Skip to content

Chapter 34

Chapter 34

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

mik'e ta gyara zama tareda gyara zaman gyalenta. Ram na shiga ya baje k'asan tiles d'in d'akin "Wash! Nidai na kama gurin kwana" "Aina!" Jamal ya zaro ido daidai lokacin daya zauna kusada Ummyn "A nan mana" Harara ya wurga mai, Mifzal yace "Sannu amarya bah magana" Shiru batace komai ba sai sheshek'an kuka da yake a hankali "Taya amarya zata maka magana ba'a sayi baki bah" cewar Taseem yana kallansa. Mifzal yace "Au haka neh fah" Yasa hannu a aljihu ya ciro rafan y'an d'ari biyu ya aje mata a kan gadon. Duk da haka dai bata iya cewa komai ba har lokacin kuka take a hankali wanda Jamal d'in kawai ke jiyota. Shakiyancin sukayi tayi sannan suka musu sallama suka tafi. Har bakin motocin su Jamal ya rakasu sannan ya dawo. Harya haura sama ya dawo yana tab'e baki ya nufi d'akin Mabrookah. Kan gadonta ya sameta tana sanye da wasu fitinanun night wears. Gabansa na ya fad'i ya kauda kai tareda k'arasawa bakin gadon "Haba Mijina tun d'aku fa nake jiran shigowanka naji shiru kuma bayan naji hayaniyarku" Ta matso kusada shi tana san manna jikinta da nasa, dasauri ya janye jikinsa yana yatsine fuska "Nazo ne naga lafiyarki, sannan na shaida miki yau a d'akin Ummy zan kwana tunda ita ce babba, ita..." "Haba Ya Jamal wanne irin magana kakeyi, ni fa matarka ce kamar yanda take matarka" "Anma kinsan dai saida aka fara d'aura aurenmu sannan aka d'aura naki koh" Turo baki tayi tana bubuga hannuwanta akan gadon alamar shagwab'a. A hankali yace "Saida safe koh" Ya mik'e tai saurin rik'e gefen rigansa tana magana cikin shagwab'a "Ina wai zaka ni fa wallahi tsoro nakeji" Janye rigansa yayi ya hasale yana kallanta "Da dakike kwana ke kad'ai meya kamaki" Yad'anja guntun tsaki ya bar d'akin dasauri. Sama ya haura zuwa d'akin Ummy, yanda ya barta haka ya dawo ya sameta saidai yanzu ba kuka take ba sai ajiyar zuciya datake saukewa lokaci zuwa lokaci. Kan gadon ya zauna ya matso kusada ita tareda sa hannu ya janye mayafin dake kanta. Kawar da fuska tayi dasauri, yayi murmushi tareda d'ago fuskanta da hannunsa. Ta lumshe ido dasauri hawaye suka gangaro daga idanunta "Oh God! Ya zanyi dake Baeby, dan Allah ki daina kukan nan. Bud'e idanunki ki kalleni" Bud'e idon tayi a hankali ta sauke su k'asa ta fashe da kuka. Batareda b'ata lokaci bah ya rungumota jikinsa yana shafa bayanta a hankali, turesa ta soma yi tana kuka mai sauti "Meye haka ka sakeni banaso" Janye jikinshi yayi daga nata yana kallanta da narkakun idanunsa "Ni mai sanki neh, i so much love uh Baeby, pls karki ce baki sona dan zan iya shiga damuwa mai tsanani. Ina sanki sosai" Ta d'ago jajayen idanunta tana kallansa da kuka "Idan nayi haka na karya alkawari, Ya Bilal ya sadaukar da abubuwa da dama dan rayuwata dana iyayena su inganta, ya..." "Pls wannan maganan ya wuce, i know nafi shi sanki" Ta d'ago jajayen idanunta ta zubasu kan nashi "Babu namijin dake sona kamar Ya Bilal, shine wan..." Saurin katseta yayi tareda saukowa daga kan gadon "Ki aje a ranki ni mai sanki neh, kisa a ranki ni mai baki farinciki neh. Bandamu da ko ki soni bah, sanda nake miki ya ishemu. And pls ki daina min maganan Bilal hakan na k'ona raina" Bai jira mai zatace ba ya bar d'akin zuwa nashi dake nan saman. Ummy Abduol✍🏻 [3/22, 5:21 AM] 0mmer Farouk: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 39 Bai jira mai zatace ba ya bar d'akin zuwa nashi dake nan saman. Kuka Ummyn ta fashe dashi tana dukan gadon da duk iya k'arfinta, tana cikin kukan bacci mai nauyi ya d'auketa nan kan gadon. Jamal ko bacci ne yayi k'aura daga idonsa, sosai hankalinshi ke tashi a duk lokacin da Ummy ta ambaci sunan Bilal. Kukansa ya soma kaiwa wajan ubangiji sai gefen asuba sannan ya samu bacci ya d'aukeshi a kan sallayan. Da safe da wuri Ummy tayi wanka ta gyara d'akinta tsaf da toilet dan tasan a aladar hausa washe garin da aka kawo amarya anayin bud'an kai. Hakan ce ko ta kasance, 'yan uwanta da abokan arziki duk sunzo da kayan lefenta sai gara da Baba sallau da Baba Tanko suka mata wanda bai taka kara ya karya bah. Ango Jamal bai farka ba sai k'arfe shad'aya ta kwata na safe, shima hayaniyar jama'a ce tasa ya farkan. "Subhanallahi!" Ya fad'a ya mik'e dasauri ya fad'a toilet, wanka yayi tareda d'auro alwala ya fito ya tada sallah. Yana idarwa ya shirya cikin bak'in yadi mai sharashara, d'inkin rigan daidai guiwa, sosai kayan suka fito da kyansa saidai kalli d'aya zakama fuskansa ka gane yana cikin damuwa. Had'adiyar Lace Ummyn tasa cikin na kayan lefenta, Najwa ce tayi mata makeup tayi kyau sosai, Itama Amarya Mabrookah ta had'e cikin atampa lemon green d'inkin dogon riga, fuskan nan nata yasha heavy makeup har tayi wani iri kamar aljana. Anyi bud'an kai lafiya tareda walima, ango na side d'in Abba shida abokansa suna hira, wayansa ne yayi k'ara alamar sak'o, bak'uwar number ya gani ya bud'e ya soma karantawa kamar haka _Kada ka tab'a tunanin dan an d'aura maka aure da Ummy hakan na nufin ka sameta, Ni Bilal indai ina raye baka isa ka mallaki Ummy ba saboda tawa ce! Kana wahalar da kanka a inda ba'a sonka ba'a muradinka. Kayi gaggawan rabuwa min da matata dan babu mahaluk'in daya isa ya rabani da ita sai Allah_ Wani guntun murmushi Jamal ya saki duk da cikin zuciyarsa yana fargaban abinda zaije yazo. Haka ya zauna sukuku kamar mara lafiya har yanma. Bayan kowa ya watse da daddare bayan isha'i ya shiga ya gaida Abba dasu Mami sannnan ya nufi side d'inshi, kamar jiya yauma d'akin Mabrookah ya soma shiga, zaune take kan gado cikin wasu arnayen kayan bacci, kallo d'aya ya mata ya kauda kai. Baisan meyasa ba Sam Mabrookah bata burgeshi, shishige mai ta soma ya mik'e a fusace yana hararanta ya bar dakin. Kamar zai shiga na Ummy sai kuma ya fasa ya shiga d'akinshi. Itako Ummy tana chan d'aki zaune shiru abin duniya ya isheta. Dakyar ta mik'e ta shiga toilet tayi wanka ta sauya zuwa na bacci ta kwanta. Washe gari monday da wuri yayi wanka ya fito cikin shirisa na fita aiki, d'akin Ummyn ya kalla sannan ya sauko k'asa Nan kan dinning d'in k'asa ya tarar da Mabrookah tana breakfast, a hankali ya k'arasa ya zauna. Ta kalleshi tareda tab'e baki tace "Ina kwana!" "Lapia" yace ta takaice yana bin abincin da takeci da kallo, ganin haka yasa tace "Mami ce ta aiko dashi, na zuba maka neh" Yad'anyi jim sannan yace "Ni ina azumi but ki zuba Ummy, koda yake kirata inasan magana daku" Fara'ar dake fuskanta ya kau ta had'e rai tana murgud'a baki "Haba Ya Jamal ni ne zan kirata" Wani mugun kallo ya bita dashi ta mik'e tana turo baki ta haura saman, kamar yanda ta saba shiga mata d'aki a wulak'ance haka yauma ta shiga, zaune ta sameta kan gado tayi tagumi "Keh ki fito mijina na kiranki" D'an d'agowa tayi tana kallanta, a

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82