Chapter 75
Chapter 75
saurin rik'osa yana cewa "Haba D'an Mami yi hak'uri mana, zauna kaji" Ya zaunar dashi shima ya zauna suna fuskantar juna "Suna prison yanzu haka baza'a bari ka gansu bah" Shiru yayi baice komai bah, Ram ya soma jansa da hira har ya samu ya ware sukayi ta hira, a nan yake basu labarin zuwan Areefah." A gida kuwa Areefah na sallah ta koma side d'insu Ummy, Kallo d'aya tama Mabrookah taja guntun tsaki ta haura sama wajan Ummy. Hira sukayi tayi gwanin ban sha'awa, tare sukayi abincin dare sunata hira kamar sun dade da sanin juna. Ran Mabrookah ya sosu sosai, ta mik'e ta shiga kicin ta soma kici kicin d'aura abinci. Tuwon shinkafa tayi da miyar Alaiyahu datasa Mai gadi tasayo mata. Cikin k'ankanin lokaci ta gama, wanka tayi ta sauya zuwa dogon rigan shadda. Ta had'a abincin a tray ta d'auka bayan anyi sallahn magriba, dai dai nan Areefah ta sauko da Tray itada Ummy, Kallansu Mabrookahn tayi ta watsar tayi gaba suna binta a baya, Areefah sai yatsine fuska take dan gaba d'aya Mabrookah bata burgeta, da Sallama Mabrookahn ta shiga Ammi ta amsa, kan dinning ta aje Trayn a tsaye k'erere ta gaida Ammin tana wani cika tana batsewa. Areefah ta k'arasa kan dinning d'in ta ture trayn Mabrookahn gefe ta aje na hannunta, Sannan ta amsa na Ummy a aje, Ammi na daga gefe tana ta musu sannu da godiya. Mabrookah tayi gaba, Itama Ummy ta mik'e ta musu saida safe ta fita, a falon k'asa tayi kicibus da Mabrookahn tana jiranta "Kwad'ayaiya, nasan dai duk abinda kikeyi nan na kwad'ayi ne dan kinga suna dashi, An saba da maula" Ran Ummy ya sosu ta wuce zata haura sama ta sake jiyota tana cewa "In ma so kike ki mallake su karyanki tasha k'arya, Uwa ta saba da bin bokaye dole 'ya ma tad'au hanya. Wayasan abinda aka kitsa miki da kikaje gidan ranan" Ran Ummy idan yayi dubu ya b'aci, ta sauko k'asan "Kullum kina zagina ban tab'a maida miki da martani bah, dan har yanzu ina miki kallan wadda ta girme mani, ko ba komai kin fini shekaru bazanyi musu dake bah. Anma yau kin kaini bango" Wani shewa Mabrookah ta saki tana cewa "In kinama Allah kada ki k'ara ganin girman nawa" Murmushin takaici Ummyn tayi tana cewa "Kiyi ta zagina daga nan har abada anma karki k'ara zagin iyayena dan basu miki komai bah" Bata ankara bah taji saukan Mari a kuncinta, ta dafe wajan dasauri tana kallan Mabrookahn "Kika mareni" Tana huci tace "An mareki ko zaki rama neh, shegiya 'yar masu bin bokaye" Mari Ummyn ta d'auke Mabrookahn dashi mai rai da lafiya, nan fa fad'a ya kaure tsakaninsu, kokawa suka shiga yi tsakaninsu dai dai lokacin Jamal ya shigo cikin gidan, kamar zai shiga side d'in Abba sai kuma ya nufi nasa, yana shiga Mabrookah ta rarumi Dogon speakern home theatern dake Falonta ta bugama Ummyn a...... Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 90 _*A Gurguje*_ Yana shiga Mabrookah ta rarumi Dogon speakern home theatern dake falonta ta bugama Ummyn akai, Wani k'ara ta saki take ta fad'i wajan a sume jini na fita a kanta. Jiki na rawa ya k'arasa falon gaba d'aya jikinsa rawa yake, tsugunawa yayi inda Ummy ke wance ya d'agota hawaye cike da idanunsa, d'agowa yayi yana wani irin huci yana kallan Mabrookah wace ya yarda Speakern itama jikinta na rawa tana kuka. A fusace ya mik'e ta juya zata gudu ya kamota ya soma had'ata da bango yana kuka, ihu take a wahale tana neman agaji, Ammi da Areefah ne sukaji yo ihun Ummy da farko, har Areefahn ta mik'e Ammi ta hanata, jin wani ihun yasa suka mik'e a tare sukayo side d'in. Suna shiga ya sake bugata da bango ta saki k'ara take itama kanta ya fashe. Ammi ta k'arasa dasauri inda suke tsaye ta rik'esa gaba d'aya ta rud'e "Jamaludeen karka kasheta, stop! Control your anger" Ya jefar da ita tare da nunta da yatsa "Na sakeki! Na sakeki!!" Harya bud'e baki da niyar furta wani abu Ammi ta d'aukesa da wani gigitacen Mari "A gabana Jamaludeen!" Baice komai ba sai hucin dayake, Areefah ko tunda ta shigo ta fashe da kuka ganin Ummy kwance cikin jini, inda take ta k'arasa ta tsugunna tana kuka. Jikinsa na rawa ya d'au Ummyn yayi waje da ita, ko takalmi babu a k'afan Areefah tabi bayansa, mota ya sakata ya ja da k'arfi bayan Areefah ta shiga suka bar gidan. Fitowansa yayi daidai da fitowan Abba da Areef daga masallaci, da ido sukabi motan ganin yanda yake gudu kamar wanda zai tashi sama. Suna shiga Ammi ta fito daga side d'in rik'e da Mabrookah wacce itama kanta ke jinin "Subhanallahi meya faru?" Cewar Abba yana k'arasawa wajan, Ammi bata b'oye masa komai akan abinda ta gani bah, sam Abbah baiji dad'in abinda ya faru bah. Areef yana daga gefe yana cin magani yanata ma Mabrookahn Allah ya k'ara a zuciya dan dama kwata kwata bata burgesa. Wani Private hospital mafi kusa Jamal yakaita, duk tabi ya rude in banda hawaye babu abinda yake haka Areefah dake gefensa sai kuka take itama, suna isa aka amsheta sukayi Emergency da ita, Wata nurse ta umarce shi daya je ya biya kud'in kati da sauransu, ba musu ya nufi receiption Areefah na biye dashi. Suna nan zaune wata nurse ta fito daga d'akin, Areefah tayi saurin mik'ewa tasha gabanta "Dan Allah ya jikin nata?" Nurse d'in ta mata murmushi "Dasauk'i karku damu" Bata jira cewar Areefan ba tabar wajan dasauri, suna nan tsaye likitan ya fito, Bayani yama Jamal d'in akan abin bai yi serious ba saidai su kiyaye nan gaba. Sannan ya basu umarnin shiga su ganta. Kwance suka sameta kan gado kanta nan nad'e da bandage tana bacci hankali kwance, wani nannauyan ajiyan zuciya Jamal ya sauke ya k'arasa bakin gadon, Areefah ta rik'e hannunta hawaye cike a idonta "Allah zai saka miki Aunty, kuwa wallahi..." Taji k'wafa ranta b'ace. Shidai Jamal bai iya cewa komai bah. Suna nan Abba ya kira wayan Jamal yana tambayansa mai jiki, halinda ake ciki ya fad'ama Abban sai a lokacin suma hankalinsu ya kwanta. A gida kuwa Ran Ammi ya b'aci sosai gaba d'aya ji tayi Mabrookah ta fitar mata a rai, babban damuwarta bai wuce cikin dataga alamar Ummyn nadashi bah. Buris tayi da Mabrookahn haka shima Areef ji yake kamar ya rufeta da duka. Dad'in ta d'aya ma dayaji Ammi tace Jamal ya saketa. Rashin sani gari yasa Abba had'a Mai gadi d'aya da Areef da ita Mabrookahn aka kaita wani Chemist nan kusa akayi mata treating kan. Koda Jamal ya fad'ama Abban halin da Ummyn ke ciki kasa sukuni Ammi tayi, kwatance tasa ya musu Areef ya d'aukesu itada Abba sukaje asibitin. Ammi har hawaye tayi ganin Ummy kwance a kan gado, Kwana biyun nan da sukayi sosai ta shiga ranta. Ta share hawayen fuskanta tana kallan Abba "A gaskiya Alhaji zaman Jaleelah da Yarinyan nan Mabrookah bazai yuwu bah" "Wani irin magana kike haka Hajiya, karki manta fah matarsa neh bamu isa mu rabasa ta itaba" Shidai Jamal
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82