Chapter 11
Chapter 11
mata kai "Allah sarki Mama ya take? Ya jikin Baba" "Dasauki" Ummy ta bata amsa. A tare suka gama gyaran alaiyahun, sannan suka wuce d'akin Ummy, tsaraban ta ciro mata na kayan ciye ciye da Mama ta bata ta kawo mata, su goruba da tsamiyar biri dadai sauransu, sosai Laurat taji dad'i tayi godiya sosai. Sannan tace "Kinsan meke faruwa a gidan nan kuwa?" Ummy ta girgiza kai alamar A'a, Laurat tace "Nima d'azu muna hira da Mama Talatu take cemin wad'an nan turawan masu kula da Jamaludeen zasu koma k'asarsu gobe da safe" Ummy ta zaro ido dasauri "Kai dan Allah dagaske?" Laurat ta gyad'a kai "Wallahi kuwa, wai an kirasu a k'asarau, dama ma'aikatan asibiti neh" Jikin Ummy neh yayi sanyi tace "Tho yanzu wazai cigaba da kula dashi?" "K'ila zasu samo wasu neh ina ganin" Shiru Ummy tayi duk saitaji hiran ta gunduretah. Haka ta yini jugum ranta bai mata dad'i, tausayin Jamal ne ya cikata. Da safe bayan ta idar da sallan asubah tana zaune kan sallayabtaba lazumi aka banko k'ofan d'akin, Mabrookah ta gani tsaye tana yatsine yatsine tana bin d'akin da kallo "Ki fito Mami da Abba na kiranki a falo" Ta sake banko k'ofan ta fita daga d'akin. Girgiza kai Ummy tayi cikeda takaici, saida ta gyara hijabin jikinta sannan ta fito zuwa falon, bataga kowa ba dan haka ta haura zuwa falon sama, hangosu tayi zaune jugum jugum ta shiga da sallama ta samu guri k'asan carpet chan nesa dasu ta zauna, d'aya bayan d'aya ta gaishe su, Abba ya kalli Mami yace "Itace yarinyar" Mami tace "Itace, kuma nasan zata iya" Gaban Ummy ya yanke ya fad'i, tad'an d'ago kai tana kallan Mami, Abba yace "Ki kwantar da hankalinki, ba wani abu baneh. Nasan kinsan d'ana Jamaludeen" Ummy tace "Eh" Abba ya cigaba da cewa "Kuma nasan kinsan lalurar dayake tattare dashi" Nan ma ta sake gyad'a kai "Akwai turawa wad'anda suke lura dashi dangane ga abincinsa da kuma maganinsa dadai sauran yan abubuwa da suka shafe shi, tho yanzu wa'adin da suka d'iba ya cika kuma sunce bazasu k'ara kwanaki bah. Dan haka shine nake neman wanda zai cigaba da aikinsu" Ya nuna Mami yace "Shine Hajiya tacemin zaki iya" Shiru tayi kanta a k'asa. Hajiya tace "Bakice komai ba Ummy" Abba yace "Karki damu indai maganan albashi neh zan ninka miki akan abinda ake biyanki, zan rink'a biyanki dubu d'ari duk wata" Da mamaki Ummy ta d'ago ta kalleshi, ya gyad'a mata kai tace "Zan Iya Alhaji, saidai kud'in yayi yawa" Mami tayi murmushi tace "Karki damu buk'atarmu dai ki yarda, sanin halinki da k'wazon ki yasa na amince dake akan aikin" Shiru ta sakeyi anya kuwa zata iya wannan aikin? Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:26 AM] +234 806 215 4020: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 14 Shiru ta sakeyi anya kuwa zata iya wannan aikin "Ke muke jira har yanzu bakice komai bah" Mabrookah ta tab'e baki tace "Mami dama kun kyaleta, wannan ba iyawa zatayi bah" Mami ta galla mata harara, ta kauda kai gefe tana turo baki. Ummy tad'an d'ago tace "Zan iya saidai ban iya bashi abinci bah" "Indai wannan neh karki damu, za'a nuna miki komai" cewar Hajiya Abba yace "Tho Alhamdulillah tunda kin amince, sannan aikin bawai zaki dauwama dayi baneh, nad'an wani lokaci ne zuwa sanda za'a samo wad'anda zasu cigaba" Ummy ta gyad'a kai, Mami ta sallameta ta tashi ta koma d'akinta tana tunani. Ranar Mami bataje aiki ba saboda tafiyan turawan nan, an musu sha tara ta arziki (abunku da gidan mai naira) har airport aka kaisu suka hau jirgin lagos dan tachan zasu tashi. A ranar Mami ta koya ma Ummy yanda ake feeding d'insa, da kuma nuna mata rosters abincinsa da magugunansa. Sosai ta fahimta kuma a ranar Mami tace zata fara aikin, Saidai abinda Mamin bata sani bah shine Ummyn bata iya karatu ba dan bata iya karanta abinda ke jikin rostern abincin Jamal d'in. Wureren k'arfe sha biyu ta shiga kitchen ta samu Laurat tana yankan albasa, murmushi ta mata bayan ta k'araso wajanta "Taimako zakimin Laurat" Laurat ta d'ago tana kallanta "Taimakon meh fah" Nan ta fad'a mata aikin da Mami ta bata na kula da Jamal, da mamaki Laurat tace "Anya kuwa zaki iya Ummy?" Hararan wasa Ummy tai mata tana cewa "Mai zai hana, wannan ai wani dama ce na samu na samun lada, kinsan kula da mara lafiya akwai lada sosai" Laurat ta gyad'a kai "Tho Allah ya bada sa'a" "Ameen, ni kinsan ma menene Laurat" Laurat ta girgiza kai "Wallahi ni rubutun kayan abincin nasa neh bana ganeh wa, dan Allah ko zaki karanta min" Papern ta mik'a ma Laurat ta duba tareda zaiyane mata duk abinda ke cikin takardan. Godiya ta mata ta amsa tana cewa "Oh Ikon Allah kenan, jidai duk dukiya irin na mahaifinsa anma ya koma shan kunun gero da dawa" Cikeda alhini Laurat tace "Allah kai mana rowan ciwo dai" Ummy ta amsa da Ameen. Sallama tama Laurat ta haura sama zuwa d'akin Jamal d'in dan lokacin bashi abincin rana yayi, kunun tamba dake flask ta d'iba tasa madara da sugar kad'an sannan tad'au syringe ta soma zuk'a tana d'uramai ta bakin NG tube d'in dake hancinsa. Tana gamawa ta dama maganinsa shima ta basa. Zama tayi kusada shi tana kallanshi fuskanta d'auke da Murmushi, duk da hali dayake ciki na rashin lapia, ko kad'an baida rama a jikinsa koh alamar wahala sai ma wani k'ara haske dayakeyi. Idanunshi kamar kullum yana nan kyam a wuri d'aya baya kyaftawa. A haka Ummy ta cigaba da aikinta a gidan har batada lokacin kanta, kullum da sassafe take tashi ta soma gyara d'akinta sannan ta haura nasu Mami ta gyara da side d'in Alhaji. Kula kuwa da Jamal ba'a magana, ta d'aukema masu gyara masa d'akin da wankin kayansa, kullum ita take masa a washing machine dan Mami ta hanata wankin hannu tasa an koya mata yanda ake anfani da machine d'in kuma ta iya, duk weekend tana zuwa wajan iyayenta. Wani lokaci ta shiga gidansu Bilal wata rana kuma bata samun shiga. Kimanin wata Ummy biyu kenan a gidan, Mami da Abba najin dad'in yanda take kula musu da d'an nasu, kyautatawa na abubuwa da dama tana samu daga wajan Mami da Abba, Mabrookah kuwa har yau ba abinda ya chanza daga halaiyarda take nunawa Ummy. Yau bayan ta gama duk ayukanta, feeding d'in Jamal take tana kallan kyakyyawar fuskarsa harta gama sannan ta basa maganinsa. Zama tayi kusa dashi kamar kullum tana kallansa, wani dabara ce ta fad'o mata ta mik'e dasauri ta sakamai belt d'in dake wajan hannuwansa, ta saka masa na k'afa ta gunguroshi ta fito dashi daga d'akin. Dakyar ta sauko dashi k'asa ta fita dashi waje zuwa chan garden d'in dake bayan gidan, ma'aikata sai kallanta sukeyi dan yawancin su basusan ita ke kula dashi bah. Garden d'in ta kaisa ta ajeshi, kneel down tai a gabansa ta sa hannunta ta d'ago fuskanshi tana murmushi "Yau kaima ka fito kasha iska kaga haske" Dariya tayi hawaye cike a idonta tana kok'arin yin kuka "Jamal! Yaushe zakayi magana? Insan jin maganarka. Inasan naga ka warke"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82