Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

kallan hannun tareda murmushi "Kyawun zoben yasa na siyeshi, dan nasan zaima Hrt d'ina kyau. Ki rik'emin amana pls, duk da nasan ke tawace, just 2weeks zanyi kinji" Kai ta gyad'a mai ya mata sallama ya shiga gidansu da sauri, tsaye Ummy tayi a kofar gidan tana kuka a hankali, tana san Ya Bilal tana kishinsa, batasan koda na kwana d'aya su rabu. Saida tayi mai isarta sannan ta shiga gida.. Kasancewar lokacin sanyi ne har Mama ta shiga d'aki saidai tana d'aga bak'in kofa tana jiran Ummyn, tana shigowa taji Mama daga d'aki tace "Ummy kece" A hankali tace "Eh Ni ce" "Yaudai kam kun dad'e" Batace komai ba ta shige d'akinta ta fad'a kan katifarta tana ajiyan zuciya. Kud'in dake hannunta ta duba, dubu biyu ne y'an dari biyar biyar guda hud'u. Ta tusa su k'arkashin Pillow ranta duk ba dad'i Tunanin rayuwar Ya Bilal ta soma, tun tasowan shi yake aikin k'arfi dan taimaka mai mahaifiyarshi da k'aninshi, ga kuma itada da iyayenta, duk da nauyin dake kanshi bai hanashi yin karatunshi bah, ynzu haka yanada degree saidai ita batama san maiya karanta bah. Tunani kala kala ta dunga yi har bacci ya d'auketa Da safe kamin ya tafi saida yashigo shida Bahar sukaima su Mama sallama, ya shiga sukayi sallama da Baba sannan suka fito Ummy na biye dasu, Bahar ya basu waje sukai sallama sai kuka takemai a haka suka rabu kowa zuciyarshi ba dad'i Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 11:34 PM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to my *Late Siblings* *Page 4* A haka suka rabu kowa zuciyarshi ba dad'i, yinin ranan sukuku Ummy ta yini, ko abinci tak'i ci saidai ta zauna tayi tagumi. Tun Mama na bata baki har ranta ya soma b'aci ta hau mata fad'a Haka suka cigaba da rayuwa a gida har na tsawon sati hud'u, tun Ummy na irga ranakun dawowan Bilal harta daina tasawa sarautar Allah ido, so dayawa takan shiga gidansu Bilal dan dai kawai taji ko ansamu labarinsa Anma shiru. Abubuwa sun taru sun mata yawa ga Rashin sanyin idaniyanta Bilal, ga talauci da suke fama dashi dan tuni sun cinye jarin waran, abinci ma yanzu dak'yar suke samu. Sosai abin ke damun Ummy duk ta rame tayi duhu kamar ba Ummyn dah bah.. Tana d'aki tana tunanin yanda rayuwarsu ta sauya lokaci guda, a hankali hawaye ya zubo mata murya chan k'asa tace "Allah sarki Baba Sanda kakeda idanu da lafiya ka watada mu, munji dadi Allah ya baka lafiya yasa kaci wannan jarabawan" Fashewa da kuka tayi mara sauti, saida tayi mai isarta sannan ta mik'e zaune tareda goge hawayen idanunta. Tunani ta soma na yanda rayuwarsu zai inganta nan gaba dole ta nemi mafita dan bazasu zauna su dogara ga Bilal ba shima akwai d'awainiyan gidansu a kanshi, dauriya kawai yake. Wasu hawaye ne suka zubo mata "Ya Bilal kana inane? Ka dawo dan Allah" Mik'ewa tayi a sanyaye ta janyo hijabinta tasa ta fito tsakar gidan, Mama ta gani tana kok'arin fitoda Baba tsakar gida yasha Iska. Dasauri ta k'arasa ta taimaka mata ta zaunar dashi kan tabarma "Sannu Baba" "Yauwa Sannu Ummy, ku cigaba da hak'uri kunji wata rana sai labari" Hawaye suka cika idanunta, ta shiga d'akinshi ta d'auko sandar shi ta tsugunna tace "Baba ga sandary ka" Lallube ya soma, ta kamo hannunshi ta saka mai sandar "Yauwa Ngd Ummy" Ta dubi Mama dake gefenshi tace "Mama barin shiga wajan Inna Yanzu zan dawo" (gidansu Bilal) "Tho a dawo lapia, karki dad'e" Tho tace ta mik'e ta fita, a zauren gidansu Bilal ta had'u da kaninshi Bahar, Gaidashi tayi ya amsa yana cewa "Ya kewar Yaya" D'an murmushi tayi kanta k'asa "Har yau bama samun wayansa, ina ga zanzo ne na bishi Abujan nan kawai dan jikina na bani ba lafiya" "Yanzu idan kaje Abujan ta ina zaka fara? Ance. Tanada girma sosai, mezai hana muje inda suke aiki ko zamu samu labarin shi wajan abokanan aikinsu dake nan" Gyad'a kai yayi "Hakane kin kawo shawara" "Barin shiga na gaida Inna sai na fito mu tafi" A tare suka shiga gidan, Inna na zaune tsakar gida tana bakace masara "Ummy ce da tsakar ranan nan" A kunyace ta tsugunna ta gaida Innan, "Ya Babanku da jiki?" "Dasauk'i" tace a hankali har lokacin kanta k'asa. Sallaman da akayi ne ya katse su, wata dilaliya ce dake anguwan ta shigo tana cigaba da rafka sallama, Ummy da Inna suka amsa mata ta k'araso ta nemi guri ta zauna, Ummy ce ta soma Gaidata sannan ta mik'e "Inna bari muje wajan aikinsu Ya Bilal yanzu zamu dawo" "Tho a dawo lapia" inna ta amsa mata, tana kok'arin fita daga gidan taji dilaliyan na cewa "Wallahi Ladidi wasu gidaje ne aka kawo min cigiyan masu aiki kuma za'a samu alheri dan ba gidajen k'ananan mutane baneh gashi har yanzu ban samu yarinya ba" Fita daga gidan tayi da sauri suka had'u da Bahar suka wuce wajan, mutanen dake wajan suka tambaya a nan suke shaida musu mummunan labari, d'ayansu ne yace "Ranar da suka tafi motarsu tai hatsari duka sun rasu babu wanda ya fita, dan achan aka musu sallah saboda yanda gawawakinsu sukayi" Ai bai k'arasa maganan ba Ummy ta fad'i wajan sumammiya.. Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 11:36 PM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* ​Page 5​ Ai bai k'arasa Maganan ba Ummy ta fad'i wajan sumammiya. A gigice Bahar yayi kanta yana kuka, jama'ar dake wajan sun tausaya sosai. Masu aikin wajan suka tsare musu napep suka saka Ummy dake sume a cikin napep d'in suka nufi gida. Suna isa gida Mai napep da Bahar suka shi da Ummy cikin gida sai kuka yake, a nan yake sanar da Inna abinda ke faruwa, nan itama ta sume a wajan kamin kace me unguwan gaba d'aya ta d'auka ko wane lungu da sak'o sunji labarin rasuwar Bilal.. Sosai rasuwansa ya girgiza mutane saboda Bilal mutum ne mai Gaskiya da rik'on amana, ga addini da son jama'a. Ba abnda ke tashi daga gidan Inna sai koke koke, Baba da Mama suna daga cikin sukajiyo kuka daga gidan Inna, ta yafa mayafinta ta fito tun a kofar gida ta soma cin karo mutane sunata shiga, itama ba'a barta a baya ba tana shiga taji wannan mummunan labari. Kuka ta soma ta k'arasa inda ze zaune ta rungumeta tareda fashewa da kuka "Allah ya jik'anka Bilal yasa ka huta" Ta k'ara rushewa da wani sabon kuka, Ummy ko dogon suma tayi bata farka ba sai washe gari da safe, a hankali ta bud'e idonta ta suka k'ankance Mama ta gani kusada Ita itama fuskanta ba walwala, mik'ewan datake k'okarin yi yasa Mama tasan ta farka "Sannu Ummy, ina zakije" Fashewa da kuka tayi tana kallan Mama "Mama yanzu dagaske ne Ya Bilal ya rasu" Kanta Mama ta shafa tana lallashinta "Bilal lokaci yayi Ummy, yanzu addu'an mu yake nema ba kuka ba kinji. Kiyi hakuri ki fawala wa Allah" Girgiza kai take tana kuka da k'arfi "Aa Mama, Ya Bilal bai mutu ba ni nasani bazai tab'a mutuwa yabarni ba. Dan Allah Mama idan wasa yake kuce ya

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82