Chapter 29
Chapter 29
zan iyayin komai a kanta matuk'ar ana neman a rabani da ita" Jamal yayi murmushin takaici yace "Kana santa ka bari har na aureta? Hakan ya nuna kai raggo ne akan soyaiya, bazaka iyayin komai dan ka mallaki abinda kakeso bah duk cika baki neh" "Haka kace!" Cewar Bilal a harzuk'e ransa b'ace Jamal ya sake sakin murmushi yace "Haka nace" Fuuuuuu Bilal yabar zauren. Sosai ran Jamal ya b'aci ya figi mota yabar anguwan cikeda takaici. ****** A b'angaren su Mami kuwa zagewa sukayi itada Aunty Faty sunata gyara 'yar tasu dan saura sati biyu biki, su Mabrookah kuwa sai b'arin d'uwawu take ita a dole amarya. Ana cikin haka Laurat ta dawo bakin aikinta, a bakin masu aikin kicin take jin labarin abinda ya faru, kuka sosai tayi gashi batasan gidansu Ummyn bah balle taje wajanta. Su Twins ta samu suka mata kwatance, washe gari kuwa ta saci hanya ta tafi. Ummy na zaune a tsakar gidansu tayi tagumi kamar a mafarki taji muryan sahibar tata. Mik'ewa tayi suka rungume juna a tare kuma suka fashe da kuka, saida sukayi mai isarsu sannan Ummy taja hannunta suka shiga Falo. Mama suka samu a falon, Laurat ta gaisheta tareda mata gaisuwa, Ummy ta gabatar da Laurat a wajan Mama sannan suka shiga d'akin Ummyn. Bayan Laurat taci tasha Ummy bata b'oye mata duk abinda ke faruwa bah, sosai Laurat ta tausaya mata, Ummy tace "Gaskiya Laurat ina cikin tashin hankali, Wallahi bana san aurena da Ya Jamal, Ya Bilal nakeso" Laurat ta gyara zama tace "Duk da ban tab'a ganin Bilal d'in nan bah, kuma bansan halaiyarsa bah. Nidai haka nan hankalina yafi kwanciya da Jamal" Ta dafa kafad'ar Ummyn tace "Wallahi kun dace keda Jamal sosai" Ummy tai saurin buge hannun Laurat d'in tace "Wannan irin magana kikeyi Laurat, kema kina sahun masu san rabani da Ya Bilal kenan" "Ba nufina kenan ba Ummy, abinda nakeso ki gane a nan shine. Babu abinda yazo zaki iyayi dangane ga maganar nan, karki manta. Yanzu haka kina a matsayin matar Jamal ne, tunda har an d'aura aure ba kuma abinda ya rage daya wuce kiyi hak'uri kima mijinki biyaiya" Shiru Ummy tayi ta sake rushewa da kuka. Lallashinta Laurat ta soma dakyar ta samu tayi shiru sannan ta mata sallama itada Mama tabar gidan. Tun daga ranan Innan Bilal ta soma gyaran 'yar nata kamar ba gobe, dan ita sam bata nuna kishi akan auran. Bilal ko abin duniya ne ya ishesa yau ciwo gobe Lafiya, haka Itama Ummyn. Ango Jamal kuwa tunda Haka ta faru tsakanin su da Bilal bai sake zuwa gidan ba duk da yanda zuciyarsa kesan ganin Gimbiyar tasa. Abba ne da Mami sai Mabrookah dake gefe da kuma Jamal harda Aunty Faty dasu twins. Gyaran murya Abba yayi sannan yace "Kamar yanda kuka sani, yau saura sati d'aya d'aurin auren Jamal da Mabrookah, saidai akwai abinda baku sani ba wanda yau nakeso na warware muku" Mami tace "Menene kuma Alhaji" Ya d'anyi murmushi yace "Sati uku da suka wuce aka d'aura auren Jamal da Ummy" Mami ta mik'e dasauri "Ummy fah kace Alhaji" "Kwarai da gaske ita" "Haba Alhaji, ya zakayi mana haka yanzu ita Mabrookahn fah" Nan da nan Mabrookah ta fashe da kuka, Jamal ko sai hararanta yake, ji yake kamar ya shak'eta ta mutu kowa ya huta. "Bance miki ai baza'a d'aura da Mabrookah bah. Itama idan Allah ya kaimu sati mai zuwa za'a daura nata. Sannan inaso ku sani banasan tashin hankali ko k'ananan maganganu" Mami ta zauna a sanyaye tana kallan Aunty Faty wacce keta hararan Mamin, ba'a gama magana ba Aunty Faty ta mik'e tabar falon tana huci. Abba ya cigaba da cewa "Kamar yanda kika zab'ar mai Mabrookah, haka nima na zab'a masa Ummy saboda na lura yarinya ce marainiya" Twins sai dariya suke k'asa k'asa cikeda farinciki. "Gobe a tara 'yan uwa da abokan arziki dan akai lefe gidansu Ummyn, kuma inaso ya zama rana d'aya za'ayi bikin dana Mabrookah" Mami dai ba amsa sai huci datake yi cikeda bak'in ciki, sallaman su Jamal d'in yayi, Mabrookah ta mik'e tana kuka mai had'e da ihu ta haura sama, Twins ma suka mik'e suka bi bayan Jamal sunata mai Congrat. "Fisabillahi yanzu Alhaji abinda kayi ya dace" "Ni ko nasan ya dace" "Gaskiya Alhaji bazai yuwu bah, a rasa wacce za'a daura ma Jamal sai b'arauniya" "Ya Isa Maimuna! Ki shiga taitayinki, ya ina magana kina magana. Tho bari kiji, ba gudu baja da baya aure dai an d'aura, kuma kamar yanda na fad'a miki gobe za'a kai lefe gidan su Ummy, sannan set biyu za'a kai mana. Idan kuma kika sake naji wani magana ya taso zamu sabu sab'ani dake sosai" Ya mik'e fuuuu yabar falon ranshi b'ace. Haurawa Mami tayi zuwa d'akin Jamal, batareda wani b'ata lokaci ba ta d'auke shi da mari "Ni! Ni Jamal kakeso ka wulak'anta?" Ta rushe da kuka "Ba laifinka baneh" Ta bar d'akin dasauri, kuka shima Jamal d'in ya fashe dashi, shi yanzu ina zaisa ranshi, ga Ummy bata sanshi, Ga Mami na fushi dashi, ga kuma auren Mabrookah da aka tilasta masa akai. Ranar Aunty Faty da Mami kacha kacha sukayi, washe gari kamar yanda Abba ya umarta, set biyu na akwati aka d'auka aka barma Mabrookah d'aya, gidan su Ummyn aka kai, Mama tace akai gidansu Innan Bilal, nan Inna tayi kiran Mak'ota aka amsa kayan cikeda farinciki. Tunda Ummy taji shigowan masu kawo lefen ta fashe da kuka, shikenan tasan aikin gama ya gama an rabata da Ya Bilal d'inta. A ranar Ramadhan ya diro Zaria, shi kad'ai yazo gidansu Ummyn ya kawo mata kud'in d'inki, dubu hamsin wanda Abba ya bada a kawo. Saida ya dinga had'ata da Allah sannan ta amsa tareda waya k'irar Samsung da Jamal d'in ya bada a kawo mata. Duk abinda sukeyi Bilal na hango su wanda yake bak'in k'ofar gida, ranshi ya b'aci sosai. Ramadhan d'in na tafiya ta juyo tayi hanyar gida, had'a ido tayi dashi gabanta ya fad'i, baice mata komai ba yayi shige wanshi gida. A sanyaye ta nufi gida, Mama ta nuna ma kud'in da wayan, tasa albarka sannan tace takaima Inna dan itace mai shirye shiryen. Bata samu ta kaiba sai washe gari, Nan take Inna ta d'au kaya kala goma ta saka a leda ita da kanta takai Ummyn wajan masu d'inki dan tasan idan tace ita kad'ai taje bazata bah. Tun daga ranar Ummy bata sake ganin Bilal bah, ko ta shiga gidan bata ganinsa. Bahar ta tambaya a nan yake fad'a mata ya tafi abuja wajan Alhajin daya zauna wajansa. Wani k'walla ne ya gangaro mata tasa bayan hannu ta share. Yau saura kwana hud'u biki, Laurat dakyar ta samu Mami ta barta ta tafi hutu kan cewa marik'iyrata batada lafiya. Tana tafiya tayo gidansu Ummy dan tayata shirye shirye. Sosai Ummy tayi Farinciki da zuwanta. Wayan da Ramadhan ya kawo mata ta nuna mata, Laurat ta kyalkyale da dariya tana cewa "Hala ma ko kunnata baki iya bah" Harara Ummy ta wurga mata "Ni ina ruwana ma da wayar" Dariya Laurat tayi ta kunna mata wayan, text ne ya shigo ta bud'e tana cewa "Ashe ma akwai Sim a ciki, har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82