Chapter 42
Chapter 42
"Yarinya tun d'azu tana d'aki tana murd'e murd'e kana chan tareda wannan maiyar" Harara yaketa wurga ma Mabrookah batareda yace komai bah. "Ina magana kayi banza dani, maza dauko makullin mota kazo ka kaita asibiti" Juyawa yayi har lokacin baiyi magana bah, dakinsa ya shiga ya d'au makulin mota ya fito. "Sai kazo ka kamata ku sauka k'asan" Ransa a b'ace ya k'araso inda Mabrookan ke zaune, saida ya take mata k'afa da gangan itako zafin dataji yasa ta saki ihu tareda matsar da k'afarta. Fizgota yayi ya d'agota suna tafe Mami na binsu a baya har suka sauka k'asa. Saida taga ya sakata mota sun fita sannan ta koma side d'inta tana dariya. Sunyi tafiya mai nisa sannan yayi parkinga a gefen titi ya d'au wayansa ya turama Wife d'insa text akan tayi hak'uri ya fita. Mabrookah ko sai cigaba da murd'e murd'e take. Zuciya tazo masa wuya ya fincikota tareda shak'e mata wuya "Ni zaki ma k'arya, wallahi idan baki daina murd'e murd'en nan ba saina b'abbalaki a wajan nan" Tari ta soma tana neman k'wacewa anma ta kasa, huci yake ransa b'ace "Abubuwanki sun fara isana Mabrookah, wallahi ki shiga taitayinki ina gab da datse igiyar auren dake tsakaninan dake" Kuka ta soma ta sa hannu yana k'okarin janye hannun daya shak'eta dashi "Wa..wayyo Zak..ka kasheniiii" Sakinta yayi ya jurata baya ta bige da murfin k'ofan. Kuka tasa tana sosa wajan data bige "Duk abinda kakemin ban tab'a cewa komai ba sai kai, yau watan mu uku anma baka tab'a kusantata bah, baka kulawa dani, baka damu da harkata bah" A harzuk'e ya juyo yana zazzare ido "Anya Mabrookah baki tab'a sanin namiji ba kuwa" Ihu ta saki tana kuka "Karuwa kake so ka cemin kenan, baka kira Ummy karuwa ba sai..." Marin dataji a fuskanta ne ya hanata k'arasa maganan datayi niya. Nunata yayi da yatsa, wannan karan takai k'ololuwa wajan b'ata masa rai "Matuk'ar a furucinki bazaki daina sako Ummy bah, haka nima bazan daina d'aura hannuna akanki bah" Kuka ta sake fashewa dashi tana dukan ko ina ta samu a cikin motan, harzuk'a yayi ya fito ya fizgota waje ya zagaya ya shiga ya tada motan yabar wajan. Kuka Mabrookah ta sake fashewa dashi, gashi bata fito da wayanta ba balle ta kira Mami, kuma hanyar motoci sai jefi jefi suke wucewa. Kuka take kamar ranta zai fita tanata bubuga k'afa a k'asa. Har yayi nisa sai kuma yaga rashin kyautawar sa na barinta a wajan, ko ba komai matarsa ce akwai igiyan aurensa a kanta. Dogon tsaki yaja ya juya ya koma, inda ya barta nan ya dawo ya sameta tanata kuka, bud'e kofan gaban motan yayi batare da yace komai bah. Dagudu ta shiga yaba motar wuta kamar zai tashi sama. Ikon Allah ne kawai ya kawosu gida, Fita tayi dasauri ta nufi part d'insu ta fad'a dakinta. Shima rai b'ace ya fito ya shiga, dakinsa ya nufa kai tsaye. Tunda aka bud'e gate d'in gidan Mami tazo bakin window tana kallansu, sosai ranta ya b'aci da abinda ta gani ta koma ta kwanta a fusace. Ummy najin motsin su tun sanda suka dawo, sam batayi gigin zuwa d'akinsa ba dan yanzu wani irin tsoronsa takeji. Dare ya tsala sosai wuraren k'arfe biyu da kwata, Jamal na kan katafaren gadonsa yaji Tim! Kamar k'aran dirowan abu. Tashi yayi zaune dasauri ya mik'e ya tsaya bakin window ya d'an d'aga labule yana hange. Wasu ya hango suna zagaye gidan dukansu sanye da bak'aken kaya fuskokin su duk a rufe, ga wasu manya manyan bindigogi dake hannunsu. A tsorace yakai dubansa wurin gate, masu gadi ya hango kan kujera an d'auresu da igiya bayan an rufe musu baki. A rud'e ya d'au wayansa ya soma neman layin Abba, bugu d'aya ya d'auka yana cewa "Jamal lafiya cikin wannan daran" A rud'e yace "Abbana 'yan fashi ne gasu nan sun zagaye gidan" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine kalmar da Abba ya fad'a yace "Ku natsu karku bud'e musu k'ofa" "Tho!" Jamal yace ya kashe kiran. D'akin Ummy Jamal ya nufa, bacci ya sameta take hankalinta kwance, Sunnanta ya kira a hankali duk da hankalinshi a tashe yake, motsawa tayi bayan ta bud'e ido "Wife tashi B'arayi ne a gidan namu yau" Ba shiri ta mik'e tana k'okarin kwalla ihu, saurin rufe mata baki yayi da hannunsa, kuka ta fashe dashi tana yarfe hannu. Shi kanshi baya cikin natsuwa, hannunta ya kama suka zauko k'asa zuwa d'akin Mabrookah, Jamal ne ya tasheta itama ta tashi a tsorace. Tsakiya suka sakashi suna kuka sosai dukansu cike da tsoro. Sam hankalinsa baya jikinsa yana chan wajan Iyayensa. A chan kuwa b'angaren Abba, Mami ya tayar ya fad'a mata, ba shiri ta mik'e dasauri tana muzurai cikeda tsoro, kan kace me sunyi anfani da wani secret key sun bud'e kofan side d'in. Nan Mami ta sake tsorata, Abba kuwa ba abinda ke fita daga bakinsa sai addua, duk wanda yazo masa yi yake kawai. Wajan su Shidda suka shigo d'akin, bindiga suka nunama Abba da Mami suka tasosu gama zuwa Main falon dake k'asa. Jamal dasu Ummy nachan hankalinsu tashe, bud'e kofan side d'insu suma akayi, Mabrookah ta saki Ihu zata gudu, d'aya daga cikinsu yace "Kina guduwa saina harbeki" Chak ta tsaya, Suka shishigo, Ummy ta makale Jamal tana cigaba da kuka, d'aya daga cikinsu yace "Hands Up" Dukansu suka d'aga hannu, tasasu suma sukayi har zuwa side d'in Abba, sai a nan suka lura ashe ba k'aramin yawa garesu bah, sun zagaye gidan kaf har side d'in masu aiki. Abba da Mami suka samu a Falon an sakasu sunyi kneeldown, an d'ad'aura musu bindiga akai. Suka su Jamal aka sakasu sukayi irin nasu Abba, Ogan ciki dake hakince kan kujera rik'e da AK47 ya kalli Ummy Yace "Woaw! Anma kinada kyan diri" Sai a lokacin Jamal ya kalli kayan dake jikin Ummyn, Riga da wando ne iya guiwa mai santsi ya matseta duk ya mammane mata a jiki. Hakan ne ya k'ara fito da suranta a fili, Ran Jamal ya b'aci, Ogan ya cigaba da cewa "Lallai Alhaji Surajo, Ashe haka kakeda zuk'a zuk'an 'yan mata. Lallai zan kwashi ganima kafin natafi" Abba yayi saurin cewa "Dan Allah ku fad'i abinda kukeso mu baki, Naira, Dollars ko Cheque" Wani dariya Ogan ya saki ta sosa gefen fuskansa da bindigar dake hannunsa "Ni duk ba wannan ya kawoni bah" "To me ya kawo ku" cewar Jamal yana huci Oga ya maida dubansa ga Jamal yace "Ran d'aya daga cikinku mukazo d'auka" Nan fa Abba da Jamal sukayi tsuru tsuru, Ummy da Mabrookah da Mami kuma suka fashe da kuka. Oga ya nuna Ummy yace "Ke tashi, Bari na fara morewa tukun sai nayi abinda ya kawoni" Ummy ta fashe da kuka tana kallan Jamal tareda langwab'ar dakai. A zuciye ya mik'e yace "Wallahi kada ka sake ka tab'amin matata" D'aya daga cikinsu ya d'aga Ummyn tsaye tana kuka sosai, a zuciye Jamal yayi kansu bai ankara ba yaji saukan abu a kansa, ba shiri ya fad'i wajan tare da dafe kansa ya saki k'ara sosai. Abba yace "Dan Allah karku kashe min Iyalina, ku fad'amin me kukeso na baku" Mami kuwa sai Jamal take dake tsugunne a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82