciki kamar wanda akama bushara da aljanna. Da daddare Mami na side din Abba, ya mik'a mata cheaque yana cewa "So nake cikin gobe zuwa jibi ki had'o min kayan lefe masu kyau da kuma tsada, kamar set uku haka" Da fara'a Mami ta amsa tana dubawa, miliyan hud'u ta gani, ta washe baki "Ahh Lallai Alhaji kanaji da 'yar nan taka" Ya saki murmushi baice komai bah. Bayan ta koma side d'inta ta sanar da Aunty Faty yanda sukayi, Ihu Mabrookah tayi cikeda murna, haka Aunty Faty. Washe gari suka d'au hanyan lagos dan achan zasuyi siyaiyan. Kaya suka jifgo, har saida Mami ta kira Abba tace saiya k'ara kud'i, ba musu ya tura mata dubu d'ari biyar suka sake wata siyaiyar na kaya masu tsada. Kwanan su uku suka dawo gida. Sosai Abba ya yaba da kayan da suka siyo dan shima sun burgeshi sosai, a nan side d'inshi ya umarce su da su bar kayan, haka kuwa akayi suka bar kayan nan side d'in nashi. _kuyi managing wannan banda chargi_ Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* _*Alhaji Haruna Jumare Marad'in Zazzau's Family*_ Wannan shafin sadaukarwa ce gareku Page 32 n 33 A nan side d'inshi ya umarce su da su bar kayan, hakan kuwa akayi suka bar kayan nan side d'in shi. Da yanma Abba ya kira Jamal yazo dan yaga kayan, sosai ya yaba tareda godiya ma Abban. Har lokacin ya hana ya fad'a ma su Mamin abinda ke faruwa. Baba Sallau da Baba Tanko ne zaune a falon gidansu Ummyn, Mama da Ummy na gefen su zaune suna sauraran abinda su Baba Sallan zasu ce. "To saboda yanayi da sauyi da aka samu, an fasa d'aura auren da Iliya d'an wajena. Yanzu an d'aura da yaran da kuka turo" Ummy ta d'ago da mamaki tana kallan Baba Sallau "Wani yaro kuma?" Cewar Mama itama da mamaki "Ko Jamalu, ko mene" cewar Baba Sallau Baba Tanko yad'anyi dariya yace "Jamaludeeni sunansa" Gaban Ummy ya yanke ya fad'i, ta fashe da kuka. Itako Mama murmushi tayi cikeda farinciki tace "Babu komai Yaya, Allah ya saka da alheri, ya kuma sanya Alkhairi" Da kuka Ummyn ta mik'e ta shige d'akinta tana kuka. itama Mama ta mik'e tabi bayan Ummyn. Baba Sallau ya kyalkyace da dariya yana kallan Baba Tanko "Ai wannan abu yayi, da mun d'aura ma Iliya ba abinda zamu samu saima wahala dan mu zamu rink'a ciyar dasu" Baba Tanko yace "Gaskiya ne Sallau, yanzu ko kaga kowannen mu yanada Million d'aya nasa na kansa" Suka kwashe da dariya tareda mik'ewa suka bar Falon. Duk abinda suke tattaunawa Mama najin su, sai yanzu ta fahimci cin hanci Baban Jamaludeen d'in ya basu har suka yarda suka bada auren. Allah wadai tayi da halaiyar su Baba Sallau ta shiga d'akin Ummy a sanyaye. Kuka ta sameta tanayi kan gado bil hak'i da gaskiya, ta d'agota ta zaunar tana share mata hawaye "Haba uwata, kukan nan na menene? Ai wannan abin farinciki neh, yakamata ki maida komai ba komai bah. Kiyi hak'uri ki fauwala wa Allah. Ni inaji a jikina Jamaludeen Alheri ne a rayuwarki" "Mama Ya Bilal nakeso, dan Allah kice Ya Jamal yayi hak'uri." "Ummy kibi umarnin Yanin mahaifinki, ki zauna da Jamaludeen d'in tunda har an d'aura. Ba kuma abinda zamu iyayi. Kiyi biyaiya zakiji dad'in rayuwar aurenki" Ummy ta sake rushewa da kuka ta fita daga d'akin dasauri, gidansu Bilal ta shiga tana cigaba da kuka, Inna ta fito a rud'e tana tambayanta lafiya, Bilal ne ya fito daga d'akin Innan yana takawa da kyar da alama baida lafiya neh. Tsugunnawa tayi guyawu biyu a k'asa a gabansa tana kuka, "Ya Bilal karka bari a rabamu, bazan iya auren kowa ba sai kai. Dan Allah karka bari a rabamu" Baice komai ba saima sulalewa dayayi ya zauna a wajan saboda jikinshi da ba k'arfi. Inna ta d'ago Ummyn ta rungumota jikinta tana share mata hawaye "Ummy ki daina kuka, Allah ya riga ya rubuta Bilal ba mijinki bane. Ki d'au dangana, haka Allah ya k'addara" Ta sake rushewa da kuka ta zame ta zauna kusada Bilal d'in. Zama Inna tayi ta dunga musu nasiha sannan da kanta ta sab'a hijab ta raka Ummyn gida tareda yima Mama murnar auren Ummyn. Yau da wuri ango Jamal ya tashi daga wajan aiki, direct gida yayi ya fesa wanka ya sauya kaya zuwa manya, keyn motarsa ya d'auka ya nufi anguwarsu Ummy. Yana shiga anguwan aka fara kiraye kirayen sallan Magriba, parking yayi ya tsaya wani masallaci nan kusada gidan ya tsaya yayi sallan sannan ya k'araso. Yaro ya samu ya aika cikin gidan, chan ya dawo yace tana zuwa. Cikin zauren ya shiga ya tsaya, chan sai gata ta fito fuskan nan nata a d'aure. "Barka da fitowa Gimbiyata" Harara ta wurga mai tareda b'ata fuska "Haba Gimbiyata ba gaisuwa" K'eya ta juyamai, ya saki murmushi mai sauti tareda tura hannayensa cikin aljihu "I know tun ba yau ba baki sona, ban tab'a tunanin wata rana zaki zama mallakina bah, sai gashi. Ina sanki Ummy fiyeda yanda kike tunani. zan iya sadaukar da komai da nakeda shi matuk'ar zaki soni ki yarda ki zauna dani" Juyowa tayi tana kallanshi idanunta cikeda kwalla "Ka tabbata kana sona" Kai ya gyad'a mata yana cigaba da kallanta "Dan Allah dan san Annabi ka sakeni, idan kamin haka shine zan yarda da cewa kana sona. Wallahi Ya Jamal bana sanka ni Ya Bilal nakeso" Ji yayi kamar ta soka mai mashi a k'irji, ya d'ago muryar shi a sark'e yace "Wanene kuma Bilal" Kan tayi magana suka jiyo Muryan Bilal gaba bakin zauren yana cewa "Ni ne Bilal" Ya k'araso cikin zauren suna kallan Juna shida Jamal. Ran Jamal idan yayi dubu ya b'aci, baice komai ba har lokacin idanunsa nakan Bilal dake tsaye kusada Ummy "Tun bansan Wacece Ni bah Ya Bilal ke sona yake tausaya ma Rayuwar da muke ciki ni da Iyayena. Ina matuk'ar sanshi, haka shima yana sona. Dan Allah ka sawak'e min ka barni na auri wanda nakeso" Ta fashe da kuka ba shiri ta shiga cikin gida a guje. Bilal ya tako gaban Jamal wanda yayi mutuwar tsaye kamar gunki yana kallan Bilal "Mallan kayi k'okari ka kyale min budurwa tah. Dan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82