Chapter 44
Chapter 44
'yan uwa. Mu sani duniya ba matabbata bace, Kullu nafsin zaikatul maut. Kowace rai dole sai ta d'an d'ani zafin mutuwa, ko ka shirya ko baka shirya ba dole idan lokaci yayi zaka tafi. Mu cire dogon buri a zuciyarmu, mu cire hassada, mu cire k'yashi. Duniya ba matabbata bace,dan bakasan a halin da zatazo ta d'aukeka bah. Mutuwa lokaci d'aya takan zo. Mu yawaita ayukan Alkhairi, sadaka, biyaiya ga Iyaye, Barin abinda Allah ya hanemu, yin abinda Annabin mu ya koyar damu. Yawaita istigfari. Sallah akan lokaci, bin umarnin miji, Dadai sauran su``` _Allah ya yafe mana kurakuren mu, wanda muka sani da wanda bamu sani bah. Allah ka yafe ma magabatan mu da suka riga mu, mukuma idan tamu tazo kasa mu cika da kyau da imani Ameen_ Har aka kaisa aka dawo Jamal bai daina kuka bah, dan shi kad'ai yasan abinda yakeji. Nan k'ofar gida aka sanya canopy na amsar gaisuwa. Manya manyan mutane daga wuri daban daban suka soma tururuwa zuwa gaisuwa. Innan Bilal ce ta shiga gidansu Ummy da sallama hankali tashe take sanar da Mama abinda ya faru dan itama lokacin take ji a rediyo. Hankalin Mama ba k'aramin tashi yayi ba jin abinda ya faru. Ranar da aka kaisan Mama da Innan Bilal harda Bahar suka zo gidan gaisuwa, duk da yanda hankalin Ummyn yake ba'a kwance bah hakan bai hanata nuna farincikin zuwansu bah. Ita ta musu jagora har inda Mami ke amsar gaisuwa. Bayan sun gaisa Najma dake wajan ta gabatar dasu a matsayin Iyayen Ummy. Nan da nan Aunty Faty ta had'e rai, itako Mami amsa gaisuwan su tayi a mutunce. Sun d'an jima kad'an sannan suka musu sallama suka tafi. Yinin ranar zazzab'i ne sosai ya rufe Jamal, ba yanda Ram beyi dashi akan yasha magani ba anma yak'i. Ko abinci yak'i ci ga yanda jikinsa yayi zafi sosai. Da daddare bayan 'yan zaman makoki sun tafi, d'akin Abba ya shige ya hau kan gadon ya k'udundune cikin barko yana kuka yana kiran sunan Abban a hankali. A haka bacci ya d'aukesa cike da kewan Abban nasa. Tun daga ranar Jamal ya k'ulla abota da tunani, Ram da sauran 'yan uwa sunyi lallashin har sun gaji. (Hmm mutuwa kenan, Allah bai tab'a barin wani dan wani yaji dad'i) Tun da akayi rasuwan Ummy bata k'ara saka Jamal a idonta ba sai ranar da akayi uku da safe, lokacin ta fito daga side d'in su zata na Mami, ta had'u dasu shida Ram sun fito daga side d'in Abba. Jikinta ne yayi sanyi ganin yanda ya rame cikin kwana uku. Wasu hawaye ne suka gangaro mata, har sun gota ta, Jamal ya tsaya ya juyo suka had'a ido. Kai ta langwab'ar ya tako zuwa gabanta ya tsaya yana kallan cikin idonta "I hope ba inda ke miki ciwo yanzu" Kuka ta fashe dashi dan sosai ya bata tausayi, lumshe ido yayi ya bud'e ya zubasu akanta "Kukan menene? Ko akwai inda ke miki ciwo neh" Kai ta girgiza alamar Aa, sake lumshe ido yayi ya bud'e, ji yayi kamar ya rungumota cikinsa "Pls ki daina, ko kinaso nima nayi neh" Batace mai komai ba ta sake fashewa kuka ta bar wajan dasauri. Har ga Allah tausayin halin da yake ciki takeji, da kuma nata, sabda mai tare mata fad'an da wulak'ancin da ake mata yanzu baya nan. Ram ya k'araso yaja hannunshi suka bar wajan dan mutane ne a wajan dank'am suna jiransu dan yin addu'an uku. Bayan anyi addu'an an gama, Ummy na zaune a falo kusada su Najma wayanta ya soma ruri, bak'uwar number ta gani ta d'auka da sallama, Muryan Ram taji yana cewa "Hello Ummy kina jina" "Eh ina jinka" tace a hankali "Tun shekaran jiya rabon da Jamal yaci abinci, pls prepare something for him." "To" tace ya kashe kiran Tashi tayi ta koma side d'insu, rasa abinda zata dafa masa tayi, chan ta d'au dankali ta fere, ta d'ibo kayan miya tayi blending. Aikin take cikin natsuwa, cikin d'an lokaci ta had'a masa faten dankali daya ji kayan lambu sai k'anshi yake. Bayan ta gama ta kira Ram ta fad'a masa ta gama. Dakyar yaja Jamal zuwa side d'in. Duk yanda yayi yaci abincin k'i yayi. Haka ya hak'ura ya mik'e ya fita daga side d'in ya kira Ummy "Dan Allah kiyi k'okari kiga yaci abincin nan, baici komai ba tun sanda akayi rasuwan nan." To tace ta shiga side din a sanyaye. Kan dinning ta samesa zaune ya k'ura ma abincin ido. Tausayinsa ne ya ratsa ta, ta k'arsa taja kujera ta zauna kusa dashi tareda rik'o hannunsa. Ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya kalleta "Ya Jamal meyasa kaki cin abinci, zaka cutar da kanka neh. Dan Allah ka daure kaci" Girgiza mata kai yayi alamar Aa "Addu'a yakamata ka rink'a masa ba tunani bah. Rashin cin abincin ka bashi zaisa ya dawo bah" Rungumota yayi jikinsa ya fashe da kuka kamar yaro, kukan itama ta soma a hankali tana shafa sumar kanshi. Sun dad'e a haka, dakyar ta tsagaita da kukan ta soma lallashin sa. Abincin ta soma bashi a baki yana taunawa dakyar kansa a k'asa. Ba laifi ya d'anci dayawa. Ta tattara takai kayan kitchen ta dawo, d'akinsa ta shiga ta had'a masa ruwan wanka ta fito taja hannunsa zuwa d'akin. Binta kawai yake da ido har ta kaisa d'akin "Ga ruwa a toilet kayi k'okari kayi wanka" Ya nufi toilet d'in a sanyaye, ita kuma ta bud'e Wardrobe d'inshi ta ciro masa kayan da zaisa. Bayan ya fito ya shirya ya sake fita wajansu Ram da sauran abokansa da suke amsar gaisuwan tare. A ranar Ram ya koma kaduna sai kuma Ranar Bakwai zai dawo. Sauran 'yan uwa da abokan arziki duk ranar suka kokoma sai kuma ranar bakwai. Jamal bai shigo gidan ba sai bayan isha'i, side d'insu ya nufa ya haura sama zuwa d'akinsa da wani zazzab'i ne ke neman rufesa. Ummy na falonta taga ya hauro ya shiga d'akinsa sam bai lura da ita a falon bah. Ita kuma tsoro ne ya cikata, dan tunda akayi rasuwan kullum cikin tsoro take da daddare, su Najma ne ke kokarin tayata kwana. To yau suma suka koma saboda makaranta. Jim tayi a nan falon tanata muzurai, tunawa tayi da abincin da ta masa, hakan yasa ta mik'e dasauri tana waiwayan bayanta saboda tsoro. D'akin ta shiga da sallama, kan gado ta hangosa kwance ya k'udundune cikin bargo sai rawar sanyi yake. Dasauri ta k'arasa bakin gadon ta zauna tana kallansa hankali tashe "Ya Jamal bakada lafiya neh" Goshinsa ta tab'a taji zafi sosai, ta mik'e a rud'e "Barin je na fad'ama Mami azo a kaika asibiti" Kallo d'aya zaka mata ka gane hankalinta a tashe yake, dakyar ya iya cewa "No barki kirasu, i will be fine" Idanunta suka ciko da kwalla "Kaga fa jikinka da zafi sosai" D'agowa yayi dakyar yace "Zo kiga abinda zaki min" Ba musu ta matso gabab gadon tana kallansa, janyota yayi ta fad'a kan gadon ya rungumota sosai jikinsa. Idanu Ummy ta zare ta soma mutsu mutsu "Pls ki tsaya, inaso naji d'umin jikinki neh, sanyi nakeji sosai Wife" Yanda yayi maganan sosai ya bata tausayi, ta daina mutsu mutsun,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82