Chapter 27
Chapter 27
layin Ramadhan anma switch off. Yana nan d'aki har Abba ya dawo, direct side d'inshi ya nufa yayi sa'a ya sameshi shi kad'ai, zama yayi ya soma ma Abban bayani, bai b'oye masa san da yakema Ummyn bah. Sosai Abba yaji dad'i duk da shima hankalinshi ya tashi dajin maganan auren da akeso ama Ummyn. Washe gari da wuri Abba ya nemi aminan sa suka tafi gidansu Ummyn nema ma Jamal aurenta. Baba Sallau da Baba Tanko fafur suka k'i yarda, duk magiyan da suka musu suka ce sam, haka suka hak'ura suka dawo gida a sanyaye. Ummy batasan wainar da ake toyawa ba dan dama bata sanar da Jamal d'in abinda Mama tace ta fad'amai ba, kawai da ta fad'amai abinda su Baba Sallau d'in suka cene. Washe gari ranar bakwai, Ummy kuka take kamar mai hauka, Mama itama na tayata, Alumma ne cike a k'ofar gidan ana addu'an bakwai. Da gudu ya shigo cikin layin kamar zai tashi sama, yana parking a ya fito aka shafa fatihar k'arshe na d'aurin auren Ummyn. Hannu ya d'aura aka ya fad'i guyawu biyu a k'asa tareda fashewa da kuka. *Idan banga dogon comment ba, bazan cigaba ba ehe!* Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Oh! Fans duk saurin ungwazo ma ta bari dai a haihu koh! Naga comment d'inku, masu addu'a ina godiya, masu k'orafi ma na gode, masu zagi suma na gode dan bazance ban gode bah.* _Aysha Humaira (Aunty Nurse) ina tayaki murnar zagayo war ranar haihuwarki. Allah ubangiji ya k'aro shekaru masu albarka, ya nuna min aurenki mu kwaso shoki Lol_ Wannan shafin sadaukarwa ce gareki K'awar arzik'i Page 31 Hannu ya d'aura aka ya fad'i guyawu biyu a k'asa tareda fashewa da kuka. Ganin kukan nasa ba ci yasa ya mik'e ya shiga cikin gida kai tsaye, Inna dake tsakar gida tana shara ta d'ago dan taga mai shigo mata gida ba sallama, ba shiri tsintsiyar hannunta ya fad'i ta dafe k'irji tana sallati "Bi...Bilal! Kai nake gani ko gizo kakemin" Ya soma takowa a hankali yana share hawayen fuskansa, "Ni ne Innata" Ya mik'a mata hannunshi "Tab'ani kiji" Cikeda tsoro ta mik'a hannunta ta tab'a shi, ba shiri ta fashe da kuka, shima kukan ya soma ya jata suka zauna kan tabarman dake tsakar gidan "Bilal ina ka shiga duk lokacin nan, meyasa ka tafi ka barmu bayan kasan bamuda kowa daga Allah sai kuma kai" Kuka ya sake fashewa dashi kamar k'aramin yaro tareda rik'o hannun Innan, Bahar ne ya shigo gidan yana k'walawa Inna k'ira, ba shiri ya koma waje a guje yana Ihu, Inna ta soma magana tana cewa "Munyi ta jiranka ba wani labari, har tsawon sati uku, sannan Bahar da Ummy suka je nemanka inda kuke aiki, a nan muka samu labarin kunyi hatsari kun mutu" Ya sake kama hannun Innan yace "Tabbas munyi hatsari, saidai kafin motar ta kama da wuta Allah ya aiko mutane inda suka ciro ni ganin ina motsi, wani Alhaji ne ya d'auke ni ya tafi dani abuja, kasancewar ba mazaunin k'asan nan baneh yasa lokacin komawar sa nayi ya d'aukeni ya tafi dani Egypt, k'asar dayake kuma a lokacin bana cikin haiyaci na dan ban farfad'o bah" Ya sake sharb'e hawayen idonsa yace "Na d'au watani bansan inda kaina yake bah sai daga baya na dawo cikin hankalina. Alhajin da matarsa sunyi d'awainiya dani sosai har zuwa wani lokaci. Dawowan mu k'asar kenan shekaran jiya shine na taho gida. Inna ba abinda take sai sharb'ar hawaye "Allah sarki mutanen kirki" Duk abinda suke tattauna wa Bahar na jinsu wanda ke bakin zaure yana lek'ensu. Bayan yaji bayanin sa ya shigo ya zauna kusada yayan nasa tareda rungumeshi "Yaya munyi kewarka sosai, badan Ummy data fara aiki tana taimaka mana ba da bansan halin da zamu shiga ba" "Aiki!?" Bilal ya maimaita yana kallan Bahar, Inna tace "Kwarai kuwa" Nan ta soma basa labarin abinda tasani har zuwa yau da ake sadakar bakwai na Baba, kuma ranar da aka d'aura auren Ummyn. Hawaye ne suka gangaro masa na tausayin halin daya bar 'yan uwansa da kuma Ummyn. Baice musu komai ba saima mik'ewa dayayi ya fita, gidansu Ummyn ya shiga kai tsaye, mutane ya gani a ciki, bin gidan ya soma yi da kallo ganin yanda aka gyara shi tareda k'awata shi sosai. Falon ya shiga da sallama ya hango Mama zaune a k'asa gefen kujera, ta d'aura kan Ummy bisa cinyarta wacce da alama kuka take. Jiki a sanyaye ya k'araso ya tsugunna gabansu "Sannu Mama" Muryan da Ummy taji ne yasa ta d'ago a razane suka had'a ido da Bilal, ba shiri ta fashe da wani sabon kukan, Mama ko tsoro taji ta d'an matsa "Bilal! Kaine" "Ni ne Mama, ban mutu ba" Ummy ta mik'e dasauri tabar d'akin tana cigaba da kuka, zaure ta nufa yayi saurin fitowa ya kamo gefen hijabinta dasauri "Ina zaki Hrt, pls ki tsaya ki saurareni" Cikin kuka ta d'ago idanunta tana cewa "Ina katafi Ya Bilal, ina kaje ka barni, meyasa ka tafi baka waiwayo ni bah. Dama nasan baka mutu ba dan naji a jikina." Ta chakume shi tana wani irin kuka mai cin rai "Kai kad'ai nakeso Ya Bilal, kai nakeso na aura. Gashi kasa an aura min wanda banaso. Meyasa Ya Bilal" Shima hawayen ya soma "Nasan nayi kuskure Hrt, anma yakamata ki tsaya ki fahimceni kafin ki yanke hukunci" A hankali ta zame hannu wanta daga rik'on data masa tana kuka. Labarin abinda ya faru dashi ya soma bata tiryan tiryan, sassauta kukan datake tayi "Yannin babana sun aura min wani wanda banaso, wanda banma tab'a ganinsa bah" Gabansa ya fad'i, ya d'ago rinannun idanunsa yana kallanta, Baba Sallau ne ya shigo zauren, ganin Ummy tsaye da wani wanda bai sani ba yasa ya soma fad'a "Ke Ummy, yanzu saboda iskanci da rashin hankali a d'aura miki aure ki tsaya kina kula wani" Ya daka mata wata uwar tsawa "Maza bar nan!" A guje ta shiga cikin gida tana kuka, ya juyo ga Bilal dake tsaye kamar gunki "Kai kuma zaka bar nan ko sai na bugeka" Jiki a sanyaye ya bar zauren ya koma gida. D'akin Innansa ya shiga ya soma kuka wui wui, dan harga Allah bazai iya rayuwa ba Ummy bah. ****** Bayan an gama d'aurin aure Abba ya baro wajan ya dawo gida, Jamal ya tarar a falonsa kishingid'e kan kujera idanunsa a lumshe, har ya nemi guri ya zauna kusada shi bai sani bah. Gyaran murya Abban yayi anma shiru, kai ya girgiza ya d'an buga hannunsa, bud'e ido yayi ganin Abba yasa ya mik'e zaune dasauri yana kallanshi "Jamal tunanin me kake?" Yayi saurin girgiza kai tareda k'ago murmushi yace "Bakomai Abba, bacci nakeyi" Murmushi Abba yayi irin tasu ta manya, ya gyara zama tareda cire babban rigan dake jikinsa "Meya hanaka zuwa addu'an bakwai" Ya sosa k'eya yana kame kame "Ahan kai nake sauraro" "Ummm..mmm Dama Ramadhan nayi ta jira muje tare kuma baizo bah" Murmushi Abban ya sakeyi, "Bakomai ai tunda ni naje, na wakilce kah. Yanzu abinda nakeso dakai shine ka shirya dan nan da sati d'aya za'a kawo maka matarka" Da mamaki Jamal ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82