Skip to content

Chapter 33

Chapter 33

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

dakai tun ba yau bah, nasan...." Mami ta shigo falon a fusace tama cewa "Wallahi abinda kakemin Alhaji banajin dad'in shi" Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Miss Eshaa* na baki wannan shafin kyautah Page 37 n 38 "Wallahi abinda kakemin Alhaji banajin dad'in shi" Abba da Jamal suka d'ago suna kallanta, kusada Abba ta zauna ta cigaba da cewa "Haba Alhaji, meyasa kake zartar da hukunci ba tareda ka tambayi ta bakina bah, kamar yanda kake da iko da Yaran nan naka nima tunda ni ce uwarsa" "To me kuma akayi Maimuna" "Meyasa zakace bazasu zauna a sabon gidasu bah sai a nan" Abba yayi murmushi yace "Uwargida sarautar Mata, to maida wuk'ar, ai ba wani abu nace bah. Inaso ne naga kamun ludayin zaman nasu sannan sai su koma nasu gidan" Shiru tayi tana turo baki Jamal ya mik'a mata takardun gidan da Abba ya basa harda makulle yana cewa "Mamina ki tayani farinciki, Abba ya bani gida" Nan da nan b'acin ran Mami ya kau ta soma murna tana "Ah! Lallai Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i" Takardan ta amsa tana dubawa tana farinciki. Abba ya kalli Jamal dake durk'ushe har lokacin yace "B'angaren chan na k'arshe a nan zaku zauna, komai na buk'ata akwai. Sannan ita Ummy tana sama tunda itace Uwargida, ita kuma Mabrookah tana k'asa" Kanshi k'asa ya amsa tareda godiya. Mami ta mik'a masa takardun ya mik'e ya fita. Wayanshi ya ciro a aljihu dan yana silent, nan yaga missed calls d'insu Ram dayawa. Murmushi yayi ya fita haraban gidan, nan fa suka masa cha, shidai baice komai bah saima Taseem daya kalla yana cewa "Yanzu dan iskanci ace har k'arfe takwas baku je d'auko min amarya ta bah" "Kuji mana wannan guy d'in, tun d'azu fah muke jiranka a nan ka bamu go ahead" cewar Mifzal. "To shikenan kuje, Anma Ram nasan kai ba hankali ka cika bah, ka d'auko min matana a hankali banasan tafiyar ganganci" Tunda ya fara magana Ram ya saki baki yana kallansa har ya gama. K'wafa yayi ya shiga motarsa, sauran ma duk suka shishiga suka d'au hanyan gidansu Ummy. Tun bayan la'asar Ummyn ta dawo gidansu tana kukan rabuwa da Mamanta. Wani sabon kuka ta saki lokacin da aka kaita gaban Maman nata dan ta mata fad'a. Kuka ne ke k'okarin kufce ma Maman, dakyar ta daure ta mata nasiha mai ratsa jiki, gidansu Bilal aka kaita, Itama Inna ta mata nasiha sosai sannan aka fito da ita. Suna shiga cikin gida su Ram suka iso k'ofar gidan. Wani sabon kuka Ummy ta kece dashi tana kokarin turjewa daga rik'on da Inna ta mata, da k'arfi ka kwace ta shiga ta rungume Mama tana kuka sosai "Mama idan na tafi wa zai kula dake, dan Allah kar ki bari a tafi dani" Duk dauriya irin ta Mama saida tayi k'walla tana shafan k'an 'yar nata "Allah na tare dani Ummy. Darajar Mace gidan mijinta, ki tafi gidanki. Ina miki fatan Alheri Ummy" Ummyn ta sake rushewa da kuka, dakyar aka samu aka b'anb'areta daga jikin Mama tanata kuka, Inna da kanta ta sakata a mota itama ta shiga dan Mama ta bata amanar 'yar nata tun bayan rasuwan Baba. Su Twins da Laurat duk motan Abdulhakam abokin Jamal suka bi da kuma sauran 'yan uwa da abokan arziki. A jere motocin suka shigo cikin gidan, wani malalacin murmushi Ram ya saki sanda ya hango Jamal tsaye chan wajan garden ya kasa ya tsare. A k'ofar side d'in Mami Ram yayi parking, Inna da kanta ta fito rik'e da hannun Ummy bayan ta gyara mata lulub'in dake kanta. Jagora Aunty Zainab ta musu har zuwa d'akin Mami. Bayan an gaisa Inna ta damk'a amanar Ummy a hannun Mamin, ba yabo ba falasa Mamin ta amshe su tareda adduan Allah basu zaman Lafiya. Suna fitowa aka musu jagora zuwa side d'in da zasu zauna, koda suka shiga sun samu mutane a ciki da alama an kai Mabrookah neh. Aunty Zainab ta musu jagora zuwa sama har d'akin Ummyn. 'yan kai amarya sai santin gidan suke dan Abba ya kashe kud'i sosai wajan k'awata musu b'angaren nasu da funitures masu kyau. Tareda kayan kicin masu tsada da kyan gaske. Da kuka Ummy ta rabu da Inna bayan ta k'ara mata nasiha sosai. Ya rage daga ita sai su Twins dan tunda aka kawo Ummyn Laurat ta sulale ta koma bakin aikinta. Hira Twins keta Jan Ummyn dashi anma hankalinta baya wajansu sai neman wayan Bilal take switch off. Takai awa d'aya tana kira baya zuwa, wani kuka ne ya kufce mata ta kife kan makeken gadonta tana kuka sosai. Najma ta soma lallashinta anma kamar k'ara zugata take. Suna cikin haka aka turo k'ofar d'akin, Najma da Najwa suka d'ago suna kallan k'ofan. Wasu 'yan mata ne suka shigo su uku suna bin d'akin da kallo tareda yatsine fuska, Najma uwar rashin hak'uri tace "Lapia malamai kuka shigo mana d'aki bah sallama" Ba wacce ta tanka ta sai zagayen d'akin da sukeyi suna cigaba da yatsine fuska, Ummy ta d'ago tana binsu da kallo har lokacin k'walla na gangara a idonta. "Warning mukazo mu baki, karki sake ki shiga harkan Mabroo dan ba sa'arki baneh" cewar d'aya daga cikinsu "Dalla malamai ku fitan mana daga d'aki, kun shigo sai warin gardi kuke ga wani shegen attachment sai d'oyi" Cewar Najma A harzuk'e d'aya daga cikinsu ta nufota tareda chakume mata gaban riga, ganin haka yasa Ummy sake rak'ubewa tana zubar da kwalla Ta cigaba da cewa "Ke kinsan mu waye da kike gaya mana magana" Najwa itama ta mik'e rai b'ace tace "Karuwai mana dan bakuda banbanci dasu, wallahi kiyi maza ki sakar min 'yar uwa idan ba haka ba nayi maganinki" D'aya daga cikinsu ta janye hannunta daga gaban rigan Najma tana cewa "Karki biyema wad'an nan yaran kuzo muje kawai" Ta kama hannunta da d'ayar suka bar d'akin rai b'ace. Najma tace "Lallai Wallahi Ummy sai kin dage" "Ni Wallahi tausayi ma ta soma bani" cewar Najwa tana kallan Ummy daketa zubar da k'walla. Suna nan zaune har wuraren k'arfe goma, da wayo suka sulale suka bar Ummyn tana sharb'ar Hawaye. A bangaren Ango Jamal kuwa yana falon side d'in Abba shida abokansa, lokaci lokaci yakan kalli Rolex d'in hannunsa yana d'an tsaki a hankali, duk abinda yake Abduolhakam abokinsa na lura dashi, shi ya fara mik'ewa yace "Kai ku tashi mukai angon nan dan naga alamun idan bamu kaisa ba za kai kansa neh" Ram yad'an b'ata fuska yace "Wajan wa za'a kaisa tho" Karaf Jamal yace "Wajan Baeby na mana, kasan itace uwargida tunda ita na fara aure" Dukansu suka saki baki suna kallansa da mamaki "Ya da kallo" Ya mik'e yad'au ledan dake kusada Mifzal yace "Dallah ku taso muje" Shine a gaba suna binsa a baya sai tsiya suke masa shi dai baice komai ba sai murmushin da yake. A hankali ya tura k'ofan d'akin ya shiga da sallama, wani sanyaiyar k'anshi ne ya musu sallama, Ya matsa dasauri Taseem ya soma shiga sannan Mifzal sai Jamal d'in da kuma sauran abokanan nasa. Tana kwance tana aikin kuka taji sallamansu, dasauri ta

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82