Chapter 21
Chapter 21
tabar falon, binta da ido Jamal yayi har ta shige kwanan d'akinta, Aunty Faty sai kallanshi take da mamaki "Kaji Jamal da wani zance, shekaran su ashirin kenan, kaida kake zaune kan kujeran k'arfe har shekara uku ya za'ayi dama kasan wad'an nan" Twins dasu Mabrookah sukasa Dariya, nan suka cigaba da hiransu Aunty Faty sai tsokanan shi take yana bata amsa, itako Aunty Zainab ba ruwanta saidai idan anyi abin dariya tayi. Suna gamawa Mami ta sake kiran Ummy dan tazo ta kwashe kayan da'aka ci abinci. Mami tace "Mabrookah Mama tazo an wani mak'ale mata, ai zata tafi ne muna nan dake" Ummy ta d'ago dan taga wacece Maman Mabrookah, Aunty Fatyn nan tagani Mabrookan ta mak'ale mawa, ta sauke ido dasauri ganin sun had'a ido da ita ta soma kwashe kayan. D'aya daga cikin twins d'in ta mik'e ta soma tattara kayan tana cewa "Barin tayaki kwashewa, Umm mu mun saba dayin aikin gida" Tana tattarawa d'ayar itama ta mik'e ta soma tayata, Mami tace "Trainning d'in Zainab kenan, kedai har yanzu bakison mai aiki" Murmushi Aunty Zainab tayi ta gyara zama tace "Aa nikam ba ruwana da mai aiki, tunda chan ban santa balle yanzu gani da yara kaman su Najma ai sai suyi" Aunty Faty ta tab'e baki, Ummy ta shigo taga su twins sun d'auko kayan tayi maza ta rik'e tana cewa "Aa ku bari na kai ku huta" K'in yarda sukayi hakanan suka cigaba da kai kayan tare sannan Ummy ta koma d'akinta. Da daddare Ummy bata samu hutu bah, tana d'an zama Mami zata k'walla mata kira tayi wani aikin. Bata samu ta runtsa ba sai k'arfe sha biyu da rabi, sosai Jamal ya tausaya mata dan yana ganin duk abinda ke faruwa kasancewar a side d'in ya wuni. Da safe wuraren k'arfe bakwai da rabi Ummy ta fito kicin ta had'u da d'aya daga cikin twins d'in ta sauko, Murmushi tama Ummyn tace "Sannu da aiki, kina k'okari maine sunanki" "Jaleelah, anma Ummy ake kirana" Ta gyad'a kai tace "Ni kuma sunana Najma, and my twin sister Najwa. Kuma nice Hasana" Ummy ta gyad'a kai da murmushi "Allah sarki, sannu" "Keh Najma me kikeyi a nan wajan" A tare suka d'aga kai sukaga Aunty Faty ce tana k'okarin saukowa daga benen gidan Najma ta zumb'uro baki tana d'an bubbuga k'afa "Dake fa nake magana Najma kinyi banza dani" "Babu komai, kawai muna magana neh. I want her to be my friend" Aunty Faty ta zaro ido da mamaki ta k'araso inda suke tsaye "What! Kinsan meh kike fad'a kuwa?" Ta juya tana kallan Ummyn fuska ta yatsine "Ke kuma zaki b'acemin da gani ko saina b'alla ki" Ai a guje tabar wajan gabanta na fad'uwa. Fad'a sosai taima Najman dan tunda suka had'a ido da Ummyn taji yarinyan bata mata bah, ga kuma labarinta dataji wajan Mabrookah a daran jiya sai taji ta k'ara tsanan yarinyan. Ranar Ummy ta wahala sosai wajan Aunty Faty, duk bayan mintina sai tasa an kira mata ita tasata aiki, duk da ta gaji sosai anma bata nuna musu bah haka taketa daurewa tana aikin. Tana kwance a d'akinta wuraren la'asar aka turo k'ofar d'akin nata aka shigo, d'an d'agowa tayi sannan ta mik'e ta zauna ganin Najma da Najwa. "Ana kirana neh?" Ta tambayesu tana kallansu "Aa ba kiranki ake ba munzo tayaki hira neh" Ta d'anyi kasak'e tana kallansu da mamaki, d'aya daga cikinsu tace "Mene sunana?" "Najma" tace da murmushi Dariya suka fashe dashi, d'aya tace "Ni ce fah Najma" Ta nuna wacce tai ma Ummyn tambayan tace "Ita kuma Najwa" Ta kafesu da ido tana k'okarin banbance tsakaninsu, kan gadonta suka zauna suka soma mata hira. Sakin jiki tayi sunata hira, a nan take sannin cewa Aunty Faty yayar Mami ce, Aunty Zainab kuma itace mamansu kuma k'anwar Mamin ce. Sun dad'e suna hira kamin daga baya Mabrookah ta shigo ta korasu bayan ta zage Ummyn tas. ****** Ranar monday da safe Jamal ya shirya cikin suit Blue da farin shirt a ciki, k'afarsa sanye da Black cover shoes kanfanin versace, falon ya shigo bai tarar da kowa bah, d'akin Ummy yayi knocking a hankali yanayi yana kallan step, jin shiru yasa ya murd'a a hankali ya shiga. Kan sallaya ya sameta tana lazimi, ya k'arasa ya zauna kan gado yana kallanta, ganin ya zauna yasa tayi saurin shafa addu'an datake ta juyo tana kallansa "Ya Jamal me kakeyi a nan?" Ya mik'e ya k'araso inda take ya tsugunna yana kallanta da murmushi "Bah gaisuwa sai tambaya" "Ina kwana" tace dasauri a d'an tsorace tana kallan k'ofar d'akin "Karki damu basu tashi bah, i just came to see uh kuma kimin addu'a yau zan fara zuwa aiki" Ta sauke ajiyan zuciya ta d'an kalleshi tace "Allah ya tsare ya kareka daga sharrin mak'iya" Sosai yaji dad'in addu'arta ya amsa da amin tareda shafa gefen fuskanta yana murmushi "Matsoraciya kawai" Ya mik'e ya fita daga d'akin, kicibus yayi da Mami a falon, ya d'an zaro ido "Jamal zo nan" Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:38 PM] +234 703 981 8283: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 25 n 26 Ya mik'e ya fita daga d'akin, kicibus yayi da Mami a falo, ya d'an zaro ido "Jamal zo nan" Sunne kai yayi ya k'araso ya zauna kan kujera yace "Ina kwana" "Yanzu dai Jamal ka daina jin magana ta" "Mai kuma nayi Mami tah" "Mai nacema akan maganan yarinyar nan" Ya sunnar dakai yana jujuya wayan dake hannunsa "Da kanajin magana ta anma yanzu ka daina, ka kiyayeni in ba haka ba ta kusa daina aiki a gidan nan" Ba shiri ya d'ago da mamaki yana kallanta "Kiyi hak'uri Mami bazan sake bah" "Menene tsakaninka da yarinyan nan neh wai" Ya sake duk'ar dakai baice komai bah, ba shiri ba mik'e tsaye dasauri "Noo! Karka cemin santa kake, dan bazan yarda bah, ya zakayi da Mabrookah daketa jiranka" Ya turbune fuska danshi harga Allah baisan Mabrookah, Aunty Faty ta sauko jin tashin muryan Mami "Lapia Maimuna kiketa d'aga murya haka" Nuna Jamal tayi tana cewa "Zo ki tayani jin abin kunyan da Jamal keso ya d'auko min" "Na meh?" Aunty Faty ta tambaya tana kallan Mami "Yaran nan ace duk jiran da Mabrookah ta masa yanzu ya samu lapia yake so ya watsa mana k'asa a ido" "Mami kiyi hak'uri ni fa ba san Ummy nake ba" Sai a sannan Aunty Faty ta gane inda Mami ta dosa "Jamaludeen me zakayi da mai aiki talaka, wacce ko boko batayi bah" Sosai maganan Aunty Faty ya b'atamai rai, Abba ne ya shigo falon da sallama, wayancewa sukayi Aunty Faty tace "Allah ya tsare ya bada sa'a Jamal" Wuf ya mik'e dan dama hanya yake nema, Abba ya gaishar ya musu sallama ya bar gidan zuciyarsa na masa suya. Nan Mami da Aunty Faty suka soma shawaran yanda zasu b'ulloma alamarin. Cikin satin Ummy tasha wuya wajan Aunty Faty kamar ba gobe, itadai Aunty Zainab Ummin su Twins batace wa komai sai ido data zuba musu, itama kanta batajin dad'in abinda akema Ummyn. Sosai Ummy ta shak'u dasu Twins, so dayawa suna tare a kicin suna aiki tare, ko idan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82