Skip to content

Chapter 61

Chapter 61

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

sannan ya aje gefen wani bishiya, ya juya ya koma wajan motansa, K'aran Harbin Bindiga yaji from no where. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 10:54 AM] Ayshaaaaaa: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Dis page goes to Sumaiya Eesah Aunty Nurse Precious Girl Xeeaction Team Bilal Team Jamal Maman Ahmad Ahmad yusuf And All Jamaludeen Fans Both Whtsapp and Facebook.💯❤ ILYSM Page 71 Cikin wani irin k'ara ya rufe diaryn ya fashe da kuka sosai "Wai meke shirin faruwa dani neh? Allah ka kawo min d'auki a wannan hali danake ciki" Ya sake fashewa da kuka, diaryn ya d'auka zaiyi gurgi dashi sai kuma ya tsaya yana kallanshi yana cigaba da kuka, dakyar ya sassauta gabansa na fad'uwa sosai ya sake bud'ewa ya cigaba da karantawa. _nan muka same KA cikin wani akwati kana ta tsala kuka, ni da matata mun matuk'ar tausaya maka. Matata tasa hannu cikin fargaba ta d'agaka, wasu daloli muka gani shak'e da akwatin da kuma wasu zinarai duk a ciki._ _Munyi matuk'ar mamaki tare dajin tsoro, haka muka d'aukeka da akwatin muka nufi wani runfar mai k'osai muka kwanta har lokacin muna cikin fargaba._ Wani kuka ya sake zuwa masa yana cigaba da karantawa _Washe gari da safe na duba cikin Jakan, inda na tsinci wata wasik'a a ciki wanda aka rubuta cewa kanada Iyaye Uwa da uba, sannan kai ba shege baneh. Da kuma wasu hotuna a ciki. Haka mukayi ta rainonka da kud'in da muka tsince ka dashi. Kud'i ne masu d'inbin yawa wanda na dunga chanza su a hankali na fara juyawa_ _Ina sanka fiye da yanda nake san kaina, haka matata ta d'auke ka kamar d'an data haifah. Na juya kud'in sosai kuma sun hab'aka fiye da tunanina. Ana haka Allah ya amshi matata Jamila ta sanadin Haihuwa inda bata ruga da ta haifi abinda ke cikinta ba ta rasu_ _Lokacin kanada shekara bakwai, nayi kuka haka kaima kayi kukan rashin Jamila. Ana haka Allah ya had'ani da Maimuna na aureta, sam na hanata sanar dakai cewa ba ita ta haifeka bah, sannan ko ita ban sanar ma ba Jamila ta haifeka bah. Wannan na rik'esa a matsayin sirrina da naka_ _Nayi matuk'ar kuskure da ban fad'a maka da wuri bah. Nayi tunanin barinsa a raina sai daga baya naga rashin dacewar hakan. Ka yafemin d'ana abin k'aunata, ka yafemin rashin fad'a maka ko kai waye....._ Page d'in gaba ya bud'e yana kuka yaga a daidai nan rubutun ya tsaya. Ya rungume Diaryn ya sake fashewa da kuka "Na yafe maka Abbana, Allah ya jikan ka kaida Mamana, nima ina sanku" Tsam ya rungume Diaryn a jikinsa yana cigaba da kuka, gyangyad'i ya soma hakan yasa ya kishingid'a jikin gadon har lokacin Diaryn na jikinsa. A haka bacci ya d'aukesa mai cike da mafarkai kala kala, kiran sallahn Asubah ne ya tayar dashi ya mik'e zaune yana mik'a a hankali, juyawa yayi gefensa yaga diaryn a fad'ai k'asa ya bud'e. Wani rubutu ya gani hakan yasa ya d'auka dasauri yana dubawa _Ajiyarka yana cikin system d'in dake had'e da wannan littafi_ Dasauri ya mik'e ya nufi inda Jakan yake, wani zip ya bud'e sai ga system k'irar toshiba ta baiyana. Dasauri ya ciro ya kunna yayi sa'a akwai chargi, Yana kunnawa yaga password, bai sha wahala ba dan yasan password d'in Abban na komai nasa. Bincike ya soma har Allah yasa ya samu wani information na wani b'oyayyen gidan Abban dake gyallesu, Harda inda keyn yake. Wani lallausan Murmushi Jamal d'in ya saki "Thank Uh dad! I love uh so much" Ya share guntun kwallar data gangaro masa. Toilet ya shiga yayo alwala ya fito. Koda ya isa masallacin har an tada sallah, yana idarwa ya fito dasauri ya shiga side d'in Abban. D'akinsa ya shiga ya duba inda yace Keyn gidan yake ya d'auka ya fito. Motarsa yama key yabar gidan dasauri duk da yanda garin yake duk'u duk'u dan garin bai soma haske bah. Cikin 'yan mintina ya isa gyallesu kwatancen ya soma bi har ya isa k'ofar wani madaidaicin gida. Keyn ya d'auka ya bud'e gidan ya shiga da k'afar dama. Ya bud'e gidan ya shiga yana haskawa da torch d'in wayansa. Gaba d'aya gidan yayi k'ura sosai, bedroom d'in daya gani ya shiga ya d'aga katifan kan gadon sai ga k'aton Akwati ya baiyana. Akwatin yajawo ya fito dashi ya bud'e. Ba shiri ya koma baya ganin mak'udan kud'i dollars da kuma naira a ciki, ware ido yayi da mamaki yana bin kud'in da kallo. Daga saman kud'in akwai wata farar takarda inda aka rubuta "Dukiyarka kenan d'ana Jamal, ka Gafarceni na rashin sanar dakai da wuri" Hawaye suka gangaro masa, ya duba k'asan takardan inda aka rubuta "Duk wani abu dakakeso ka sani game da kai kana iya duba cikin wardrobe" Ya aje takardan a hankali yana cigaba da hawaye, wardrobe d'in ya bud'e yaga wani akwati mai d'an girma duk ya kod'e. D'aukowa yayi ya fita dashi zuwa mota sannan ya dawo ya d'au na kud'in dakyar ya kai mota shima. A police station kuwa, kamar yanda Mifzal da Lawyern Alhaji Alameen sukayi, k'arfe bakwai tama Lawyern a police station d'in. Mifzal bai iso ba sai wuraren k'arfe Bakwai da rabi. A wajan canther ya samu Lawyern, Mifzal na ganinsa ya cire eye glasses d'in dake idonsa yana kallansa da Mamaki "Are uh not Barr Ishak Haruna Lawyern Alhaji Surajo" Yayi saurin gyad'a kai yace "Yes nine" Mifzal ya sauke ajiyar zuciya ya bashi dama suka shiga office d'inshi, bayan sun zauna Mifzal ya mik'a masa hannu sukayi musabaha "Sunanan detective Mifzal Ibrahim, muna zargin Alhaji Ameenu neh da laifi guda biyu, Murder da kuma kiddnapping" Da Mamaki Barristern yace "Anma kuwa wannan abin da mamaki yake, duka duka watan Alhaji Ameenu nawa da dawowa k'asar Nigeria da zama" Knocking akayi Mifzal ya bada umarnin a shigo, Ramadhan ne ya shigo da sallama yana sanye cikin Suit b'aki da wani breifcase a hannunsa. Sosai Mifzal yaji dad'in ganinsa ya nuna masa kujera ya zauna. Mifzal ya nuna Ram yace "Barrister Ramadhan Ahmad kenan Lawyern Jamaludeen Surajo" Sukayi musabaha, Ram sai kallan Barristern yake da harara. Barr. Ishak yace "Zan iya ganin Alhaji Ameenun" Mifzal yace "Why not" Waya ya d'auka ya kira, chan sai ga wani d'an sanda, ya bashi Umarnin yakai Barr. Inda Alhaji Ameenu yake tsare. Yana fita Ram ya kalli Mifzal yace "Akwai wani abu mai matuk'ar d'aure kai dake faruwa" Jamal bai zame ko ina ba sai gida, bai samu kowa a farfajiyan gidan bah, ya kinkimi Akwatin yakai d'akinsa, ya dawo yad'au d'ayan yakai. Already dama yasayi ghana must go a hanya, zama yayi dirshan ya soma irga kud'in yana sakawa cikin ghana must go d'in batare da wani tunani bah, dan gaba d'aya hankalinsa nakan Wife d'insa. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:16 AM] ‪+234 706 272 2689‬: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ _Salam Masoyana, kuyi min Afuwa jina shiru kwana biyu. Uzuri ne a gabana dts why, anma insha Allahu zan cigaba da posting kamar yanda nakeyi dah_ *Kusha Kurumin ku masu tambayan Labarin Jamaludeen, Insha Allahu yazo k'arshe nan da

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82