Skip to content

Chapter 51

Chapter 51

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

idonta. Da saurinsa ya k'arasa ya hau gadon tareda rungumota jikinsa. sosai yaji jikinta yayi zafi, a rud'e ya d'agota "Wife meya sameki? temperature d'inki its so high" Kasa ce masa komae tayi har lokacin idanunta a lumshe. suranta yayi ya shiga toilet da ita ya mata wanka ya gasa mata jikinta. da kansa ya shiryata har lokacin hankalinsa ba'a kwance yake bah. dogon riga ya saka mata mara nauyi, sosai taji dad'in wankan dan har tad'anji dama dama. Rungumota jikinsa yayi ya rad'a mata "Sannu Wife, taso muje asibiti" Ta turo baki ta kauda kai, a shagwab'e tace "Nidai bazanje asibiti bah, na warke" K'ara matseta yayi a jikinsa "No pls, kinga har yanzu jikinki da zafi." Ya soma shafa suman kanta a hankali "I love uh so very much, Banasan ganinki a damuwa" Ta rungumesa sosai tana turo baki, bayanta ya soma shafa mata a hankali. Cikin mintina kad'an bacci ya d'auketa. Kwantar da ita yayi kan gadon yana mamakin baccin datayi dan yasan ita ba ma'abociyar baccin rana bace. Fita yayi ya koma d'akinsa shima yayi wanka ya fito. Wayan Mifzal ya kira bugu d'aya ya d'auka, bayan sun gaisa ya sanar dashi halin da ake ciki na maganar Alhaji Tijjani. Daga chan b'angaren Mifzal yace "Abu na farko shine ka fara neman Lawyern Abba first, kaje abujan office d'inshi ka duba shi. dan wannan ba k'aramin magana baneh" Ajiyar zuciya Jamal ya sauke sannan yace "Duk fa maganan nan da ake ni da Mami bamuda masaniya akan komai na dukiyar Abban" "Dole shi lawyern sa zaisan komae dangane da dukiyar nasa. abinda nakeso dakai shine kayi k'okari ka tafi abujan zuwa gobe ko jibi, sannan ka samu lawyer kaima dazai tsaya maka" Shiru Jamal yayi yana tunani, Ramadhan ne ya fad'o masa a rai, dan Barrister ne shima mai zaman kansa. Ya sauke nannauyan ajiyan zuciya yace "Zanma Ram magana, nasan komae zaiyi daidai" Sukayi sallama ya kashe kiran, hawaye ne ya gangaro masa. Shikenan yanzu ya zama maraya ba Abbah. Kuka ya soma kaman k'aramin yaro saida yayi mai isarsa sannan bacci mai nauyi ya d'aukesa a wajan. K'arfe hud'u da rabi ya farka saboda yunwar data addabeshi, yau kwanan Wife d'inshi ne gashi batada lafiya. Tashi yayi yayo alwala ya fito ya tada sallahn la'asar. Daidai lokacin itama ta farkah, toilet ta shiga ta sake yin wanka da alwala ta fito. tana idar da sallah ta mik'e ta cire hijab d'in jikinta ta fito dan tasan Jamal baici komai bah.Tana fitowa sukayi kicibus dashi shima ya fito daga d'akinsa. ware mata hannu yayi alamar ta taho gareshi, dagudu taje ta rungumesa tana murmushi. Janye jikinta tayi dasauri tana b'ata fuska. ya sake rungumota "Ya jikin Wife" Zuciyar ta ne ya soma tashi, ta k'ara turesa tana yatsine fuska "Kai Wife dan Allah, why bakiso ina zuwa kusa dake." Ya shagwab'e fuska kamar yanda takeyi, k'ara matsawa tayi "Ni banasan k'anshin turarenka neh" Da mamaki ya kalleta, ta turesa dasauri tabar wajan. Ajiyan zuciya ya sauke ya bita har kitchen din, indomie ta dafa yana tayata har suka gama. da kansa ya bata a baki, chokali biyu ta amsa ta kauda kai gefe "Na lura kwana biyun nan baki san cin abinci" Baki ta turo gaba "Na k'oshi" Kwaikwayan yanda tayi maganan yayi, dariya tayi tana hararansa. gaba d'aya k'amshin abincin ne ya addabeta, ta mike tana runtse ido, ya bita da kallo har ta shige d'akinta. Saida yaci ya k'oshi sannan ya shiga d'akinsa. kiraye kirayen sallahn magribah aka soma yayo alwala ya fita zuwa masallaci.Yana chan har akayi sallah isha'i, wayan Ram ya kira ya masa bayanin abubuwan dake faruwa, ba tare da wani dogon tunani bah yace su had'u ranar friday a kaduna sai su tafi abujan tare. Yana shiga gida side d'in Mami ya nufa dan rabansu da b'angaren tun da safe, Bai samu kowa a falon k'asan ba ya haura sama zuwa d'akin Mamin. Kan sallaya ya sameta tana lazimi, ya zauna kusada ita har ta gama tayi addu'a ta shafa. da murmushi yace "Sannu da hutawa Mamina" Murmushi ta masa sai kuma kuka ya kufce mata, da rarrafe ya k'araso inda take hawaye cike a idonsa ya rungumeta shima ya soma kukan, muryanta na rawa tace "Allah ya jik'an Alhaji" "Amin" yace a hankali yana rungume da ita har lokacin suna kuka a tare. Bayansa ta soma bugawa a hankali tana cewa "Your Dad was a very good Man. naji dad'in zama dashi" Kuka ne ya k'ara kufce mata dakyar ta iya cewa "Try to b like ur father Jamal. inaso nayi alfahari dakai a matsayin d'ana, kamar yanda nayi alfahari da mahaifinka. Mutun neh na gari mai gaskiya" Cikin muryan kuka tace "Mai tausayin talakawa, mai taimako. Har ya mutu yana rik'e da addini sosai" D'ago fuskanta yayi yana share mata hawayen dake gangara daga idonta. "Its ok Mamina, stop crying. Insha Allah zakiyi alfahari da kasancewa na d'anki" Hawayen fuskansa itama ta soma sharewa tana murmushi, ta sake rungumesa wasu hawayen na gangara daga idonta. "Allah ya isan mana wanda suka kashe mana shi, sun cucemu" Sake d'agota yayi daga jikinsa yana sake share mata hawayen "Insha Allahu komau ya kusa zuwa k'arshe Mamina" Kwantar mata da hankali ya dunga yi har zuciyarta yad'an sanyaya, sannan ya sanar da ita maganan tafiyarsu neman Lawyer. Addu'an samun nasara ta masa yayi godiya tare da mata saida safe ya fita. Wulgawan mutum ya gani a k'ofar d'akin, kamar an lab'e anji abinda sukace, bayansa ya juya baiga kowa ba ya yatsine fuska tareda d'aga kafad'a ya wuce. Aunty Faty ce ta fito daga inda ta b'oye tana tab'e baki tana bin hanyar dayabi da harara. Motansa ya shiga ya fita yayo musu take away harda Mabrookah ya dawo. Kasancewar ba ranar girkin Mabrookah baneh yasa ya lek'a d'akin da sallama rik'e da ledanta. Tana kwance ruf da ciki akan gadonta daya chukur kud'e ba gyara. Girgiza kai yayi cike da takaici ya aje mata ledan kusa da ita "Ga naki. Sai da safe" Bai jira mai zatace ba yabar d'akin, dakinsa ya shiga yayi wanka ya sauya kayansa sannan yad'au ledan ya nufi d'akin Ummy. Da sallama ya bud'e kofan, kakarin amai ya soma ji daga toilet d'inta, dasauri ya shiga ya aje ledan ya k'arasa toilet d'in dasauri. Tsugunne ya sameta tana amai dafe da k'irjinta saboda yanda yake amsawa. Gabanta ya tsugunna tausayinta na ratsa sa ya d'agota yana mata sannu, tana ganinsa ta sake fashe wa da kuka, ya d'ibo ruwa ya wanke mata baki ya kaita kan gado yana cigaba da mata sannu. Toilet d'in ya koma ya gyara ya fito, kud'undune ya sameta cikin bargo tana kuka tana maida numfashi. Hankalinsa duk a tashe ta zauna kan gadon kusada ita ya yaye bargon ya d'agota tare da mannata jikinsa. Rawar sanyi kawai take tana kuka tana k'ara shiga jikinsa. Rasa bakin magana yayi tausayinta da santa ke k'ara shigarsa. Harya bud'e baki zaiyi magana ta tursa ta mik'e dasauri ta koma bayin ta durk'ushe tana wani aman kamar zata shid'e, ya biyota bayin ya dafata yana mata sannu. Wani kukan ta fashe dashi tana k'ara shiga jikinshi tana kuka. Wanka ya mata sannan ya

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82