Skip to content

Chapter 60

Chapter 60

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

yanda nakeyi dah_ *Kusha Kurumin ku masu tambayan Labarin Jamaludeen, Insha Allahu yazo k'arshe nan da kwana kad'an zan gama* Page 72 n 73 Already dama ya sayi Ghana must go a hanya, zama yayi dirshan ya soma k'irga kud'in yana sakawa cikin Ghana must gon batare da wani tunanin bah, dan gaba d'aya hankalinsa nakan Wife d'insa. *A gurguje* Ram ya kali Mifzal fuskanshi ba walwala "Naji High court wajan lawyern dayazo da Wannan Alhaji Tijjanin, abin was terrible" Mifzal ya gyara zama yace "Kamar yah?" Ram ya sauke ajiyar zuciya yace "Anyi hayansa ne kawai yaje ya bada shaida akan bashin da akace Alhaji Tijjani na binsa" Sosai Mifzal yayi mamaki, yace "To yanzu menene abin yi?" Ram ya gyara zama ya matso kusada Mifzal yace "Kama Barr nan zakuyi ku tuhumesa, or a turashi state CID for investigation" Sosai Mifzal yaji dad'in shawaran Ram, ya mik'e yana cewa "Muje tare dan akwai tambayoyin da nakeso Alhaji Ameenu ya amsa min kuma inaso ya kasance a gabanka" A tare suka mik'e suka fito, already dama Mifzal yasa record a wayansa, inda Alhaji Ameenu yake suna nufa, Mifzal ya zauna kan kujera Ram kuma na tsaye gefensa "To Alhaji tunda ga lawyern ka a kusa dakai yanzu ina iya maka tambayoyi koh" Harara Alhaji Ameenu ya wurga masa, Mifzal yayi murmushi sannan yace "Inaso nasan ko kai wanene" Saida Alhaji Ameenu ya kalli Lawyernsa ya gyad'a masa kai sannan yace "Sunana Ameenu Jibril, ni d'an Kano neh, inada mata d'aya da kuma 'ya'ya biyu namiji da mace. Mafi yawan zama na a Egypt nake yinsa tare da iyalina" Mifzal ya jinjina kai sannan yace "Ko zan iya sanin sana'arka?" Barr. Ishaq ya karb'e da cewa "D'an kasuwa neh ku..." Saurin d'aya masa hannu Mifzal yayi ransa b'ace "Ina magana neh da Alhaji Ameenu Jibril bakai bah" Gum Barr. Ishaq yayi sai hararan Mifzal d'in yake a fakaice. Alhaji Ameenu yace "Kamar yanda lawyer na ya fad'a ni bussiness man neh, a da ne nayi siyasa" "Menene Alak'ar ka da Alhaji Surajo" "Mene kuwa tsakanin mu? Ni ko sunansa ban tab'a ji ba balle nasan shi" Sosai yanda Alhaji Ameenu ya daburce yaba Mifzal dariya "Come down Alhaji" Gaba d'aya Alhaji ya tsure sai muzurai yake yana zufa, Mifzal yace "An kashe Alhaji Surajo Ranar Ashirin ga watan January da daddare an shiga gidan Alhaji Surajo an kashe shi, ko zaka iya fad'amin ranar kana ina" Alhaji Ameenu ya k'ara tsurewa, muryansa na rawa yace "I...inna k..kuwa? Ina gidana dake Abuja mana" Barr. Ishaq yayi saurin cewa "Why all this questions? Ni Lawyern Alhaji Surajo kadiri neh, haka zalika ni Lawyern Alhaji Ameenu neh. Kuma inada tabbacin babu wanda yasan wani tsakanin su" Ran Mifzal in yayi dubu ya b'aci musamman yanda Barr. Ishaq ke d'aga murya yana magana a fad'ace. Yace "Kullum da daddare wuraren k'arfe tara zuwa goma kana fita daga gida ina kake zuwa?" Alhaji Ameenu ya juya ya kalli Barr sannan ya juyo ga Mifzal "Bana zuwa ko ina sai wajan kasuwanci nah" "Detective wannan tambayoyin ya isa haka, ba hannun Alhaji Ameenu a duk wad'an nan abubuwan. Kuyi gaggawan sakinsa ko na maka ku a kotu" Wani dariya Mifzal ya saki "Dako naji dad'i idan ka kaini kotu" A fusace ya mik'e yama Ram nuni ya biyosa, ba musu suka fita daga seil d'in. Barr ya kalli Alhaji Ameenu yace "Alhaji ka kwantar da hankalin ka komai zaizo k'arshe yau d'in nan" Mifzal na fita yasa wasu 'yan sanda su fito masa da Barr Ishaq, cikin sauri suka fito dashi aka kaishi Secret room sai fizge fizge yake yana fad'a. State CID aka kira sukazo suka tafi dashi dan a tuhumesa. Mifzal yace "Jamal na cikin wani hali na rashin Ummy, idan ka ganshi sai ya matuk'ar baka tausayi" Jikin Ram yayi sanyi yace "Kafin mu samu wani information akan Barr Ishaq mu duba Jamal d'in mu dawo. sai shima mu tambaya ko sun k'ara kira" Ba musu Mifzal ya zari key suka bar office d'in. A b'angaren Jamal kuwa, Cikin Awa d'aya zuwa da rabi ya gama had'a kud'in tsaf ya saka a ghana must go kamar yanda suka buk'ata. Zama yayi yana jiran kiransu dan su fad'a masa inda zai aje kud'in. Ba dad'ewa wayansa ya soma ringing, numbern Ummyn neh yayi appearing ya d'auka dasauri jikinsa na rawa ya kara a kunnensa "Hello Wife!" Muryan namijin nan neh ya sake ji, gabansa ya fad'i ya yayi saurin cewa "Ina matata? Ina take? Ga kud'in ku na had'a muku ina zan sameku" Daga chan b'angaren yace "Good Boy! Lallai kana san matar nan taka." "Dan Allah ka bani naji muryanta, dan Allah" Ba musu ya kara ma Ummyn a kunne, tana kuka tace "Ya Jamal ina kake? Dan Allah kazo ka tafi dani, ban..." Akayi saurin fizge wayan, hawaye ne suka soma zarya a fuskansa yace "Pls karku tab'ata, ku fad'amin inda zan aje muku kud'in na d'auki matata" Cikin wani irin dariya Mutumin yace "Ka aje kud'in a wajan bishiyoyin Bomo Village, daka iso wajan zamu ganka by 11:00am dot, kana wucewa zamu kasheta" Wani k'ara ya saki, kamin yayi magana aka kashe wayan, agogo ya duba yaga 10:15am. Ya fashe da kuka ya d'au ghana must go d'in dakyar ya fita, bai ko kalli Mabrookah dake masa magana tana k'okarin k'arasowa inda yake. Yayi saurin shiga motan ya tada ya bar gidan a guje. Fitanshi Express yayi daidai da k'arasowan su Mifzal bakin Layin, sam Jamal bai lura dasu bah ya k'arama motar wuta yayi gaba, da Mamaki Mifzal yabi motar da kallo "Kaga Jamal chan ina kuma zashi" Ram yace "Ji yanda yake driving da gudu, anya kamar ba lafiya bah mu bisa" Ba musu ya juya kan motan suka soma binsa da gudu suma. Hold up ya samu wajan ABU ya daki stiering motan wasu hawaye suka sake gangaro masa, agogo ya duba 10:40am, ya rushe da kuka yanata danna horn. Yakai Minti Biyar a wajan ya samu ya wuce ya cigaba da gudu su Mifzal na binshi, Bomo Village sukaga ya shiga suka suka sa kan motarsu ciki. Daga mirrown gaban motan ya Hango motar Mifzal d'in, ya sake dukan Stiering yayi saurin Parking ya fito yana kuka. Suma suna ganin Haka sukayi parking, ya k'araso inda suke tsaye "Dan Allah ku koma, ku kyalleni Pls karsu kashe min matana. Amsota zanje yi, dan Allahu ku koma" Gaba d'aya ya basu tausayi, Ram yace "Ka samu kud'in neh?" Ya duba Agogon Hannunsa 10:50am, wasu Hawaye suka sake zubo masa, cikin fad'a yace "Ku rabu dani! Ku tafi ku kyalleni" Ya sassauta murya cikin kuka yace "Zasu kashemin matata idan har bankai bah har 11:00am bah" Ha had'e hannayensa alamar bada hak'uri "Dan Allah ku koma, kuyi hak'uri" Hawaye Ram ya share na tausayin abokin nasa, ya duba agogon Hannusa 10:54am, Mifzal yace "Yi sauri tho" cewar Mifzal. Da gudu ya shiga mota ya figa a guje yabar wajan. Da wani matsiyacin gudu ya k'arasa inda sukace masa, Parking yayi ya bud'e booth ya ciro kud'in, a hankali yake tafiya har ya k'arasa wajan da akace ya ajiye. Gabas da yanma, kudu da arewa ya duba baiga kowa ba

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82