Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

Mama shiknan ni nasan na Baba abu mai sauk'i neh" "Shiknan Ummy Allah dai ya zab'a abinda yafi zama alheri, Allah kuma ya mana jagora" "Ameen Mama" A tare suka fito suka soma aiki gyaran gidan. Inna najin motsin su ta shiga ta k'ara gaida Baban dan dama taje ta gaidashi a asibiti. Bayan kwana biyu Ummy ta tari Baba da maganan aikin da takeso ta fara, da farko yak'i yarda dakyar ta shawo kanshi ya yarda dakyar. Nasiha ya mata sosai akan kare mutuncinta sannan ya bata izini taje gidan Dilalliyan ta tambayo, tana zuwa ko tace mata dama gida d'aya ya rage kuma har yanzu ba'asamu bah. Sosai Ummy taji dad'i sun aje akan washe gari zasuje ta kaita gidan. Da farinciki ta dawo ta sanar dasu Mama sun mata fatan Alheri sosai da haka ta soma shirinta na gobe dan zuwa gidan babban fatanta Allah yasa kud'in da xa'a biyata yakai dubu uku dan tasamu na sayama Babanta Magani.. ​This is just the Beginning​ Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 11:40 PM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* ​Page 7​ Babban fatanta Allah yasa kud'in da za'a biyata yakai dubu uku dan ta rik'a samu tana sayama babanta magani. Washe gari da wuri ta tashi ta gama duk wani aikinta, tana shiryawa ta leka d'akin Baba tamai sallama ta fito, Addu'an nasara Mama ta mata sannan ta fita ta nufi gidan dilalliya. Tana zuwa suka d'au hanyan samaru, itadai Ummy sai rarraba idanu take tana kallan hanya, a wajan aviation suka sauka wani anguwa da ake cema hanyin mallan, nan suka k'ara hawa mashin suka d'au hanyan cikin anguwan, gine gine na zamani masu kyawun gaske suketa wucewa har suka kawo wani had'adden gida gate d'in gidan k'ato ne ga tsayi sai shek'i yake. Dilalliya ta biya masu mashin sannnan ta soma kwankwasa gidan, bin gate din da kallo kawai Ummy keyi da sha'awa, wani ne ya bud'e karamin k'ofan ya leko yana wani yatsine fuska "Lapia dai koh?" Dilalliya aka washe baki "Aa lapia lau, dan Allah iso za'a mana ace ma Hajiyar dilalliya ce" Baice komai ba ya rufe k'ofan, suna nan tsaye aka k'ara bud'ewa nan ya basu izinin shigowa, suna shiga Ummy ta bud'e baki tana kallan gidan, dank'ararren gida ne na gani na fad'a, Main building d'in na tsakiya sai kuma wasu parts guda hud'u, biyu gefen hagu, biyu a dama. Sosai gidan ya burge Ummy musamman Swimming pole d'inda ta hango a chan gefe d'aya, sai kuma wani d'an garden daga gefensa d'an cage ne a ciki akwai kaya na wasan yara iri iri, ganin tana k'okarin fad'uwa Dilalliya ta rik'eta tana b'ata rai "Wannan wanne irin kallo ne haka sai kinje kin fad'i kinjima kanki ciwo, keda a nan zaki cigaba da rayuwa" Itadai Ummy batace komai bah har suka k'arasa falon, nan ma Ummy tasha kallo dan tunda take bata tab'a ganin gida mai tsaruwa irin wannan ba. Hajiyar suka hango zaune a falon tasa Laptop a gaba tana daddanawa hannunta rik'e da wani paper. Dilalliya ta zauna kan carpet chan nesa da Hajiyar ta gaidata, batareda hajiyan ta kalleta ta amsa gaisuwan, Ummy itama ta gaidata har lokcin idanun Hajiyan nakan abinda takeyi. "Dilalliya maike tafe dake" Nan fa ta gyara zama ta soma magana cikin ladabi "Hajiya dama akan maganan y'araikin da kikamin kwanaki neh, tho gashi na samo miki" Kurrri tama Hajiyar tana jira taji mai zatace, saida tad'au minti Goma sannan ta d'ago tana duban Dilalliyar "Ai na riga na samu, danaji shiru sai naba wata cigiya" Ummy wacce kanta ke k'asa hawaye suka taru mata a ido ta d'ago da sauri tace "Hajiya d'an Allah ki taimakeni ki d'aukeni, ina buk'atar aikin nan dan Allah Hajiya" Ta k'are maganan da fashewa da kuka, Kallanta Hajiyan take bako kyaftawa "Menene Sunanki?" D'an dagowa tayi batareda ta kalli Hajiyar ba "Sunana Jaleelah anma Ummy ake ce min" "Ummy d'ago idanunki ki kalleni" Bah musu ta d'ago suka had'a ido da Hajiyar, sai a sannan ta shaidata Hajiyar data taimaketa a asibiti rannan kan tayi magana Hajiyar ta rigata "Ya jikin Mahaifinki?" "Dasauk'i Hajiya mun gode" Dilalliya sai kallansu take da mamaki "Ummy dama kunsan juna neh" Hajiyar tace "Babu damuwa zan d'aukeki aiki Ummy, tun randa na fara ganinki naji kin kwanta min arai, ina miki kallon kamar y'a a wajena" "Tho Tho Madallah Hajiya" cewar Dilalliya "Zakiyi hak'uri da abinda zan rinka baki dan ba yawa dubu goma ne" Ai a rud'e Ummy ta d'ago idanunta taf da hawaye "Nagode Hajiya Allah ya saka da Alheri ya k'ara bud'i" Ameen Hajiyar tace tana lumshe ido, Sosai taji dad'in addu'ar da Ummyn ta mata. "Abu na gaba shine a nan zaki rink'a zama saida sabda lalluran mahaifinki zan rink'a sawak'e miki kina zuwa gida duk ranar Sati ki dawo lahadi" Shiru Ummy tayi kanta k'asa "Ke nake saurare" cewar Hajiya "Amm da an bari sainayi shawara da iyayena tukun" "Tho babu damuwa zaki iya zuwa" Mik'ewa tayi ta haura sama chan ta sauko rik'e da wani envelop ta mik'ama Ummyn tana cewa "Gashi nan idan sun amince sai ki bar musu gobe ki fara zuwa aiki" Hannu biyu tasa ta karb'a tana godiya, Itama Dilalliyar an mata ihsani suka fito dukansu cikeda farinciki. Tana zuwa ta zaiyanema Iyayen nata duk yanda sukayi sosai sukaji dad'i kuma suka bata goyon baya, Mama ta mik'ama envelop d'in ta bud'e, kudi ne dubu goma sha biyar, Baba yasa albarka haka Mama. Kud'in ta amsa ta tafi kasuwa ta musu sayaiyan duk abinda suke buk'ata harda Inna tad'an mata siyaiya daga nan kuma ta saima Baba maganinsa ta dawo gida.. Albarka Su Mama suketa sa mata tanata murmushi cikeda jin dad'i, batasamu kaima Inna nata ba saida daddare a nan take fad'a mata aikin data samu itama tayi mata murna tareda Addu'a, a nan suka sha kukansu na tunawa da Bilal sannan Ummy ta dawo gida. Daren ranan kuka Ummy tayi sosai rungume da hannunta wanda ta sanya zoben da Bilal ya bata. Addu'an Naiman rahama ta dunga mai duk da ita har yau zuciyarta tak'i aminta da cewa Bilal ya rasu.. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:22 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* ​Page 8​ Addu'an naiman Rahama ta dunga mai duk da ita har yau zuciyarya tak'i aminta da cewa Bilal ya Rasu. Washe gari da wuri ta gama ayyukanta, Mama da kanta ta had'a mata kayanta a ghana must go k'arama, Ummy ko sai kukan rabuwa da iyayen nata take dan tunda take bata tab'a matsawa daga kusada Iyayenta na kwana d'aya ba ma. Mama taita lallashinta har tayi shiru, d'akin Baba ta shiga da mai sallama, Lalluban kanta yayi ya d'aura hannunsa akai ya mata addu'a tareda nasiha, har lokacin kuka Ummyn keyi. Yana gamawa tayi mai sallama ta fito, suka k'ara sallama da Mama ta fito ta shiga gidan Inna itama sallaman tayi mata sannan ta fito ta tari adaidaita sahu ta hau. Kasancewar ranar Lahadi neh Hanyar duk yad'an chuse saboda masu zuwa church, cikin idon Allah suka isa kofar gidan, Mai gadi na ganinta ya

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82