Skip to content

Chapter 53

Chapter 53

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

ne ya katse ta ya shigo ya nemi guri k'asa ya zauna tareda gaida Maman. Da fara'a ta amsa masa tana tambayansa mutan gidan, ya amsa da lafiya. "Ke Ummy har yau bazaki girma bako" Turo baki tayi tace "Dan Allah Mama kice ya barni a nan mu zauna tare" Buge mata baki Mama tayi ta b'ata fuska "Hankali k'aranci Ummy, ke wa kika tab'a ganin ya dawo gida da aurensa indai ba mutuwa auren yayi bah" Jamal yayi murmushi "Mama barinyi sallah" Godiya ta masa ya mik'e yad'an saci kallan Ummyn sannan ya fita. Mama ta mik'e "Matsamin ki gani karki k'arasani." Ta shiga kitchen ta zubo mata fatan wake daya sha alaiyahu da kifi. "Yau abinda na fada kenan" Ummy tayi saurin rufe hanci tana b'ata fuska "Dan Allah Mama ki d'auke banasan k'anshin" Baki bud'e Mama ke kallanta, kantace komai ta fita daga d'akin dasauri ta durk'ushe ta soma amai jinkinta na rawa. Mama na tsaye bakin k'ofa tana kallanta tana 'yar murmushi. Tad'au buta takai mata "Gashi ki d'auraye bakinki" Ta amsa butan ta d'aura ye bakin, harta d'au tsintsiya zata share wajan Mama ta amsa "Aa bashi jeki huta abinki" Ba musu ta aje ta shiga d'aki tana cigaba da b'ata fuska. Wanke wajan tsaf Mama tayi sannan ta koma falon ta tarar da ita kwance kan 3seater idanunta a lumshe. Binta da kallo tayi daga sama har k'asa, tad'anyi murmushi batace komai bah. Sun d'an tab'a hira a nan take jin Inna zasu tashi daga gidan zasu koma abuja, sosai tayi mamaki saidai bata nunama Maman bah. Suna cikin hira Jamal ya kirata a waya, turo baki tayi sannan ta d'auka yace ta fito su tafi. Ba hakan taso bah, ta k'ara lafewa a kujera saida Mama ta mata fad'a sannan ta mik'e ta mata sallama tana turo baki. Haka Ummy ta cigaba da laulayi har na tsawon sati biyu sannan tad'anji dama dama. Ganin ta samu sauk'i yasa Jamal ya kira Ram akan maganarsu. Ranar Juma'a da safe yabar zaria zuwa kaduna cike da kewan Wife d'insa, wacce ya bari gida tana kukan rabuwa dashi. Saida ya tsaya yayi sallahn Juma'a a Sheikh Ja'afar dake unguwan dosa sannan ya k'arasa gidansu Ram d'in. A ranar suka d'au Hanyan Abuja. Bayan sun sauka a hotel Jamal ya kira wife d'insa, shagwab'a take ta masa ya dunga biye mata harda d'an kukanta na rashin son tafiyarsa. Hira sukayi sosai sannan ya kashe kiran. Ram dake gefensa yace "Yau dare yayi saidai mu bari gobe sai muje office d'insa" Kai Jamal ya gyad'a, Ram ya mik'e yana cewa "Ni fah kasanni banasan zaman waje d'aya, bani key dallah nad'an zaga gari" Jamal ya hararesa "Muje dai tare" Wayan Jamal ne yad'au ruri, ganin Numbern Mifzal yasa ya d'auka tareda sallama. Daga chan b'angaren Mifzal yace "Nasu Labarin Bilal da mai gidansa sun dawo Nigeria yau" Jamal yad'an zaro ido yace "Yanzu ya za'ayi" Mifzal yace "Na turo reports d'in nan abuja, gobe insha Allahu nima zan shigo sai mu cigaba da bincike" Sosai Jamal yaji dad'in labarin ya masa godiya sannan ya katse kiran. Ram yaba labarin yanda sukayi da Mifzal, yayi addu'an samun nasara suka fita zuwa yawonsu. A Zaria kuwa, bayan fitan Jamal da kusan awa biyu tajiyo hayaniya a farfajiyan Gidan, tashi tayi ta lek'a window Ma'aikata ta hango tsaitsaye a wajan sunata surutu. Aunty Faty ce ta fito ta tsaya gabansu "Zakuyi hak'uri yau kowa za'a sallamesa dan kusan ba'a tab'a dukiyar mamaci wuri" Nan fa ma'aikatan suka soma cece kuce, wasu na k'orafi wasu na fad'in albarkacin bakinsu. Mamaki ne ya cika Ummy, da tausayi ta dunga bin ma'aikatan da kallo hawaye cike a idonta. Mami ta hango ta fito sanye da hijab wasu mata na biye a bayanta. *Ayi hak'uri da wannan inada uzuri ne* Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/? Page 62 n 63 Mami ta hango ta fito sanye da hijab wasu mata na biye a bayanta rik'e da wasu buhuhuna. Wurin yayi tsit ganin Mami, d'aya daga cikin tsofafin masu aiki yace "Hajiya idan wani laifi mukayi ayi hak'uri, munyi Alka'awari Insha Allahu bazamu k'ara bah" Kan Mami tayi magana Aunty Faty tayi saurin cewa "Babu abinda kukayi bayanin dana muku farko shine dai" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Kuyi hak'uri, nasan yawancin ku da wannan aikin kuka dogara, muma ba munyi hakan baneh dan cin zarafin ku. Kunsan halin da dai ake ciki na rasuwar mai gidan, mu gaskiya bazamu iya d'aukan d'awainiyarku bah" Nan fa wuri ya sake kaurewa da hayaniya, Mami ta d'aga hannu tace "Ku saurareni" Nan wajan yayi tsit "Duk da haka bazan barku haka bah, duk da jiya akayi albashi, zan k'ara a kowannen ku naira dubu biyar biyar, mata na basu atampa super kowacce, maza kuma na basu shadda gezina." Badan ran ma'aikatan yaso ba suka bi layi, d'aya bayan d'aya Mami ke basu dubu biyar biyar, Aunty Faty na mik'a musu Atamfan, maza kuma shadda. Kuka Ummy ta saki sanda ta hango Laurat a kan layi. Sosai ta tausaya ma masu aikin. A ranar dukkansu suka tattara inasu inasu suka bar gidan. A sace Laurat ta shigo side d'insu Ummy. Rungume juna sukayi suna kukan rabuwa. Ummy ta haura sama dasauri ta d'auko paper da biro "Tunda baki da waya ki rubuta min addreshin ki insha Allahu wata rana zaki gani" Laurat ta amsa takardan tana hawaye ta rubuta mata address d'in ta mik'a mata. Suka sake rungume juna, cikin kuka Laurat tace "Allah yasa mu gana Ummy" Ta janye jikinta dasauri yana kuka tabar side d'in. Kuka kam Ummy tasha harta gode Allah, gaba d'aya ma'aikatan sun tafi sai masu gadi biyu da kuma wasu mata su biyu wanda batasan aikin me suke bah. Dadddare da Jamal ya kirata bata fad'a masa maganan tafiyan yan aikin ba dan a tunaninta da saninsa akayi. Hira suka sha sosai har zuwa sha biyu sannab sukayi sallama ta kwantah. Washe gari tana sallan asubah ta koma ta kwanta, bata farka ba sai k'arfe goma da kwata. A kasalance ta mik'e saboda yanda takejin jikinta, wanka tayi sannan ta shiga kicin ta had'a ruwan lipton ta fito dan shi kad'ai yanzu take iya kaiwa cikinta, shima wata ran amanshi takeyi. Dinning ta zauna harta kai kofin bakinta Mabrookah ta shigo falon tana yatsine yatsinen Fuska "Uwar kinibibi idan kin gama Mami nasan ganinki" Ta juya tabar falon tana wani botsaro baya, da ido Ummy ta bita har ta sauka, a gurguje tasha tean ta shiga d'aki ta d'au Hijab, wayanta ne ya soma ruri kamin ta k'arasa har ya tsinke, missed calls d'in Jamal ta gani har guda goma, bata d'au wayan ba ta juya ta fita sannan yasa hijabin ta nufi side d'in Mamin. Da sallama ta shiga falon, kamar kullum yauma hakane saida gabanta ya fad'i da suka had'a ido da Aunty Faty, ta nemi guri chan nesa dasu ta zauna tareda gaida su. "Wai na tambayeki" cewar Aunty Faty "A gidanku haka kikeyi har sai rana ya fito sannan zaki gaida uwarki" Gaban Ummy ya fad'i ta duk'ar dakai k'asa idanunta cike da kwalla. Mami ta

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82