Chapter 80
Chapter 80
bacci tayi ana shafata ta mik'e dasauri a razane, duhu ta gani a d'akin, cikin wani irin murya yace "Shhhh! Ni neh, Pls Wife ki tausaya min" Yanda ya rik'eta yasa ta soma kokarin kwacewa "Ni kunyansu Ammi nakeji dan Allah ka tafi d'akinka kada tazo ta samemu" Bai ce mata komai bah ya kwantar da ita kan gadon tare da soma mata wasu salo wanda yasa hankalinta ya d'auke. (Asubah ta gari Amaryan Jamal" Kuka ta dunga masa gaf da asubah kan ya koma d'akinsa dakyar ya kyalleta ya fita ransa a d'an bace wanda ta lura da hakan. Washe gari bata fito da wuri ba sai k'arfe Tara na safe, da Ammi ta soma had'uwa ta durk'usa har k'asa ta gaidata, ta amsa da fara'a tana cewa "Kije Mama na d'akinta" To tace ta mik'e ta shiga d'akin, Itada Bilal ta da Jamal ta samesu suna hira, ta k'arasa a sanyaye ta zauna kusada Maman ta gaisheta sannan ta gaida Bilal kanta k'asa, ya amsa shima yana sunne kai dan gaba d'ayansu kunyan juna suke yanzu. Jamal ta gayar saida ya harareta sannan ya amsa tad'anyi murmushi kawai. A bakin Areefah take jin Maganan Gidan da Jamal yasai ma Mama, da farinciki ta shiga d'akinsa lokacin ya fito wanka yana saka kaya, saurin juya baya tayi tasa hannayenta ta rufe fuskanta tana dariya. Shima murmushi yayi sannan yad'an d'aure fuska "Kina buk'atan wani abu neh" Cikin sanyin murya tace "Mungode Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i, ya kuma rabaka da iyayenka Lafiya, ya kareka sa sharin mak'iya" Sosai yaji dad'in addu'anta ya amsa a hankali yanda bazataji bah sannan yace "Da akayi meh" Tad'an waiwaya ta kallesa tace "Gidan da aka saima Mama" K'ugu ya rik'e yana murgud'a mata baki, ta saki dariya "Ina ruwanki toh, ai mamana masai mawa ba naki bah" Ta ruga ta fad'a jikinsa tare da kaimai kiss a kumatunsa "Thank uh so much Noorul Qalb" Ya d'agota da mamaki "Repeat what u said Plsss Wife" Murmushi ta masa ta sake rungumesa tana dariya "I love uh so much Noorul Qalb" "I love uh more" yace a hankali yana k'ara rungumeta, ganin take takensa yasa ta kwace da k'arfi tayi hanyan k'ofa "Ni koh" Tamai gwallo "Eh d'in" Binta yayi ta fita da gudu, da Ammi tayi kicibus tayi saurin b'oyewa a bayanta. "Ammi kingansa koh" Ammi ta had'e fuska "Jamaludeen ka kiyayeni fah, kazo kenan zaka daman min 'ya. Baka ganin abinda take tare dashi" Ya sosa k'eya, Ummy ta masa gwalo yayi kwafa ya koma d'aki yana gungunai. Summ summ tabar wajan ta shiga kicin wajan Areefah. Bayan la'asar gari yayi sanyi sukaje ganin gidan Ammi, k'aton gida ne mai kyan gaske da tsaruwa, sosai Ummy tayi santin gidan. Suna fitowa suka shiga na kusa dana Ummyn, A nan yake shaida musu nan ne zasu zauna. Gidan shima yayi kyau matuk'a, bakin Ummy yak'i rufuwa saboda farinciki. Ammi da Areefah suka tayasu Mama yi masa godiya ya kauda kai gefe yana murmushi tare da girgiza kai. Da farinciki duka suka koma gida, ba yanda baiyi Ummy taje d'akinsa ba tak'i. Haka ya hak'ura ya kyalleta anma wannan karan yayi fushi sosai. Wuraren k'arfe Tara da rabi na dare ya dawo daga yawo yaga wad'an nan manyan mutanen masu sanye da bak'aken kaya a k'ofar gidan, parking yayi bai fitoba yana nan zaune cikin mota Abba ya fito shida Bilal suka shishiga motan suka fita da gudu daga layin sauran mutanen na mara masa baya a wata hilux. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 93 🔚 Parking yayi bai fitoba yana nan zaune cikin mota Abba ya fito shida Bilal suka shishiga Motan suka fita da dugu daga layin sauran mutanen na mara masa naya a wata helux. Shiru yayi yana tunanin Abinda ke fita da Abba da daddare, ya kunna motan yayi horn mai gadi ya bud'e masa gate ya shiga. Ammi ya samu a falo itada Mama dasu Ummy suna hira, a hankali ya k'arasa ya zauna tare da gaidasu suka amsa da fara'a. Su Ummy suka mai sannu da zuwa ya amsa yana satan kallan Ummyn. Ammi tace "Yauwa Jamaludeen dama Maman Jaleelah ce tace mai zai hana Umman Bilal ta dawo gidan da take su zauna tare" Mama tace "Gidan ne yamin k'ato kaga idan muna jin motsin juna yafi dad'i tunda itama ba miji gareta ba kuma Bilal d'in na nan" Ya d'ago fuskansa d'auke da murmushi yace "Babu damuwa Mama wannan shawaran yayi" Mama ta sake masa godiya ya mik'e ya shiga d'akinsa. Gaba d'aya jikinsa ne yayi sanyi ala ala yake su dawo dan yau ya k'uduri niyan tambayan Abban inda suke zuwa. Kwanciya yayi kan gado a rigingine yana kallan ceiling ya dad'e a haka yaji knocking a k'ofar d'akin, bada izini yayi a shigo, Da sallama Ummyn ta shigo hannunta d'auke da k'aton tray ta k'araso ta aje k'asa sai binta da ido yake. Tad'an kalleshi tace "Yau naganka wani iri lafiya kuwa" Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Lafiya lau kawai dai na gaji neh" Ta duk'a ta soma zuba masa abincin, tana cikin zubawa yace "Barshi haka" Ta d'an d'ago ta zuba masa narkakun idanunta "D'an kad'an fa na zuba ai bazai isheka bah" Ya gyad'a mata kai kawai batare da yace komai bah. Ganin yanayin sa yasa ta mik'e ta xauna kusa dashi tare da kamo hannunsa "Ya Jamal ko bakada Lafiya neh" Yad'anyi dariyan k'arfin hali "Lafiya na lau Wife kawai gajiya neh" Plate d'in ta d'auka ta diba a spoon takai bakinsa, ya kauda kai tare da yatsine fuska "Plsss Ya Jamal" Yanda tayi maganan a shagwab'e yasa ya juyo ya d'an bude baki tasa masa. Da kanta ta basa yanata mata shagwab'a tana dariya har yad'anci dayawa. Yana gamawa ta tattara kayan ta aje gefe ta shiga toilet ta had'a masa ruwan wanka. Nan ma saida sukasha daru dan tsayawa yayi kai da fata dole ita zatai masa. Guduwa tayi niyan yi yayi saurin janyota ta fad'a jikinsa ya sakar musu shower. Soyaiya mai tsafta ya nuna mata wajan wankan sai susune kai take kamar *Ummu Manal* har suka fito. Da kansa ya shafa mata mai tanata turjewa idanunta a lumshe. Wajan shafa man ne kid'a ya soma chanzawa ina ganin haka nayi waje abuna. Su Abba basu dawo gidan ba sai k'arfe shabiyu da rabi, lokacin gidan tsit da alama duk mutanen gidan sunyi bacci banda Jamal dake kwance rungume da Ummynsa dake bacci hankali kwance. Jin k'aran gate yasa ya zame daga jikinta ya d'an d'aga labule yana lek'awa. Bilal ne ya bud'e ma Abban mota ya fito sannan ya wuce side d'insa shi kuma Abban ya shigo cikin Falon gidan. Jiki na rawa yad'au jallabiya yasa ya fito daga d'akin, ga mamakinsa Ammi ya gani a falon tana karb'an babban rigan daya cire, Yana juyowa suka had'a ido da Abban, Ammi itama ta juyo suna kallan kallo, Kamar wanda k'wai ya fashewa a ciki ya k'arasa indasu Abban suke ya sadda kai yace "Sannu da zuwa Abba, Ab..." Yayi saurin d'aga masa hannu yace "Nasan me zaka tambayeni" Ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82