Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

now on ke friend d'ita ce and my Maid, uh must obey my rules" Kallashi kawai Ummyn keyi dan ba abinda ta fahimta a maganarsa Kwalla ta matse ta kauda kai gefe murya k'asa k'asa tace "Kai kasan abinda kace, Mugu kawai" Yayi murmushi tareda mik'ewa "Mugaye dai, wayasan me kikaita min sanda banda lapia" Batace mai komai ba ta zunguro baki ta koma ta kwanta. Mabrookah na shigowa falon taji kamar maganan Jamal a d'akin, ji tayi anyi shiru ta girgiza kai, har ta gota d'akin zata wuce ta k'ara jin magananshi. Ba shiri ta tura k'ofar d'akin ta shiga, tsaye ta sameshi ya bada baya yana rik'e k'ugu sai kallan Ummy yake "Ya Jamal" Ya juyo suka had'a ido, ta k'araso kusada shi da mamaki "Meh kakeyi a nan?" "Meyasa bakiyi sallama ba da zaki shigo" Ta b'ata rai "So nawa zance kiyi sallama Mabrookah" Ta tsuke fuska ta juya fuu tabar d'akin tana danasanin shiganta gashi ya dizgata a gaban yarinyan daya tsana. Kallan Ummy yayi yaga ta rufe ido yayi murmushi, kwana biyu kenan da samun lafiyarsa har ya lura da rashin jituwar dake tsakanin Ummy da Mabrookah. D'akin ya bari ya haura sama dan cima Mabrookahn mutunci dan ya tsani yana ma mutum magana ya wuce ***** Sati biyu kenan da samun lafiyar Jamal, Alhamdulillah jikin Ummy yayi sauk'i sosai har an kwance d'aurin saidai ance ta daina yawan anfani dashi sosai kuma kada ta d'au abu mai nauyi. A sati biyun nan har saida zaman gidan ya gundureta saboda Jamal, kullum yana d'akin yayita sata surutu kuma bazai bar d'akin ba sai yaga tayi kuka sannan hankalinshi zai kwanta. Yau Sati kamar yanda ta saba shiri take da zuwa gida sai zumud'i take dan kimanin sati uku kenan bata je gida bah duk hankalinta nakan Iyayen nata. Kayanta set hud'u ta zuba a leda dan wannan karan kwana uku Mami ta bata. Cikeda farinciki da zumud'i take komai, Turo k'ofar d'akin da k'arfi, ko ba'a fad'a mata bah tasan Mabrookah ce dan ita kad'ai ke shigo mata d'akin haka. D'agowa tayi dasauri suka had'a ido "Zuwa nayi naja kunnenki, ki daina shiga harkan Ya Jamal, ki fita daga harkansa, kada na sake ganin ki kusa dashi. Kina jina" "Insha Allahu bazan k'ara bah" Dogon tsaki taja "Ku dama Talakawa haka kuke, shegen kwad'ayi a tara a kaima iyaye" Ummy ta d'ago ta kalleta dasauri, hawaye ya gangaro mata ta share. Wani tsakin ta sake ja tabar d'akin tareda bugo k'ofan. Rushewa da kuka Ummyn tayi, bah abinda ta tsana a rayuwanta kamar a zagan mata iyaye. Saida tayi mai isarta sannan ta tashi ta d'au ledan kayanta tasa hijab ta fito, Mami ta samu a falo ta mata sallama tasa driver ya kaita tayi godiya ta fito. A haraban gidan ta had'u da Jamal ya dawo sallan azahar, kallo d'aya ta masa ta kauda kai tana k'okarin shiga motan. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:29 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 22 A haraban gidan ta had'u da Jamal ya dawo sallan azahar, kallo d'aya ta masa ta kauda kai tana k'okarin shiga motan. Binta da ido yayi harta shiga cikin motan, tsayuwa yayi jim sannan ya k'araso ya amsa keyn motan a hannun drivern ya shiga, hankalinta sam bai kai wajansa ba dan duk a tunaninta drivern neh. Window taketa kallo kwalla na fita daga idonta, abubuwan da Mabrookah ke mata ya soma damunta, musamman yanzu data kirata da talaka kuma kwad'ayaiya. Hawayen idanunta ta share a hankali tace "Indai Jamal ne daga yau bazan k'ara masa magana bah" Taja dogon tsaki "Kema sai ki ja mai kunne ya daina shiga harkana" Burki taji anja da k'arfi ta juyo, ganin Jamal yasa ta bud'e baki zatayi ihu dan duk a tunainta Garba driver ne ke tuk'in. Ganin tana kokarin yi masa ihu yasa galla mata harara, k'ofan motan ta murd'a ta fita dasauri. "Ummy ina zaki" Batace mai komai ba tacigaba da tafiya, hakan yasa dole ya fito ya soma binta, tafiya ta cigaba dayi sauri sauri "Wai meye haka Ummy, tsaya mana" Dakyar ya sha gabanta, ta kauda kai gefe "Dan Allah Ya Jamal ka daina bina, ka koma gida" Had'e rai yayi dole ta natsu tana kallanshi, ledan kayanta ya amsa a hankali yana kallan fuskanta "Muje mota and banasan musu" Ba yanda zatayi hakanan ta soma binshi a baya har motan, gidan baya ya bud'e mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga. Kallanta yayi nad'an mintina fuskarsa d'auke da damuwa "Ummy fad'amin damuwarki, me aka miki" Batace komai saima kauda kai datayi gefe tana kallan Window "Fad'amin mana" Hawaye suka gangaro mata ta soma sheshek'a, lumshe ido yayi yana jin kukanta har ransa "Na lura kuka na miki dad'i" Hannu tasa ta share hawayenta ta d'ago tana kallan fuskansa "Wani alfarma nake nema dan Allah" "Ok ina jinki" "Inaso dan Allah daga yau ka daina zuwa inda nake, idan mun gaisa shi knan" Da mamaki yace "Saboda meh?" "Babu komai, dan Allah" Saida ya sauke ajiyar zuciya yace "Wa yasaki ki daina min magana" Ta d'an dago ta kalleshi da mamaki, gira ya d'aga mata "Tell me, ina jinki" Kuka takesan yi ta b'ata fuska hawaye cike da idonta "Dan Allah kai kaini gida, ko ka baro na hau adaidaita na tafi" "Zakije gida but sai kinmin alkawarin zako gad'amin" "Bazan iya fad'ama ba kayi hak'uri" Baice komai bah ya bud'e kofan ya fito "Ki dawo gaba" yace a takaice fuskarsa ba walwala Ba musu ta dawo gaba ta zauna, jan motan ya soma, tafiya kawai yake batareda yasan inda zai nufa bah, ganin suna shirin barin hanyan unguwansu yasa ta kauda kai gefe ta soma mai kwatance, murmushi yayi ya soma bin inda take kwatanta mai har suka kawo k'ofar gidan. Batace mai komai ba tad'au ledan kayanta zata fita, lock ya danna ta soma k'okarin bud'e kofan ta kasa "Ummy!" Ya kira sunnanta a hankali, bata juyo ba tace "Dan Allah ka bud'emin k'ofa na fita" "Banida aboki daya wuce Ramadhan, sai kuma keh" Ta juyo da mamaki tana kallansa, ya gyad'a mata kai "Kinada babban matsayi a gareni, dan ban d'aukeki a matsayin ma'aikaciya ba, kinada matsayi kamar yanda Mabrookah ke dashi" Shiru tayi bata daina kallonsa ba "Nasan zakice ina shiga rayuwarki" Yayi murmushi tareda danna lock d'in, tayi saurin murd'a kofan ta fita, ko waiwayowa batayi ba tayi shigewanta gida. Gabanta ne keta fad'uwa, saida ta tsaya bakin zaure ta daidaita kanta sannan ta shiga gidan da sallama, Mama ce ta fito dasauri jin muryan 'yar nata, rungume juna sukayi Ummy ta fashe da kuka "Ummy ina kika shiga tsawan sati uku bamu ganki bah" Ta sake rushewa da kuka, dakyar Mama ta samu ta lallasheta suka shiga wajan Baba, saida ta huta sannan take sanar dasu abinda ya faru. Sunyi Alhini sosai tareda farincikin samun Lapian Jamal d'in. Kwananta Biyu a gida ranar da daddare tana zaune a tsohon d'akinta tana cin abinci yaro ya shigo gidan da sallama, Mama dake tsakar gida ta amsa yace ana sallama da Ummy inji Jamaludeen. Gaban Ummy ne ya fad'i, Mama tace kace tana zuwa,

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82