Chapter 30
Chapter 30
an turo miki message" "Ni ina na iya wani karatu balle na karanta" ta k'are maganan tareda turo baki "To bari na karanta miki" Ta gyara zama tana kallan Laurat "Salam! Ina fata gimbiyar tawa tana cikin k'oshin lafiya. Duk da nasan Gimbiyar tawa bana gabanta, anma inaso tasan wani abu guda d'aya..." Ummy ta ja dogon tsaki "Dallah ki bari banason ji" "Haba Ummy bakyau wulak'anta d'an adam, ai sai ki tsaya ki gama sauraran abinda ya rubuto koh" Ta sake turo baki tace "Ina jinki" "Ina sanki Fiyeda yanda nake san kaina, Ina matuk'ar k'aunar ki. Dan Allah ki bani dama na shigo rayuwarki dan na jiyar dake farinciki da annashuwa na rayuwa. ke Alheri ce a rayuwata Ummy! Ke Alheri ce a tare dani. Ina san mu kasance tare koda kuwa zaki rink'a..." "Kai! Nifa na gaji da sauraran ki" Ta mik'e tana cewa "Muje wajan Inna dan tace na dawo d'an anjima" Laurat ta saki Murmushi ta mik'e suka tafi gidan Innan. Ana saura kwana uku 'yan Uwan Baba dana Mama suka sake dawowa biki, kan kace me gidan ya cika sosai da mutanen k'auye. Dole Ummy da Laurat suka tattara inasu inasu suka dawo gidan Inna. _dan jin yanda bikin Jamaludeen da Jaleelah da kuma Mabrookah zai kasance sai ku bini a page na gaba_ ```Zaku min afuwan jina shiru kwana biyu, hakan ya faru bisa rashin Lafiyan danake D'an fama dashi. Sai ku sakani a addu'a``` Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* _Naga sak'on Addu'an ku da dama, ina godiya Allah ya saka da Alkhairi_ ```Maman Ahmad, Ayoush Gidos, Maman Abba, Tintima Shuwa and all My Fans Grp``` Ina godiya Page 34 Dole Ummy da Laurat suka tattara inasu inasu suka dawo gidan Inna. Bahar na zaune a cikin gida yana waya suka shigo, Inna dake tsakar gida tace "Maraba da Amarya" Ummy ta turo baki tana gungunai, ta nemi guri kusada Innan ta zauna "Ni fa bah amarya bace" "Ke ko kike amarya Ummy, ni abinda ma ke damuna wannan Raman da kikayi a haka za'ayi bikin" Laurat tace "Nima dai haka nace" Dai dai lokacin Bahar ya gama wayan da yake yana cewa "Innan mu Ya Bilal ne yace na gaishe ki" "Aa to madallah ina amsa wah" Idanun Ummy suka cika da hawaye, Bahar dake gefe yace "Amarya kinsha k'anshi, d'azu nake ganin katin Programs d'in bikin hannun wani abokina. Allah ya sanya alkhairi" Batace mai komai ba sai ma kauda kai datayi gefe. Bahar ya mik'e ya fita, tana ganin haka ta mik'e dasauri tabi bayanshi "Bahar dan Allah numbern Ya Bilal zaka bani" Ba musu ya bata numbern ta dawo gida cikeda farinciki. Da yanma suna zaune itada Laurat wayan da Ramadhan ya bata ya hau ruri, Laurat ta d'au wayan tana cewa number ce. "Tho ni ai ko d'aukan kiran ban iya bah" Dariya Laurat ta mata ta nuna mata yanda ake d'auka, karawa a kunne tayi Muryan Jamal ya daki dodon kunnenta "Salam Amarya tah" Sunan da ya kirata dashi sosai taji dad'in shi ta d'anyi murmushi tabace komai bah "I know kina jina kodai saina sayi muryan neh" Nan ma shirun ta sakeyi, ya d'an sassauta murya yace "Kiyi hak'uri muna k'ofar gida nida Abokai na, pls badan niba ki fito" Ta yanke kiran tana kallan Laurat tana turo baki "Wai Ya Jamal ne da abokansa a k'ofar gida" Laurat ta mik'e dasauri tana gyara gyalen kanta, tashi to muje Myb zasu mana magana ne akan abinda zamuyi. Ummy tayi turus alamar bazata mik'e bah, Inna dake tsakar gida tace "Wai Ummy baji nayi kince Jamalu na k'ofar gida bah" Turo baki ta sakeyi ta mik'e tasa hijab suka fito tana turo baki, su Biyar ne jingine jikin motar. Kallo d'aya ta musu ta d'ukar dakai, ji tayi tana jin nauyinsu. Laurat ta d'an tab'ata murya chan k'asa tace "Dan Allah kar dai ki dizga shi a gabansu" Hannun Laurat ta rik'e suka k'araso wajan, kunyan su Ummyn keji sosai ta b'oye bayan Laurat tana Murmushi. Laurat tace "Sannunku da zuwa ina yinin ku" Karaf Ramadhan yace "Lah! Abin kunya, ki ma daina jin kunyan wad'an nan" Ya nuna sauran abokanan yana cewa "Wad'an nan da kike gani duk shaki yayi neh" D'aya daga cikinsu mai suna Mifzal yace "Lallai Ram kaci abinci, anma ba komai zamu rama" Suka sake kwashewa da dariya, shidai Jamal na gefe sai kallan Gimbiyar tasa yake yana murmushi. Dakyar Ummy ta iya cewa "Ina yinin ku" d'aya daga cikinsu yace "Oh ashe ba haka nan kawai baneh take mana rowan muryan nata" "Kai wai ya haka, kuyi abinda ya kawo ku dallah mu tafi" cewar Jamal yana hararansu Mifzal yace "Ni ban tab'a ganin Ango ma mara kunya irinka bah, waya cema ango na biyo abokai wajan k'awaye" Harara Jamal ya sake wurga mai, Laurat da Ummy dariya suke musu k'asa k'asa Taseem yace "Ni fah tarko na ne ma ya kama kurciya a nan wajan Wallahi" Ram ya had'e rai yace "Kai lets be serious" Mifzal yace "Saidai bamu san sunan Malaman bah" Laura tace "Sunana Laurat" "Woaw nice name" cewar Taseem yana gyad'a kai Ram yace "Dame dame kuke buk'ata wajan hidimar bikin naku" "Kawai walima zamuyi shikenan" Taseem yace "Tho kamar nawa kuke b'ukata" Laurat ta sake cewa "Duk abinda Allah ya hore muku babu matsala" Take Taseem yasa hannu a aljihu ya ciro bandir d'in yan d'ari biyar ya mik'a mata. Ansa tayi ta musu godiya, itadai Ummy har lokacin tana bayan Laurat dan kasa had'a ido tayi dasu. Takowa Jamal ya soma yi har zuwa bayan Laurat, ya kamo hannun Ummy batareda yace komai ba ya kalli su Mifzal yace "Idan kun gama ku fad'a mana" Ganin tana k'okarin turje masa yasa ya d'auketa chak ya sakata a seat d'in bayan motan Ram shima ya shiga suka kulle ya kulle k'ofan. Baki bud'e su Ram suka bisu da ido. Taseem ya dawo kusada Laurat ya tsaya suna hira. Ram ya sake had'e rai ya matsa chan gefe yana waya fuska a had'e. Ummy ko ido ta zaro tana kallansa "Dan Allah ka bud'emin na fita" Ya janyota jikinshi yana y'ar murmushi "Wai mena miki ne Yasa baki sona" Ta turo baki tana tureshi daga jikinta. D'an dariya yayi k'asa k'asa yana kallanta "Why are uh pretending, ni nasani kina sona. C'ommon ki daina, I love uh so much and i know uh love me too" Ta turesa da k'arfi tana kokarin bud'e kofan, hannunta yayi saurin rik'ewa ya d'aura mata katuna a hannu yace "Ga katu nan ki da zaki raba" Ya d'auko wani k'atan leda ya d'aura kan cinyanta tace "Gobe akwai Dinner, inaso kisa d'aya daga cikinsu. Jibi kuma akwai Kamu. Zamu zo nida abokaina mu d'auke ki" Batace komai ba sai bin ledan datake da kallo. Kwankwasa windown motan aka soma, Ya rik'o hannunta tareda yin kissing d'inshi a hankali, zame hannunta tayi dasauri tana turo baki "I love uh my pearl" Saurin bud'e kofan tayi ta fito rik'e da ledan da katunan, dakyar ta iya sallama da abokan nasa suka shige gidan Inna. Ram ko kamar ya fashe saboda b'acin rai. _manage
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82