Skip to content

Chapter 38

Chapter 38

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

tare furta mata "I love uh Wife!" Ya k'ara sakin murmushi ya mik'e ya fita cikeda farinciki. Binsa da kallo tayi wani abu na shiga zuciyarta wanda ta kasa gane menene shi. Ranar daga Ummy har Jamal bacci sukayi mai cike da nishad'i. K'arfe bakwai da kwata y sauko cikin shiri na fita office, Bak'in shirt ne a jikinsa da brown d'in wando, ya nad'e wuya da farin tie. Sai baza k'anshi yake. D'akin Ummyn ya lek'a ya sameta zaune kan mirrow taci kwalliya cikin atampha purple and black. Sosai tayi kyau duk da ba wani makeup tayi bah. Kici kicin d'aura sark'a take tayi ta kasa, ya k'arasa ya amsa a hankali ya soma saka mata. Ta Mirrown suka k'urama juna ido, ta d'anyi murmushi ganin kallon yayi yawa ta sadda kai k'asa. Bata ankara ba taji fuskarsa a wuyan nata yana sunsunata yana lumshe ido cikin salo, idanunta itama ta lumshe tana d'an murmushi "Kinyi kyau sosai Wife" Shiru tayi ba magana, ganin haka yasa ya juyo suna fuskanta juna, light kiss ya mata a lips d'inta tayi saurin mik'ewa a kunyace zata bar d'akin. Hannunta ya kamo ya janyota zuwa jikinshi "Ina zaki bayan bamu gama magana bah" Ta d'anyi murmushi tana k'okarin k'wacewa daga rik'on daya mata. Baki ta turo gaba a shagwab'e tace "Dan Allah ka sakeni kaga fa zakayi latti" Yakai fuskanshi wuyanta yana sunsunar k'anshinta cike da nishad'i "Ai na riga da nayi lattin, kuma duk laifinki neh" Ta d'ago tareda zaro ido tana kallansa "Ni ba ruwana kai neh" Ganin abin nasa naso ya wuce wuri yasa ta d'an turesa da k'arfi ta fito daga d'akin tana mai dariya. K'asa ta sauko sukayi kicibus da Mabrookah akan dinning tana breakfast. Bata kawo komai ba tace "Ina kwana" Dogon tsaki Mabrookan taja ta mik'e ta d'au handbag d'inta tabar falon cikeda bak'in ciki. Zama Ummyn tayi kan kujera tayi shiru. K'aran saukowan sa daga sama taji ta d'ago tana kallanshi, shi ko harara ya sakar mata yana d'an murmushi, kai ta duk'ar k'asa tana wasa da zoben hannunta. Jan kujeran dake kusada nata yayi ya zauna ya d'an b'ata rai yace "Serve me" Ba tareda b'ata lokaci ba ya mik'e ta had'a mai abincin ta tura masa gabansa, folk ya d'auka ya saka yace "Mu ci!" Yanda yayi maganan fuska a had'e yasa ta d'au folk d'in ta soma ci a hankali. Shiko zagewa yayi yaci yayi nak sannan ya mik'e yana cewa "D'auko gyalanki muje" Gabanta ne ya yanke ya fad'i, kardai ace sakinta yayi, maimaita wa yayi yana kallanta fuskansa ba yabo ba fasara. A sanyaye ta hau sama ta d'auko hijab tasa, hannunta ya rik'e suka fito daga side d'in, tsakar gidan take bi da kallo dan rabonta da fitowa yau kwana hud'u kenan. Side d'in Mami taga ya nufa har lokacin yana rik'e da hannunta, da sallama suka shiga falon, kan dinning suka hango Mami da Abba suna breakfast, kici kicin k'wace hannunta ta soma yi ta kasa, shiko k'ara damke hannun yayi tareda d'an juyo wa ya kalleta. Har dinning d'in suka k'arasa, a kunyace ta sulale k'asa ta gaida su, Abba ne ya amsa da fara'a itako Mami kicin kicin tayi da rai, Jamal yaja kujera ya zauna ya gaida su, nan Mami ta washe baki tana amsa gaisuwan nasa. Abba yace "Taso daga k'asan tiles d'in nan 'yata, hau kujera ki zauna" A kunyace kanta k'asa tace "Aa Abba nan ma yayi" Ba k'aramin burge shi Ummy tayi bah, ganin yanda take da kunya da sanin yakamata. Itako Mami mik'ewa tayi fuska ba walwala tayi musu sallama ta fita. Ido Abba ya bita dashi yana girgiza kai. Nasiha sosai ta musu akan zaman aure sannan shima ya mik'e ya fita. Jamal na ganin ya fita ya mik'e ya dawo kusada ita ya zauna yana k'okarin janyota jikinshi, matsawa tayi tana turo baki "Ni dai ka tashi ka tafi" Ta nuna masa agogo tace "K'arfe fa takwas da rabi" "Na fasa zuwa yau" Ido ta zaro tana kallansa da mamaki "Meyasa" "Saboda ina tare dake" Ta d'anyi murmushi tace "Aa nidai ka tafi dan Allah nasan mutane na nan suna jiranka" Matsowa yayi kusada ita sosai yana murmushi "Kinaso naje" Ta gyad'a masa kai, yace "Idan dai kinaso naje to sai kin min Kiss" Mik'ewa tayi dasauri tabar falon a guje tana masa dariya. Shima dariyan yad'anyi ya girgiza kansa ya hau motarsa ya fice. Hau jinsa yake cikin farinciki mara misaltuwa, koda yaje office kyaytar dubu dubu ya dunga ma ma'aikatan dake k'arkashinsa. Itama Ummy kasa b'oye farincikinta tayi, albarka ta dunga sama Laurat a zuciyarta, lallai Laurat k'awa ce ta gari. Saidai matsalar ta d'aya son da Mami da Mabrookah basa mata, duk sanda ta tuna sai gabanta ya fad'i. Wuraren k'arfe sha d'aya na rana akayi knocking k'ofar side d'in, k'asan ta sauko ta bud'e a d'an tsorace. Wani mutumi ta gani tsaye, gaida shi tayi ya amsa tareda gabatar mata da kansa a matsayin malamin lesson da zai rink'a koyar da ita karatun boko dana addini. Da farinciki ta haura sama zuwa d'akinta, wayanta ne taji tana ruri ta d'auka da sauri ta kara a kunnen ta "Hello wife" Lumshe idanunta tayi ta bud'e, tad'anyi murmushi mai sauti yace "Ba magana? Any way idan nadawo yau zansaki magana" Ya d'anyi dariya tareda sassauta murya yace "Maganganu mah" Baki ta turo gaba, ya sake cewa "Kinga bak'on dana turo" Tace "Eh" a hankali. Jim yayi yace "Kisa Hijab pls, sannan ba Hira and banasan kina dariyan nan naki mai tsada a gabansa" Ta saki murmushi tareda k'ara rik'e wayan sosai a hannunta. A shagawab'e yace "Kinji!" Yanda yayi maganan sosai ya bata dariya, daga cikin wayan ya dunga jiyo dariyar ta a hankali. Lumshe ido yayi ya bud'e yana shafa cikinsa yana turo baki "Ina jin yunwa sosai Wife, dazu baki bani abinci bah" "Lah! Ba gaskiya baneh, ba kaci bah" "Nidai pls ki dafamin wani abu mai dad'i kafin na dawo kinji" "Ummm..." Tace a hankali ya sake cewa "I love uh so much, zamuyi magana ltr" Ya kashe kiran yana bin wayan da kallo yana murmushi. Itama wayan tabi da kallo da murmushi, ta rasa meke damunta daga jiya zuwa yau. Tunani ta soma, chan ta mik'e dasauri tunawa da tayi tabar lesson teacher a waje. Jotern bikinta ta d'auka da biro bayan ta binjima k'atan Hijab ta fito. Nan varendern side d'in nasu ta samesa zaune kan farin kujera. Zama tayi bayan ta sake gaisheta sannan ya soma mata 'yan tambayoyi na boko dana addini. Sam baiyi tunanin tasan abubuwa sosai na boko bah, na addini kuwa ba k'aramin yaba mata yayi bah. Nan suka soma karatu har zuwa k'arfe d'aya. Bayan la'asar kicin d'inta dake nan saman ta shiga shiru ta tsaya tana bin kicin d'in da kallo dan ya burgeta sosai. Fridge ta bud'e taga shima shak'e yake da nama kala kala da kuma kayan miya. Cikin sa'a d'aya ta had'a had'adiyar miyar kub'ewa d'anya dayaji nama. Sannan ta mulka tuwon semonvita ta kukulla a leda tasa a kula. Harta fito ta tuna Abba nasan tuwo, ta koma ta bud'e sabon kula ta zuba masa da miya a saka

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82