Skip to content

Chapter 82

Chapter 82

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 645 words 0 views Progress saved
Download Book

Ram shima ya samu wani contract da wani Company inda ya kasance Lawyern Companyn duk dai a nan Abujan. Ranar wata talata Ummy ta tashi da ciwon nak'uda, cikin ikon Allah ana isa asibiti ta sub'uto santalelen d'a namiji mai kamada Jamal sak. Murna wajan Jamal ba'a magana, su Abba sunyi Farinciki sosai Bakuna yak'i rufuwa. Ranar suna Yaro yaci sunan Abba Mijin Mami wato *Suraj* anma ana kiransa da *Alwaz* anyi bidiri sosai ranar suna harda su Laurat duk sun zo a nan Ram ya ganta ba wani b'ata lokaci ya nuna mata buk'atarsa bata tsaya wani jan aji ba ta amince masa. ```Bayan shekara D'aya abubuwan cigaba da alheri dayawa sun faru, Alwaz yayi wayo sosai har ya soma tafiya, Ummy tana shekarantanta na farko a Turkish Nile University, Ta k'ara murjewa tayi kyau kamar ba itaba. Kallo d'aya zaka mata ka gane tanada shigan ciki saboda yanda tayi fari da ta cicciko. A cikin watan Jamal ya samu aiki a k'asar Germany tare da sabon Companyn Versace. Murna wajan Ummy ba'a magana su Abba sunyi farinciki tare da sa Albarka.``` A cikin watan akasa Ranar Mifzal da Areefah wata Uku, Lokacin saura Wata biyu bikin Ramadhan da Laurat wanda za'ayi a tudun wadan kaduna. Tun a makaranta take ta jin kamar zazzab'i zai rufeta, dakyar ta iya attending lectures d'in ranar, tana fitowa ta kira Jamal a waya, ba'adau lokaci bah ya iso makarantar duk hankalinsa a tashe, hand bag d'inta ya amsa tare da rik'o hannunta ya sakata a motan yanata mata sannu. Sun d'au hanya suka hango chinchirindon jama'a a tsakiyar titi, parking yayi ya fito wani mutumi ya gani yana baro wajan, ya masa sallama tare da tambayansa abinda ke faruwa, mutumin yace "Wata 'yar shaye shaye ce ta shigo hanya mota ta bigeta wallahi, tama mutu. Kai irin wannan rayuwa ta 'yayan yanzu Allah ya sawake" Jamal ya masa godiya harya bud'e kofan mota ya hango ambulance d'in road safety sun k'araso wajan, nan aka mutane suka mamatsa aka basu waje, kamar a mafarki ya Hango Mabrookah kwance a wajan, sake mutsutsuke idanunsa yayi dan ya tabbatar da abinda ya gani, bai san sanda ya saki k'ofan motan ya k'arasa wajan bah, har an d'auketa an sakata a mota. Sai bin motan yake da kallo gabansa na fad'uwa. Yana nan tsaye aka wuce da gawanta, hawaye suka gangaro masa yayi maza yasa hannu ya share. Koda ya shiga motan bai fad'ama Ummyn wacece bah, yadai ce wata aka bige. Da damuwa suka isa gida har lokacin yana tausayawa Mabrookahn da tunanin Makomanta. Bayan wata d'aya Jamal yayi reporting a wajan aikinsa achan Germany, ba b'ata lokaci ya soma aiki dasu kuma yana jin dad'in aikin saidai abu d'aya dake damunsa rashin iyalinsa kusa dashi. Haka itama Ummy tun bayan tafiyarsa ta dawo gidan Ammi da zama saboda kewar mijinta, tare suke zuwa makaranta da Areefah, Alwaz shekaransa d'aya da wata d'aya yayi wayo sosai kamar d'an shekara d'aya da rabi. Lokaci guda yak'i nono ya yaye kansa, gashi bashi da k'iuya hakan yasa ya koma Wajan Ammi tana kula da jikan nata. _A nan sai ince Allah ya k'arama wannan Family zaman lafiya da san juna Ameen_ *ALHAMDULILLAH* A nan na kawo k'arshen Littafina mai suna _JAMALUDEEN_ Kurakuren danayi Allah ya yafeni, abinda na fad'a daidai Allah ya bamu ladan gaba d'aya. Darusan dake ciki Allah ya bamu ikon d'auka Ameen. ```Na yanke labarin neh saboda Zuwan watan Ramadhan, dan banaso mukai har bayan sallah bamu gama bah. Ina fatan zakumin Afuwa``` Ina godiya ga Masoyana gaba d'aya, Allah ya barmu tare. Ina sanku kamar yanda kuke sona. Sai kunjini a cigaban littafina mai suna *GA ZARAH GA WATA* bayan sallah insha Allah. Inayi ma kowa fatan alheri, Allah yasa muyi azumi Lafiya ya kuma bamu lada da falallan dake cikinta Ameen. RAMADHAN KAREEM In Advance Ummy Abduol✍🏻

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82