Chapter 32
Chapter 32
Mifzal ne zai d'aukemu ita kuma kai da kanka zaka je ka d'auketa" Juyowa yayi ya watsa mata mummunan kallo "Saboda ita Matata ce, hakk'inta tun sati hud'u da suka wuce ya dawo wuyana" "Wannan ai ba adalci bah, kamar yanda take matarka haka nima nake matarka" Ya tako zuwa gabanta yana cigaba da kallanta "Har yau ke ba matata bace, saboda ba'a daura bah. Idan kuma na k'arajin wani magana sai na fasa auren muga tsiya" Ya nuna mata k'ofa "Fitar min daga d'aki" Fuuuuu tabar d'akin rai b'ace kamar ta fashe da kuka. Wayansa dake kan bedside ne ya soma ruri, ganin numbern Najma yasa ya saki murmushi ya fito ya samu abokan nasa. Shi da Ram ne suka nufi gidansu Ummy, da kuma wasu daga cikin abokansa dan d'aukan sauran k'awayen Ummyn. Mifzal kuma dasu Taseem zasu d'au Mabrookah da k'awayenta. Daidai k'ofar gidan Inna sukayi Parking, numbern Najma ya soma kira ta d'auka tana cewa "Haba Ya Jamal tun fa d'azu muke jiranku" Saida yayi dariya sannan yace ku fito muna k'ofar gida. Najma ta gyara ma Ummy head d'in kanta tareda rik'o hannunta "To ku muje suna k'ofar gida." Ummy tad'an zaro ido tana kallan Laurat tana yatsine fuska "Ni fa wallahi wannan dogon takalmin ya isheni" "Haba karki badamu mana" Cewar Najwa. Najma na rik'e da hannunta har suka fito daga gidan, sauran k'awayen na take musu baya. Ram ya fito dasauri ya bud'e mata baya inda Jamal ke ciki, ba musu ta shiga ta sadda kanta k'asa ganin Jamal a cikin motan. Laurat ce ta shiga gaba, su Najma kuma suka shiga sauran motocin suka d'au hanyan Hall d'in da za'ayi dinnern. Tunda Ummy ta shiga ba abinda Jamal keyi sai aikin kallanta yana murmushi, kunya ne ya lullub'eta ta k'ara sadda kai k'asa tana wasa da clutch d'in hannunta. Hannunta ya kamo ya had'a da nashi ya d'an matse kad'an, kokarin k'wacewa ta soma yi. Yasa d'ayan Hannunshi ya d'ago fuskanta. Dasauri ta runtse ido saboda kunyarshi da taji tana ji sosai, motsowa ya sake yi har suna gugan juna, yakai bakinsa saitin kunnenta ya rad'a mata "Kinyi kyau sosai Pearl" Ta saki d'an murmushi har lokacin idanunta a lumshe. D'agowan da zaiyi suka had'a ido da Ram dake kallansu ta mirrown gaban motan "Ka kalli gabanka dai banasan gulma" Dariya Ram kawai yayi ya cigaba da driving suna hira da Laurat. Wayan Jamal ne yayi k'ara yasa hannu ya ciro, ganin Mifzal ne yasa ya d'auka ya kara a kunne "Mifzal ya akayi" Daga chan b'angaren yace "Wai kuna ina neh, muna fa nan k'ofar hall d'in tun d'azu muna jira, ga kuma Amaryar ka nan sai masifa take dan Allah kuyi sauri" Tsaki yaja sannan yace "Ba sai taita yi bah, ko so take muyi tsintsu muzo" Ya kashe wayan tareda sassauta rik'on dayama Ummyn, tana ganin haka ta zame dasauri ta matsa gefe. Su Aunty Faty dasu Mami da Aunty Zainab da sauran 'yan uwa da abokan arziki duk suna cikin Hall d'in da za'ayi Dinnern. Jin har lokacin Jamal bai tso ba yasa Aunty Faty ta had'e rai kamar zatayi bindiga, Mami ma ranta ya b'aci sosai da jin Jamal d'in ne da kansa yaje d'auko Ummyn. Basu iso wajan ba sai k'arfe bakwai da rabi lokacin har Mabrookah dake cikin mota ta gaji da jira. Ram na parking ya fito, Laurat ma ta fito. Najma ce ta bud'e side d'in da Jamal d'in ke ciki, Taseem kuma ya bud'e na amarya. A tare suka fito, Ummy kanta a k'asa kunya sosai ya rufeta musamman ganin Flash lights d'in cameras daban daban dake ta d'aukan su hoto. Laurat tayi saurin rik'e mata hannu ta jata zuwa inda Jamal d'in ke tsaye, Mabrookah ma ta fito itada k'awayenta, A tare suka soma jerawa Ummy na'a gefen damansa, shi yana tsakiya Mabrookah na gefen hagunsa. A bayansu K'awayen Mabrookah ne da abokan Ango sai su Najwa da Laurat. Nan da nan wajan ya d'au tafi, wajan zamansu da aka tanada dominsu suka zauna. Sosai Couples d'in sukayi kyau su duka, bama kamar Jamal da Ummy duk wanda ya kallesu sai ya k'ara kallansu. 'Yan jarida da masu hoto sai d'aukansu suke, hakan ba k'aramin bak'anta ran Mabrookah yayi bah. Bayan anci ansha aka umarci Amare da ango su taso su d'an taka. Wuf Mabrookah ta mik'e Ummy ko kasa tashi, Jamal ya rik'o hannunta ya d'agata, kanta ta sauke k'asa duk jinta take a takure a wajan. Hannunta ya kama sannan ya juya ya fizgo na Mabrookah suka sauko daga step d'in dake wajan. Wak'an su Psquare bank alert ke tashi, Mabrookah ta zage sai rama take, itako Ummy tsaye ta tsaya dan ita bata iya rawa bah koma ta iya bazata iyayi a gaban mutane bah. Jamal na yana d'an rausaya wa a hankali yana bin wakan dan yana san wakan sosai. Hannun Ummy ya kamo ya matso da ita sosai kusada shi, hannayenshi biyu yasa a k'ugunta ya zagaye yana cigaba bin wak'an yana murmushi. Ba k'aramin burge mutane sukayi bah, kan kace me wajan ya cika da 'yan lik'i sai ruwan nerori ake musu. Ran Mabrookah idan yayi dubu ya b'aci, dakyar Ummyn ta iya sa hannu ta ciro kud'in daya basa ta masa lik'i saboda kunya. Sanda akazo yanka cake ma saida Mabrookah tasha haushi. Anci ansha tareda raba kyaututuka masu yawa sannan kowa ya kama gabansa. Kamar wanchan lokacin Jamal da Ram ne suka maida Ummy gida da k'awayenta. Ita kuma Mabrookah Taseem ya maida ta gida. Washe gari kuma kamu, shima Anyi shagali kamar ba gobe, anyi taro lafiya an tashi lafiya duk da su Aunty Faty ransu a b'ace yake da ganin rashin kunyan da Jamal keyi k'iri k'iri yana nuna banbanci tsakanin Ummy da Mabrookah. Bayan an dawo Kamu su Ummy suka koma gidansu dan washe gari za'a kaita. Sai a lokacin Ummyn kejin Abba yace ya d'auke musu yi mata kayan d'aki shi zai yi mata komai. Tun a ranar ta soma kukan rabuwa da Mamanta da kuma Sahibinta Bilal. A ranar sati duban jama'a suka shaida d'aurin auren Jamaludeen Surajo da Amaryar sa Mabrookah Ismail a bisa sadaki dubu d'ari. Ango yayi kyau cikin farar shadda d'an daidai shi, rigan iya guiwa dan yace shi baya isa saka babban riga. Fuskan shi ba yabo ba fallasa, sai dai ta wani b'angaren yana farinciki mara misaltuwa idan ya tuna da Ummyn shi. Bayan an d'aura aure akayi k'asaitaciyar walima a nan harabar gidan. Sannan kowa ya kama gabansa. Bayan Magriba ana shirye shiryen d'auko Amarya Ummy Abba ya kira Jamal d'akinsa. "Jamaludeen!" Ya d'ago ya kalli Abba tareda amsa wah "Yanzu ka shiga wani rayuwa na daban, ka zama babban mutum, inaso ka kasance mutum mai adalci tsakanin Iyalinka. Karka zama mai yawan sa ido, sannan kada ka fifita d'aya ka bar d'aya" Kan Jamal k'asa yace "Insha Allahu" Key Abba ya mik'a mai da takardu yace "Wannan keyn gidan ka ne na baka halak malak, saidai inaso ku fara zama a nan gidan saboda naga kamin ludayin zaman naku" Godiya sosai Jamal yayi masa kansa k'asa. Abba ya nisa yace "Akwai wani sirri dayake cikin zuciyata wanda nake son sanar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82