Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,194 words 0 views Progress saved
Download Book

ta fito ta tsugunna ta gaidasa, Mami ya tambaya tace taje aiki, baice komai ba ya haura sama zuwa d'akin Jamal. Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 8:33 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* _*Shekara shidda kenan da rasuwan d'aya daga cikin yanina, Ina baran Adduar ku Allah ya masa rahama yasa Aljanna ce makoma a gareshi. Ameen*_ Page 17 Baice komai ba ya haura sama zuwa d'akin Jamal, wayam yaga d'akin ya fito dasauri ya nufi sashin masu aiki yana tambayansu inda Jamal d'in yake, Laurat ce masa jagora har zuwa garden din. Tun daga nesa ya hangosu tana share masa zufa tana cigaba da rera masa karatun alkur'ani, dakatar da Laurat saurayin yayi suka tsaya nan wajan sai binsu da ido yake. Suratul Baqrah tayi bismillah ta fara, tana kan aya ta ashirin bata ankara ba taji an mak'ure mata wuya, idanunta ta fifito dasu ta d'ago dasauri Jamal ta gani idanunshi sun rune sun koma ja haka fuskan nasa, tari ta soma had'e da kakari tasa hannayenta tana k'okarin cire hannunsa akan wuyanta. Dasauri saurayin nan ya k'araso wajan ya soma janta dakyar ya samu ya fincike hannunsa daga wuyan Ummyn, chan gefe ta fad'i tana rik'e da wuyanta tana tari had'e da kuka kamar ranta zai fita. Laurat ta k'arasa wajanta dasauri, shi kuma saurayin ya tsaya gabanshi yayi bismillahi ya cigaba da karatun daga inda ta tsaya fuskarshi d'auke da damuwa. Wani irin zabura Jamal d'in keyi yana wani irin ihu, belt d'in wheel chairn ya tsitsinka yana ihu yana k'okarin mik'ewa, kan kace meh ma'aikatan gidan sun taru a wajan suna ba idanunsu abinci, itako Ummy nachan gefe idanu sunyi luhu luhu sabda shak'an da yamata. Karatun saurayin ya cigaba yama wasu maza cikin masu aikin nuni akan su rik'eshi, su wajan biyar suka rik'eshi da kyar yanata k'okarin kwacewa. Wajan da Ummy take Saurayin ya k'arasa ya duk'a yace "Sannu tashi ki k'arasa ladanki" Kallanshi ta tsaya yi ya gyad'a mata kai ta mik'e tana rik'e da wuyan nata suka cigaba da rairo karatun alkur'ani a tare, chan gefe saurayin ya matsa ya soma neman Layin Abba, bayani ya masa sannan ya kashe ya kira Mami. Wani kukan kura Jamal yayi ya doke samarin dake rik'e dashi yayi kan Ummy, bata ankara ba taji ya d'auketa chak yayi wurgi da ita, wani razananen ihu ta saka a hankali ta sulale ta sume. Daddaneshi samarin suka k'arayi, duk hankalin saurayin nan baya jikinshi, kota kan Ummyn beyi ba sai safa da marwa dayake tayi a wajan, k'aran mota sukaji kan kace me masu aikin dake cike a wajan kowa yayi hanyarsa dasauri, Hankali tashe Abba ya shigo garden din shida wani dattijo, ganin halinda yake ciki yasa Abba ya karasa dasauri yana kokarin kama Jamal d'in, Dattijon ya dakatar dashi dasauri yamai nuni daya matsa, hawaye suka soma gangaro ma Abba ya matsa yana kallan d'an nasa. Ruwa dattijon yasa aka kawo mishi a wani bowl, addu'a yayi ya tofa yace samarin su sakeshi, suna sakeshi ya yunk'ura zai tashi Dattijon ya watsa masa ruwan a fuskansa da kirji, wani Ihu ya saki ya koma ya zauna har lokacin idanunshi a jujuye. Dattijon ya tsugunna gabansa yace "Wanene kuma me kake nema a jikinsa" Shiru yayi chan kuma ya soma wani irin ihu kamar na doki, Dattijon yayi murmushi yace "Kunaso ku nuna taurin kai koh? Idan bakuyi magana ba zan la'anta ku zan d'aidaita ku" Nan ma dai baiyi magana ba sai zare zaren ido dayake, Ana cikin haka Mami ta karaso wajan hankali tashe, ganin halinda d'an nata yake ciki yasa ta sulale ta zauna ta fashe da kuka. Dattijon nan kuwa ganin sunk'i magana yasa yayi gyaran murya ya soma karatu cikin k'ira'a mai dad'i, Nan ya soma ihu yana fizge fizge tareda Birgima a k'asa. Sun d'au lokaci a haka sannan yayi wani irin ihu yace "Ku tsaya zamuyi magana" Dattijon yace "Meyasa ka shiga jikinshi" Jamal yace cikin wani irin k'aton murya "Turomu akai dan mu kulle alak'ar sa, mu muka daki motarsa shekara uku da suka wuce mukayi anfani da wannan daman" Dattijon yace "Ka fita daga jikinshi sannan kaji tsoron mahalucin ka" Wani dariya Jamal d'ina yayi yace "Harkai ka isa kasa mu fita" Dattijon baice komai ba ya cigaba da karatun alkur'anin, Ihu ya cigaba ganin ba sarki sai Allah yace "Ka tsaya tsoho, ka daina k'onamu zamu fita" Dattijon yace "Maza ku fita sannan ku fita ta hanci" Atishawa Jamal d'in yayi sau uku sannan ya sulale baci mai nauyi ya d'aukeshi. Hamdala Abba ketayi ya k'araso ya tsugunna ya d'ago kan d'an nasa yana murmushin farinciki, "Allah na gode maka, Allah abin godiya" Dattijon yace "Alhamdulillah, sun fita sai a kiyaye" Ya kalli Abba yace "Zan turo akawo magani da zai cigaba da anfani dashi insha Allahu komai zai warware" Mami ta d'ago dasauri tana kallan Malamin "Yanzu Mallan lapia lau zai tashi ba wata matsala" Kai Mallamin ya gyad'a mata, ta fashe da kuka takai goshi k'asa taima Allah godiya. Godiya kam Mallamin nan yasha wajan Abba, kud'i masu yawa Abba ya basa yak'i karba yace yayi sadaka neh, nan suka k'ara masa godiya Abba yasa driver ya kaishi gida. Da taimakon Saurayin nan Abba ya d'au Jamal d'in suka d'aurasa kan Wheel chairn, sai a sannan idanunsu ya sauka kan Ummy dake kwace achan gefen Garden d'in kanta na fitarda jini. Abba hankali tashe ya nufeta shida Mami yana cewa "Ramadan garin yaya haka ta faru" Bai iya cewa komai ba ya d'auketa chak yana cewa "Tana bleeding akai, ka kira doctor Abba" Cikin gida yayi da ita, Mami ta gunguro Jamal ta shiga ciki tashi Abba kuma ya soma neman layin doctorn. Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 8:30 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* ``` Ina kuke JAMALUDEEN FANS group Wannan shafin naku neh. Kuna bani farinciki sosai, ina godiya buhu buhu ``` Page 18 Cikin gida yayi da ita, Mami ta gunguro Jamal ta shiga ciki dashi, Abba kuma ya soma neman layin doctor. Mami tama Ramadan nuni da d'akin Ummyn, ya shiga ya shimfid'eta kan gado yana kallanta, sosai kanta ke fitar da jini, yasa wani zaninta dake kan gadon ya tare jinin gabanshi na fad'uwa. Bayan kamar minti goma sha biyar likitan ya k'araso gidan, bashi guri yace Ramadan yayi shi kuma ya shiga dubata. Mami da Abba suna bakin k'ofan chirko chirko cikeda zullumi, a haka Mabrookah ta shigo gidan ta samesu, tambayan abinda ya faru tayi Mami ta mata bayani cikeda damuwa. Likitan ya d'au lokaci kamin ya fito ya samu Abba nan bakin k'ofan, Mami ce tai saurin k'arasowa itada Ramadhan, likitan ya kalli Abba yace "Da sauki Alhamdulillah, saidai ta bugu sosai a kanta sannan ta samu karaya a hannunta na hagu" Mami ta saki sallati tana duban likitan "To yanzu wani hali take ciki doctor?" Cewar Ramadan Likitan ya cigaba da cewa "Na mata allurar bacci saboda yanayin da take ciki, but idan so samu ne da an kaita asibiti idan ta farka saboda ai mata xray ko akwai wata matsala" Ramadan ya mik'a masa hannu sukayi musabaha

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82