Chapter 67
Chapter 67
kanta. Ya direta kan gado tana cigaba da turo baki "Zaki fara koh" Ta sake zumb'uro baki, bata ankara ba taji bakinsa cikin nata sam batayi yunk'urin hanasa ba dan ita kanta tayi missing d'insa alot. Sun dad'e a haka ganin yana neman wuce gona da iri yasa ta janye jikinta ta mike tana turo baki ta shiga toilet. Saida ta wanke toilet d'in sannan tayi wankan ta fito, kishingid'e ta samesa kan gado idanunsa a lumshe fuskarsa d'auke da murmushi. Itama murmushin tayi "Kaje kayi wanka sai ka huta" Yad'an bud'e idonsa ya zubasu akanta, ya mik'a mata hannu "Zo kiji na fad'a miki" Ba musu ta k'arasa inda yake ya janyota ta fad'a jikinsa, juyata yayi ta koma k'asa ya mata runfa da kafadarsa. Ba tare da b'ata lokaci ba yakai bakinsa kan nata, Soyaiya ya shiga nuna mata mai wuyar fassara kuma da alama tana karb'ar karatun nasa. Jin yanaso ya tsallaka yasa ta saki kuka tana turesa "Dan Allah ka daina" Ya d'ago idanunsa da suka rune "Pls Wife" Ta k'ara turasa tana cigaba da kuka shagwab'a "Nidai Aa" Baice mata komai bah ya cigaba da abinda yake, kuka ta cigaba da rera masa a wajan kunnensa, chan dabara ta fad'o mata ta turesa tana cewa "Dan Allah ka bari, kaje kayi wanka" Ya d'ago jajayen idanunsa tare da shinshina Armpit d'insa "Ina tsami koh?" Ta d'anyi murmushi tana turo baki "Bafa haka nace bah, ni dai kaje kayi ka dawo" Ba musu ya mik'e rik'e da maransa yana cije lab'e "Ki jira dawowana" Ya fita daga d'akin tana tafiya a hankali, tana ganin ya fita tayi saurin mik'ewa ta d'aura towel ta kulle d'akin da key tana dariyar k'eta. A falo ya tarar da Mabrookah wacce tun shigowan su ta shigo side d'in ta zauna tana jiranshi, duk tayi tsuru tsuru ta rame ko saboda meye oho. Sam baima lura da itaba, tana ganinsa ta tashi da gudu ta fad'a jikinsa tare da fashewa da kuka "Ya Jamal ina kuka shiga? Kun barni ni kad...." Tureta yayi dasauri ta d'ago tana kallansa da Mamaki. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:19 AM] +234 706 272 2689: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 83 n 84 Tureta yayi dasauri ta d'ago tana kallansa da Mamaki "Karki kuskura ki k'ara tab'ani" Tsagaita kukan datake tana kallansa da mamaki. Ya nunata da yatsa "Kin bani mamaki Mabrookah, harda ke za'a had'a baki a cuceni" Ta fashe da kuka tana kallansa "Ni abinda kukamin banyi k'orafi ba saikai ne zakay..." Ya d'auketa da wani kyakyyawan mari, ta sake fashewa da kuka "Wallahi bazan yarda bah, kutafi ku barni a gida ni kad'ai sannan yanzu kazo kayita dukana" Ransa idan yayi dubu ya b'aci, d'akinsa ya nufa yana huci da alama ransa ya matuk'ar b'aci. Batsa batsa yaga d'akin kamar yanda yabarshi rannan. Ya k'arasa jiki a sanyaye ya soma tattara kayan wajan, tsaf ya gyara komai sannan ya shiga wanka. Ganin ya shige d'aki yasa Mabrookah fashewa da kuka ta sauka k'asa zuwa nata d'akin. Jamal bai fito ba sai dayaji ana kiraye kirayen sallahn Magrib, ya fita ya tafi masallaci, bai dawo ba saida akayi isha'i. Falon k'asa ya tarar da Mabrookah zaune taci kwalliya cikin atampha riga da skirt, kallo d'aya ya mata ya kauda kai. Idanunta ya ciko da kwalla ta mik'e dasauri tasha gabansa, rai b'ace yace "Matsa ki bani waje" Ta matso inda yake yyi saurin matsawa, ta sake matsowa ya k'ara had'e rai "Kinaso ki kaini bango Mabrookah, ki matsamin na wuce" Ta fashe da kuka ta tsugunna guiwa biyu a k'asa "Wallahi Ina sanka Ya Jamal, ban tab'a san wani a duniya ba inba kai bah, kaji tausayina" Ya d'aga mata hannu alamar dakatarwa "Kina sona kika bari aka had'a baki dake aka cutar dani? Menai muku a rayuwa Mabrookah" Ta sake fashewa da kuka "Ni ban gane abinda kake nufi bah, wallahi babu wanda na had'a baki dashi dan a maka wani abu. Ka yarda dani Ya Jamal" Kallanta ya tsaya yi na y'an mintina, batare da yace komai ba ya haura sama. Direct d'akin Ummy ya shiga, yana murd'awa yaji ya bud'e, mamaki ne ya kamasa dan d'azu yanaji sanda ta rufe da key. Kakarin Amanta yaji daga toilet ya k'arasa dasauri cikin toilet d'in ta rik'eta harta gama. Sannu ya dunga mata tana gyad'a masa kai tana hawaye. Laulayin Ummy ne ya dawo sabo, haka suka shafe kwana biyu kullum cikin amai da zazzab'i Cikin kwanakin sunyi zarya a asibiti, abubuwa ne suka taru suka masa yawa, ga Halinda Wife d'insa ke ciki, ga bak'in cikin abinda su Mami suka masa. Ga kuma Mabrookah wacce yanzu ya gama yarda batasan Plan d'in da su Mami sukayi bah, hasalima kullum saita tasashi a gaba tayi ta masa kuka na rashin Mami da Aunty Faty, daga shi har Ummy babu wanda ya iya fad'a masa abinda ya faru. Yau Sunday babu laifi Ummy tad'anji kwarin jikinta, da kanta ta tashi ta had'a musu breakfast, yana fitowa wanka wayansa ya soma ringing, ganin Numbern Ram yasa ya d'auka had'e da sallama, daga chan b'angaren Ram ya sanar dashi yana san ganinsa Shi da Ummy harda Mabrookah dan akwai tambayoyin dayakeso ya musu dan washe gari za'a shiga court. Jim Jamal yayi har Ram yayi tunanin baijishi bah, saida ya kira sunansa sannan ya sauke ajiyar zuciya yace "Ram Mabrookah batasan abinda ke faruwa bah, bansan ta yanda zan fad'a mata bah. And kuma akwai abinda nakeso ku sani" Ram yayi jim sannan yace "Ok to ka bari ina nan zuwa anjima sai muyi maganar gaba d'aya" "Tho" kawai yace ya kashe kiran. Cikin 'yan mintina ya gama shiryawa ya fito falo, dai dai lokacin Ummy ta fito daga kicin da Mugs a hannunta, amsa yayi dasauri "Haba Wife banace ki daina aiki bah, banaso ki wahalar min da baby nah" Tayi dariya tace "Banaso Daddyn Bbyn ya zauna da yunwa, kaga fah tun bayan faruwan abubuwan nan baka wani ci abincin kirki bah" Harya bud'e baki zaiyi magana, tasa yatsanta a lips d'insa "Shhhhh...!" Ta kama hannunsa har zuwa dinning d'in ta zaunar dashi kan kujera, babu surutu kayi breakfast kawai, har zata bud'e Warmern dake gabanta ta dakata tana kallansa "Na manta ban kira K'anwata bah" Yayi murmushi mai k'ara masa kyau "K'anwa!" Ya maimaita, ta hararesa da wasa "K'anwata mana ko ka manta nice ta farko" Dariya yad'anyi mai sauti sannan ya mik'e ya sauka zuwa d'akin Mabrookah, kan gadonta ya sameta ta kwanta ruf da ciki tana kuka a hankali, ya k'arasa dasauri ya d'agota dan yanzu tausayi take basa "Haba k'anwata kukan nan kuma na menene" Ta k'ankamesa ta sake fashewa da kuka "Kullum idan na kira wayan Mummy da Mami bana samu, hankalina yak'i kwanciya ji nake kamar wani abu ya faru dasu" Yad'anyi jim sannan ya d'ago kanta "Nasan inda suke" Da mamaki ta zaro idanunta da suka rune zuwa ja suka kumbura "Dan Allah dagaske ya Jamal" Ya gyad'a mata kai da d'an murmushi "Sosai mah, anma bazan fad'a miki ba sai kin hau sama munci abinci" Ta b'ata fuska a shagwab'e "Nidai banajin yunwa, dan Allah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82