Skip to content

Chapter 54

Chapter 54

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

tab'e baki tace "Ai kinsan tarbiya daga gida yake farawa, idan uwa babu ta yara zasu samu" Mabrookah ta amshe da cewa "Ragowar Soyesoye, Allah dai yasa cikin nan nasa neh" Aunty Faty tace "Aikuwa kinsan irinsu da bin mazan tsiya, wayasan nawa aka zubar kafin a samu wannan" Ummy ta fashe da kuka tace "Dan Allah kuyi hak'uri, zan dunga zuwa da wuri ina gaish..." "Dallah rufe mana baki" cewar Aunty Faty, itako Mami tsabar takaici ne ya hanata magana sai bin Ummyn take da kallo cike da tsana. "Ai tuntuni ke kikayi sakaci Maimunatu har kika bari ta zauna a gidan nan bayan warkewan sa" Mami ta tab'e baki "To ya zanyi, Alhaji ne yace bazata ko ina bah, kuma kinsan duk abinda ya fad'a ta zauna babu wanda ya isa ya tsallake" Aunty Faty taja dogon tsaki batace komai bah. Chan kuma tace "Ai ko wallahi kafin Jamal d'in ya dawo sai kinci ubanki a gidan nan" Ta maida dubanta ga Mami "Tunda yanzu babu masu aiki, ai ga wata mun samu" Mabrookah ta fashe da dariyan k'eta tace "Wallahi kuwa Mummy, ni kawai girki zata dunga min" Ummy ta d'ago ta kalli Mabrookah, aiko suka had'a ido "Bar kallona, shegiya Maiya. Kindai san Ya Jamal baya nan, wallahi sai na miki shegen duka naga uban da zai k'waceki" Nan Ummy tasha jinin jikinta, in akwai abinda take gudu bai wuce a tab'a lafiyar jikinta. Mami tace "Aikin gidan nan ya koma hannunki daga yau, shara, mopping, gyaran d'akunan mu da girki." Wani shu'umin murmushi Aunty Faty tayi tana kallan Ummyn sannan tace "Ai yau zata fara aikin nata tunda dai babu masu yi" Tana hawaye ya mik'e ta shiga store inda ake aje tsintsiya da sauran abubuwa. Mami ta kalli Aunty Faty tace "Babban bak'inciki na bai wuce cikin dake jikin yarinyan nan bah, harga Allah banasan had'a zuri'a da wannan yarinyar" Aunty Faty ta fashe da dariya mai sauti sosai "Kwantar da hankalinki Maimunatu, wannan ai abu ne mai matuk'ar sauk'i" Mabrookah ta sauke ajiyar zuciya dan itama sosai ta tsani cikin Ummyn. *** Da wuri Jamal da Ram suka shirya suka fita zuwa Office d'in lawyern dake zone 2, saidai abin takaici basu samesa ba sai PA d'insa nan yake shaida musu baya k'asar yaje wani confrence meeting a Cairo anma zai dawo zuwa tuesday. Ba haka ransu yaso ba haka suka koma hotel d'in da suka sauka. Sun yanke shawaran tsayawa a abujan har zuwa sanda zai dawo. Jamal ya d'auko wayansa ya cigaba da neman layin Ummyn bata d'auka bah. Hankalinsa ne ya tashi sosai na rashin d'aukan wayansa da batayi ba. Tunani ya soma ko jikin nata ne ya tashi, da lafiya lau yasan da yanzu ta d'auka. K'ara kira yayi har ya katse ba amsa, yayi wurgi da wayan tareda jan tsaki "Anya Ram bazamu koma zaria ba kuwa" Ram dake kan gado yana chating ya juyo da mamaki "Saboda meh?" "Tun safe nake kiran Wife bata d'auka, inaji a jikina something is wrong dan ko laifi na mata bata k'in daukan wayana" Ram ya mik'e zaune yace "To ka kira Mabrookah mana ko Mami" Jim yayi na 'yan mintina sannan ya soma neman layin Mami, bugu d'aya ta d'auka da sallama, bayan sun gaisa yace "Mami tun safe nake kiran Ummy bata d'auka bah, i donno ko jikin ne dan na barta bata jin dad'i" Tad'an juya ta kalli Aunty Faty dake zaune kusada ita sannan tace "Lafiya lau take kam, dan ko d'azu da safe tashigo ta gaishe ni" Nannauyan Ajiyan zuciya ya sauke har saida Mami ta jiyosa, ta tab'e baki tace "To ita Mabrookan ka kirata" Saida yad'anyi Jim sannan yace "Itama bata d'auka bah" Tambayansa abinda sukaje yi tayi yake shaida mata basu samesa ba sai ran tuesday. Tamai addu'a sosai sannan sukayi sallama. A b'angaren Ummy kuwa ta wahala sosai ranar, ga jikinta da ba wani k'wari, duk bayan 'yan mintina sai tayi amai, tana kuka tana aikin har ta gama, ba ita ta koma side d'insu ba sai bayan sallahn Magriba, dakyar ta iya k'arasawa d'akinta tayi wanka ta kwanta, nan da nan zazzab'i mai zafi ya rufeta. Cikin bacci taji wayanta na ringing kan bedside ta mik'a hannu dakyar ya dauka tare da karawa a kunne "Haba Wife yanzu abinda kikamin kin kyauta kenan" Kuka ta soma mara sauti "Ya salam! Meya faru? Ko jikin neh" Duk yabi ya rud'e hankalinsa a tashe, kasa fad'a masa tayi dakyar ta iya cewa "Bai kaine kak'i dawowa bah" Ya sauke ajiyar zuciya tare da k'ara kara wayan a kunnensa "Tun safe nake neman wayanki baki d'auka ba Wife, hankalina ya tashi sosai na d'auka jikin neh" Hawaye suka k'ara gangaro mata, cikin sanyin murya tace "Banga wayan baneh kuma yana silent, sai d'azu na duba k'arkashin gado ashe nan ya fad'a" "Pls ki daina sa wayanki a silent kinji" "To" tace a hankali, sun d'an tab'a hira sannan sukayi sallama. Kuka ta sake fashewa dashi na tausayin kanta kafin Jamal ya dawo. A daran ranar Mifzal ya iso abujan, nan hotel d'in dasu Jamal suka sauka nan shima ya sauka. Washe gari dasafe dukansu suka shirya suka fita. Saida Mifzal ya fara reporting a Station d'in dayakai case d'in sannan suka wuce Wuse 2 dan a nan suka samu labarin Bilal d'in yake. Daga bakin layin sukayi parking, Mifzal da Ram suka fito suka shiga cikin layin sosai suna takawa suna bin gidajen layin da kallo. Wani mai shago suka samu nan suka zauna kan benchn sa tare da masa sallama. Bayan ya amsa Ram ya mik'a masa dubu d'aya "Bamu Fayrous guda biyu" Jiki na rawa mai shagon ya mik'o musu dan yau kusan kwana biyu kenan babu ciniki, ya irgo chanji ya mik'a masa. Mifzal yayi saurin cewa "Ka bashi, dan Allah mallam in tambayeka mana" Jiki na rawa yace "Allah yasa na sani" "Dan Allah wani nake nema sunansa Bilal, abokina ne sosai saidai lambarsa ta b'ace a wayata. Kuma gashi tun daga Kano nazo nemasa" Mutumin ya rik'e baki da Mamaki "Wai! Kace kasha tafiya, sai dai ni bansan wani mai suna Bilal ba anan layin" Mifzal ya d'au wayansa ya zak'ulo hoton Bilal d'in dake jikin Dp d'insa na whatsapp ya nuna masa "Ka ganshi nan" Baki mutumin ya bud'e "Aa indai wannan ne ai na sanshi, yakanzo nan wayena yasayi sigari" Ram da Mifzal suka kalli juna da mamaki. Ram ya wayance yace "Tabbas kuwa shine, dan Allah bakasan gidan dayake bah" Wani dank'ararren gidan chan gefensa ya nuna musu da hannu "Ga gidan chan, saidai...." Yayi saurin yin shiru ya matse bakinsa da hannu, Mifzal ya kallesa yace "Fad'a abinda kakeso ka fad'a babu komae" Ram ya ciro dubu uku ya aje masa ga wannan ka tab'a, aiko d'an fulani ya gyara zama "Akwai abinda mu 'yan unguwan nan bamu gane masa bah" "Na meh fah" cewar Ram "Alhajin nan bashi fita sai da daddare, sannan kuma kullum sai kaga wasu murd'a murd'an mutane a k'ofar gidansa wanda mu bamu yarda dasu bah" Mifzal ya jinjina kai, "Kamar da wani lokaci sukafi zuwa?" "Kaman tara haka zuwa goma na dare idan dai kazo nan zaka samesu" Mifzal

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82