Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

d'ago dasauri yana kallanta da murmushi "Aa 'yar nan bashi kawai keda kike naki aikin" Tad'anyi Murmushi ta kwashe kayan tana cewa "Ba komai Baba ai zan iya kawo kaga" Albarka ya soma sa mata tareda tambayan sunanta, ta fad'amai yace shi yana aikin ba flower ruwa neh a gidan. Cikin y'an mintina ta gama wankin ta d'auraye ta shanya ta koma sama. D'akin Mami ta shiga, d'akin tsaf yake ba datti sai k'anshi dake tashi, bedsheet d'in taja da niyar karkad'ewa, bandle d'in dari biyar ne ya fad'o ta matsa dasauri da mamaki tana kallan kud'in, jim tayi sannan ta d'au kud'in ta aje saida ta gyara d'akin tsaf ta wanke toilet sannan ta d'au kud'in ta aje k'arkashin filo ta fito bayan ta rufe d'akin da key. Saukowa tayi ta nufi babban kicin d'in side d'in, ma'aikata ta gani sunata aiki duka sanye da irin kayan jikin Laurat, gaidasu tayi ta k'arasa inda Laurat d'in ke tsaye tana wanke wanken kayan da akayi breakfast dasu a sink. "Ummy har kin gama naki aikin?" Kai Ummy ta gyad'a tace "Na gama, nayi sauri koh?" "Sosai ma" Laurat tace K'aran bell sukaji Laurat ta wanke hannunta taja hannun Ummy tana cewa "Lokacin amsan Breakfast yayi muje" Binta Ummy tayi har zuwa wani runfa chan bayan gidan, nan Ummy ta baza ido ganin ma'aikata daban daban, dukansu sanye da uniform wasu da Blue riga da black wando, wasu Green riga, wasu pink. Sakin baki tayi ganin ma'aikatan gidan harda turawa su hud'u, maza uku mace d'aya, su kuma suna sanye da Arsh riga da bak'in wando. Tab'ata Laurat tayi tana nuna mata plate, a tare suka d'auka suka soma bin layin amsar abincin. Soyaiyar doyace da k'wai sai Slice d'in bread guda uku da Tea. Ma'aikatan sai kallan Ummy suke ganinta cikinsu kuma babu uniform, suna amsa itada Laurat suka shiga d'akin Ummy suka zauna suka soma karyawa. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:23 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 10 Bayan sun gama Laurat ta soma bin d'akin da kallo cikeda sha'awa "Keh kam kinji dad'inki, d'akinki daban" "Ku ya naku yake?" Ummy ta tambayeta "Tab aimu d'aki d'aya mutum biyar neh, ko ku nawa neh a b'angaren da kuke aiki to d'akinku d'aya" Gyad'a kai Ummy tayi sannan tace "Niko inaso na miki wani tambaya Laurat" Gyara zama tayi sannan tace "Ina jinki" Ummy ta cigaba da cewa "Naga Kunasa Uniform ma'aikatan kicin, Sauran dana gani ma'aikatan menene" Laurat tad'anyi murmushi tace "Ko wani b'angare da uniform d'insa, bakiga ko masu gadin gidan nan da uniform ba" Ummy ta gyad'a kai, Laurat tace "Wannan matsiyaciyar Mabrookan ce, da ba'asa Uniform itace ta kawo wannan tsurfan" "Na lura batada kirki ko kad'an" Laurat tayi dariya tace "Keda kikazo ma jiya knan har kin fahimta" "Tho wad'an nan turawan fa dana gani" Dasauri Laurat ta mik'e tana cewa "Ki bari zamuyi magana anjima, barin koma bakin aikina gwara ke har kin gama naki" Itama Ummyn ta mik'e "Barinzo muje na tayaki aikin" Kicin d'in suka nufa Laurat ta cigaba da wanke wankenta Ummy na mata d'auraya. Shanyanta ta kwaso ta nunke ta kai mata d'aki ta koma kicin inda Laurat take. Haka Ummy ta cigaba da aikinta a gidan, kullum sai taga kud'i a k'arkashin pillown Mami saidai ta aje gefe data gama ta mayar inda ta aje. Kullum tana gama aikinta zata tafi kicin su cigaba da aiki da Laurat. Hurama Mami wuta Mabrookah tayi dole akayi ma Ummy uniform dan itama asan cewa y'ar aiki ce a gidan, badan taso ba aka d'inka ma Ummyn Purple riga da bak'in wando wanda ita kad'aice mai irin Uniform d'in duk cikin masu aikin. Yau Sati, da wuri Ummy ta gama ayukanta wuraren k'arfe Sha biyu, Mami ta samu a falo tana rubuce rubuce a wani takarda, ta rusunna tace "Sannu da hutawa Hajiya" D'agowa Mamin tayi tace "Yauwa sannu Ummy" Jim tayi sannan tace "Hajiya na shirya zan tafi gida" "Ohh kinga ko na manta da maganan zuwa gida yin weekend" Handbag d'inta ta d'auko dake gefenta ta ciro dubu uku ta mika mata tana cewa "Gashi kiyi kud'in mota ki gaidasu" Godiya Ummy ta mata ta mik'e ta koma d'akinta, Uniform ta cire tasaka doguwar rigar atampha tasaka hijabinta har k'asa ta fito, Laurat tama sallama da sauran ma'aikatan gidan, tama Baba mai ba flower ruwa sallama ta fito. Saida ta biya kasuwa tayi sayaiyar kayan miya yarda kaza guda d'aya ta nufi gida. Mama da Baba sunyi farinciki sosai da ganinta, ranar ita ta musu girki sai sa mata albarka sukeyi, sai bayan isha sannan ta shiga gidansu Bilal, itama Umman Bilal tayi murna da ganinta, d'ari biyar ta bata tanata godiya sun d'an tab'a hira sannan tamata sallama ta dawo gida. Ranar sunday sai da yanma sannan ta koma gidan aikinta, Ranar tasha fad'a sosai wajan Mabrookah kan k'in komawanta da wuri. Sadda kai kawai tayi k'asa harta gama fad'anta tayi gaba sannan ta shiga d'akinta. Washe gari da safe kamar kullum Ummy ta fito dan gaida Hajiya da kuma Mabrookah, yau harda Alhaji ta gani suna breakfast d'in tare, Yau neh karo na biyu da ta tab'a ganin Alhajin gidan, daga gani ko ba'a fad'ama ba kasan babban mutum neh, Tsugunawa tayi har k'asa ta gaidasu duka suka amsa Alhaji yad'au Briefcase d'inshi ya musu sallama ya fita. Mabrookah ma ta mik'e tadau jakanta sai hararan Ummyn take tama Mami sallama ta fita. Har Ummy ta tashi Mami ta kira sunanta tareda nuna mata kujera nan kan dinning, ba musu ta zauna kanta k'asa Mami tace "Na gwada ki da dama Ummy kuma kinci jarabawar dana miki, Lallai kinada gaskiya da rik'on amana" Duk'ar dakai Ummyn tayi tana murza zoben dake hannunta, Hajiya ta cigaba da cewa "Inaso na k'ara miki wani aiki guda d'aya, duk da nasan wannan ba tsarin mai aiki baneh. Anma yanayin aikina neh banida lokaci. Inaso ki rink'a gyara ma Alhaji d'aki duk safiya" Ummy tad'an d'ago da mamaki tana kallanta, lallaima Matar nan ita ina ta tab'a ganin wata ta gyara ma mutum d'akin miji. "Kina jina" cewar Hajiya tana kallanta "Eh Hajiya" Keyn d'akin ta mik'a mata tana cewa "Ga keyn d'akin ya zamana yana hannunki. Karnaji ko naga ba daidai ba ina fatar kin ganeh" Ummy ta gyad'a kai "Insha Allahu Hajiya zan kiyaye" Batace komai ba ta Haura sama ta d'auko Handbag d'inta ta fita. Kallan Keyn Ummy ketayi tana jujuyashi a hannunta, a haka ta shiga kicin inda su Laurat suke, zaune ta sameta tana yanka kankana ta zauna kusada ita "Kinsan menene?" Cewar Ummy tana kallan Laurat "Aa saikin fad'a" Ajiyar zuciya Ummy ta sauke ta ciro keyn da Hajiya ta bata ta nunama Laurat tace "Wai keyn d'akin Alhaji Hajiya ta bani na rink'a gyara masa" Magana sukaji daga bayansu ana cewa "Lallai kam kina cikin tsaka mai muya" A tare suka juya sukaga wata y'ar dattijuwa wacce zatayi sa'ar Hajiyan saidai Ita Uniform d'inta Green neh, ta k'araso ta dafa Ummyn tace "Baki ganeni ba koh" Kai Ummy ta girgiza alamar eh, Matar tayi murmushi tace "Ni ce wacce na ganki Ranar da

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82