Chapter 55
Chapter 55
ya mik'e dasauri ya mik'a ma d'an fulanin hannu "Mungode sosai" Shima Ram ya mik'a masa hannun, d'an fulani ko sai godiya yake. A mota suka samu Jamal jingine da seat ya lumshe ido, jin motsinsu yasa ya bud'e ido ahankali. Basu ce masa komai ba shima haka, suka shiga ya tada suka bar anguwan. Saida sukayi nisa sannan Mifzal ya soma masa bayanin yanda sukayi da Mai shago, mamaki ne a fuskansa sanda yaji Bilal nashan taba. Police station suka koma suka kai report d'in da kuma record d'in maganan su da d'an fulani. Ummy kuwa irin jiya ce ta faru, aiki tayi tuk'uru duk ta galabaice ga wani ciwon ciki dake damunta. Yauma saida tayi aikin tas sannan ta wuce side d'insu tana tafiya da k'yar. Yauma kamar jiya saida suka d'anyi daru itada Jamal akan k'in d'aukan wayansa da batayi bah. Washe gari ko zazzab'i ne da ciwon jiki ya rufeta. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 64 n 65 Washe gari ko zazzab'i ne da ciwon jiki ya rufeta, sosai, har k'arfe sha d'aya na safe bata tashi bah. Ran Aunty Faty idan yayi dubu ya b'aci. Da kanta ta shigo side d'in dan Mabrookah ta tafi makarantah. K'ofan d'akin ta banko ta shigo, k'udundune ta sameta kan gado tana rawar sanyi sosai. Duk da yanda take kad'uwa hakan bai hana Aunty Faty d'aka mata duka a k'afa ba. Ba shiri ta mik'e zaune dakyar, idanunta na wani lumshewa "Uban me yau ya hanaki zuwa aiki" Ta fad'a tana huci. Cikin Kuka Ummyn tace "Dan Allah kiyi hak'uri Wallahi banajin dad'i neh bazam iya aikin bah" Wani duka Aunty Faty takai mata a baki har saida bakin ya fashe, ta dafe wajan tana kuka sosai "Saboda bakida kunya, kin rik'a harni kike cema bazaki iya aikin bah. To wallahi nabaki nan da minti biyar in ganki a falon chan" Fuuuu ta juya tabar d'akin tana sababi, wani marayan kuka Ummyn ta fashe dashi, ga wani irin sarawa da kanta keyi, dakyar ta iya mik'ewa ta fito ta nufi side d'in tana tafiya a hankali. Aunty Faty na isa ta labarta ma Mami abinda ke faruwa sannan tace "Bari tazo na bata ruwan nan, sai nace tasha magani dashi, indai tasha an gama. Haihuwa saidai taji anayi" Karaf a kunnen Ummyn, tad'anyi jim a k'ofar falon sannan ta shiga da sallama, kini kini darai Mami tayi, ta tsugunna ta gaidata. Anma bata amsa bah. Haurawa sama tasoma yi a hankali dan ta fara aikinta, Aunty Faty ta kwalla mata kira ta sauko da d'an sauri. Bottle water ta mik'a mata da wani capsule tace tasha, saida tad'anyi jim sannan tace "Ban karya bah" "To idan kin karya sai kisha" Cewar Aunty Fatyn, ajiyar zuciya tayi ta haura sama da maganin, zubar dashi tayi a toilet, ta saka maganin a WC tayi flushing. Tana aikin jiri na d'ibanta, so uku tana fad'uwa saboda jiri. Haka tayi aikin dakyar tana kuka. A wahale ta dawo side d'insu ta fad'a kan gado tana kuka tare da kiran sunan Jamal. A b'angaren su Jamal kuwa washe gari da daddare suka koma layin tare da rakiyar wasu daga cikin 'yan sanda anma bada uniform bah. Nan sukaga wad'an nan murd'a murd'an bak'akken mutanen da D'an fulani yayi maganansu. Suna nan b'obb'oye sukaga Alhajin da Bilal sun fito sun shiga motoci suma mutanen sun shiga suka bar anguwan a guje. Binsu su Jamal suka somayi anma kamin kace me har sun b'ace musu. Haka suka koma hotel d'in da suka sauka kowa da abinda yake sak'awa a ransa. Washe gari Tuesday, basu samu ganin Lawyern Abba ba sai da yanma, nan yake nuna alhininsa na rasuwar Abba dan baya k'asar tun lokacin. Jamal ne ya tambayesa dangane da bashin da Alh Tijjani yake bin Abba, ba tare da b'ata lokaci ba Lawyern ya basa tabbacin akwai bashin. Haka Jamal ya dawo jiki a sanyaye, Ram dake gefensa zaune yace "Yanzu Jamal ya xa'ayi maganan Bashin nan" Wani ajiyan zuciya ya sauke yace "Nima kaina bansani bah Ram, i knw nothing akan dukiyar Abba. Kuma kaji shima Lawyern yace baisan komai bah" Mifzal ya gyara zama yace "To why not ka koma gida ka binciki D'akinsa, Myb ka samu wani abu da zaiyi guiding d'inka zuwa inda abubuwan nasa suke" Jamal ya gyad'a kai alamar gamsuwa. Wuta ya hura yak'i bari su kwana, a ranar suka d'au hanyan Zaria saidai sun bar Mifzal anchan dan bai gama bincikensa bah. Saida ya sauke Ram a kaduna sannan ya d'au hanyan zaria. Karfe goma da rabi ya isa gidan. Bai shiga side d'in Mami ba dan yasan sunyi Bacci, side d'insu ya wuce yasa keyn d'insa ya bud'e ya shiga. D'akinsa ya wuce kai tsaye yayi wanka ya sauya kayansa sannan ya shiga na Ummy. Kwance ya sameta kud'undune cikin bargo tana rawar sanyi sai yamutsa fuska take. Ya hau kan gadon ya rungumota jikinsa a haka sukayi baccin. Da asubah sosai tayi mamakin ganinsa, ya shafa gefen fuskanta yana binta da kallo "Wife kinga yanda kika rame? Kin k'arayin ciwo neh" Girgiza masa kai tayi alamar Aa idanunta cike da kwalla. Da taimakonsa tayi wanka ya gasa mata jikinta sosai sai kuka take dan jikin mata yayi tsami. Da kanshi ya musu breakfast sukaci. Mabrookah na k'asa ta jiyo muryansa, da mamaki ta haura ta ganshi tsugunne a k'asa yana matsa mata k'afa sai dariya take masa. Ran Mabrookah in yayi dubu ya b'aci, rai b'ace ta shiga falonsu Mami, kan dinning ta xauna tana turo baki "Yaya dai" cewar Mami "Ya Jamal ne ya dawo yana chan yare da wannan maiyar yana matsa mata k'afa" "What!"cewar Mami "Har Jamal ya dawo ya kasa zuwa ya gaishe ni? Lallai na yarda Ummy ta shanye min d'a" Mabrookah ta sake zumb'ura baki tana kallan Aunty Faty "Ni babban abinda ke damuna ma, Mummy kince in tasha ruwan nan da akasa magani cikin zai zube anma har yanzu naji shiru" Aunty Faty ta gyara xama "Nima abin na bani mamaki" Sallaman Jamal da Ummy ne ya katse su, Mami ta sake had'a rai tare da amsa gaisuwan. Zama yayi kamar kullun sannan ya gaida su, Ummy ta tsugunna ta gaishe su, babu wanda ya amsa mata, hakan sam baima Jamal dad'i bah. Abin da yafara tambaya shine "Mami yau naji gidan shiru Ina Ma'aikatan neh bangansu bah" "Na sallamesu" cewar Mami Ya zaro ido da mamaki "Saboda me Mami" Ta sake b'ata fuska "Saboda bamu da abinda zamu cigaba da rik'esu" Bai sake cewa komai ba dan ransa ya b'aci sosai. "Ka dawo baka iya zuwa ka duba halin danake ciki ba anma ka tafi wajan matarka" Ya sassauta murya "Kiyi hak'uri Mami ban dawo da wuri bah cikin dare ne kuma nasan kinji bacci" Itadai Ummy kanta na k'asa. Aunty Faty ta daka mata tsawa "Ke! Akuya tashi kiba Uwa da d'a wuri suyi magana" Dasauri ta mik'e ta fita, Ja juya ransa b'ace wajan Aunty Fatyn "Matata ba Akuya bace, karki k'ara kiran matata da wannan sunan" Baki bud'e dukansu suke kallansa "Jamal yayar tawa kake gayama irin wannan maganan" "Mami kiyi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82