Chapter 17
Chapter 17
Ramadhan yayi shida Laurat, shi kuma gogan murmushi kawai yayi yana cigaba da kallan Ummyn. Ramadhan yace "Ka mata uzuri bata sami baneh, kuma kaga tasamu buguwa akai kila ta samu matsala neh" Maganan Ramadhan ya sosa mata zuciya, wato kenan ya d'auketa mahaukaciya ma kenan, idanunta cikeda kwalla ta d'ago tana kallan Jamal "Ni ba mahaukaciya bace da hankalina" Ta fashe da kuka tace "Kuma ai bansan ka warke baneh shiyasa ka bani tsoro. Ta sake d'agowa tana kallan Jamal wanda shima ita ya zubama ido "Ni ban kiraka da wannan sunanba sai ku ne zaku kirani da mahaukaciya" "No bah haka baneh baki fahimceni baneh, I'm sorry ba haka nake nufi ba believe me" Cewar Ramadhan cikin tattausan murya. "Nagode Laurat, har dake aka had'u ana zagina bakomai" Ta kwanta kan gadon ta janyo blanket ta rufe jikinta har kai tana cigaba da kuka. Tab'o Jamal Ramadhan yayi "Say something mana" Guntun tsaki yaja ya mik'e ya kama hannun Ramadhan d'in suka fito daga d'akin. Jamal ya saki Hannunshi yana cewa "Kaifa Matsalata dakai kenan bakin ka baida control" "Eh naji bakina ba control, kai kuma idonka da shegen gulma, tun dazu kaketa kallan musu 'ya" Dukan wasa Jamal ya kaimai yana dariya "Kai kaidai Ram ta shiga uku" Laurat ta fito daga d'akin Ramadhan ya tab'o Jamal suka juyo suna kallanta "Dama inaso ne naje gida na d'auko mata kayan da zata chanza" Ramadhan yace "Taci abinci neh" ta girgiza kai alamar A'a "Tak'i taci tayi fushi sai kuka take" Shiru ne ya biyo baya, Ramadhan yace "Yanzu muje ki d'auko kayan mu dawo" Gaba tayi Ramadhan ya tab'o Jamal yana y'ar dariya "Na barka da ita ka lallasheta kasan kai na mata neh" Bai jira mai Jamal d'in zaice ba yabar wajan dasauri yana masa dariya. Jim yayi yana tunanin yanda zai shiga d'akin dan shifa bai iya magana da mace ba dan shi a rayuwarsa ko budurwa bashida. Handle d'in ya murd'a ya shiga da sallama ciki ciki, zaune ya saketa ta jingina da pillow idanunta a lumshe, kan kujeran gabanta ya zauna yayi shiru yana kallanta a hankali yace "Ummy" Batace komai bah kuma bata bud'e idon ba saima turo baki datayi ta juya kai gefe, murmushi yayi mai sauti yana shafa sajen fuskansa "Kiyi hak'uri da abinda Ram ya fad'a dazu, ba ya fad'a baneh dan ranki ya b'aci" Shiru ne ya biyo baya na y'an mintina ya cigaba da cewa "And kiyi hak'uri akan abinda ya faru jiya, i wasnt my self har naji miki wannan raunin. And ina godiya da lokacinki da k'arfinki da kikayi wasting wajan lura dani" A hankali ta bud'e ido tace "Bana buk'atar godiyanka" Ya saki murmushi mai sauti yace "Ok! Ok!! But kiyi hak'uri pls akan abinda ya faru" "Na hak'ura" ta bashi amsa a takaice. Shiru ya sakeyi har lokacin idanunshi na kanta, kujeransa ya matso dashi kusada ita sosai yace "Dan Allah na miki wata tambaya mana" "Ina jinka" Ya shafa suman kanshi yace "Anma dai lokacin da banda lapia baki tab'a min wanka ba koh" Kuji min Jamal d'in nan fah Fans...Haha Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:20 PM] +234 703 981 8283: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 21 "Anma dai lokacin da banda Lapia baki tab'a min wanka ba koh" Maganansa sosai ya bata d'ariya, dakyar tayi k'okarin dakewa tana kallansa k'asa k'asa "Wanka na nawa kuma" Ta tab'e baki tace "K'arshen magana ma jiya ni na maka wanka" Mutuwar zaune yayi yana kallanta fuska a had'e, anma dai an gama cutar shi wallahi. Dogon tsaki yaja ya mik'e yana hararanta rai b'ace yana nuna kanshi, har ya bud'e baki zaiyi magana Mami ta turo k'ofa ta shigo, ya juyo dasauri yana kallanta har lokacin fuskanshi a had'e "Mami yanzu abinda akamin an kyauta knan?" Da mamaki Mami ta kalleshi ta juya ga Ummy tana kallanta "Me kuma aka maka?" "A rasa mai min wanka sanda banda lapia sai wannan?" Ya nuna Ummy fuskan nan nasa a had'e Mami da Ummy suka kyalkyale da dariya a tare "Ai Ummy tayi d'awainiya dakai sosai, wankan ka, wankin ka, kai hatta toilet idan kayi ita..." "Haba Mami! Habaaaaa" A fusace yabar d'akin yayi waje, Mami ta sake kyalkyalewa da dariya, "Allah ya shiryeka Jamal" Itama Ummyn dariya tayi, Mami ta mata sannu tana cewa "Nace ma dr ya sallameki ki koma gida sai a rink'a zuwa ana dubaki achan" Godiya tama Mamin, su Ramadhan suka shigo shida Laurat "Mami meh akaima Jamal ne naganshi yanata kumbure kumbure a waje" cewar Ramadhan. Mami ce ta fad'amai abinda ya faru, yayi dariya yana kallan Ummy "Oh kin rama knan" Harara ta wurga mai ta kauda kai gefe. Likitan da kansa ya kawo musu takadar sallama bayan ya k'ara dubata tareda rubuta mata magunguna. Laurat da Ramadhan suka kwaso kayan da aka kakkawo, Mami ta rik'o Ummy suka fito. A haraban asibitin suka had'u da Jamal sai cika yake yana batsewa, kallo d'aya Ummy tamai tayi dariya, harara ya zafga mata tareda kauda kai. Suna isa ya d'au wayan Ramadhan ya kira Layin Abba, saida ya tambayesa ya fad'a masa gaskiya sannan hankalinshi ya kwanta. Kiran ya kashe tareda sauke ajiyar zuciya "Lallai ma Yarinyan nan" Yayi k'wafa yace "Kinci bashi" K'in saukowa yayi k'asa shi a dole yayi fushi, yayi zamanshi a d'aki abinshi yanata bacci. Washe gari da safe Ramadhan ya koma Kaduna, hakan baima Jamal dad'i bah dan shi ke d'ebe masa kewa sbda har yanzu Abba yak'i yarda ya fita zuwa wani guri shi kad'ai. Ummy na zaune a d'akinta, duk hankalinta nakan Iyayenta gashi har weekend yazo ya wuce bataje ba kuma tasan suna chan hankalinsu tashe dan idan har zata jima takan fad'a musu. Laurat dake gefenta ta d'ibo abinci a plate, shinkafa da miyan naman rago sai salad, d'iba tayi takaima Ummyn baki dan bata iya cin abincin da kanta, ta kauda kai gefe idanunta cikeda kwalla "Ummy ci mana, tun safe fa Bakici abincin kirki bah" "Bazan iya ci bah, bansan halinda Iyayena ke ciki bah yanzu nasan hankalinsu nachan a tashe" "Haba ki kwantar da hankalinki, ai Mami tace yau ko gobe za'a kwance d'aurin kanki. Kinga hannu ma bazai jima ha knan" Gigiza kai kawai Ummyn tayi, dakyar Laurat ta lallab'ata tad'anci kad'an sannan ta koma bakin aikinta ta barta ta huta. Harta kwanta aka turo k'ofan d'akin, bata d'agoba dan a tunaninta Laurat ce. Kujera akaja aka zauna har lokacin ba'ayi magana bah. Jin shirun yayi yawa yasa ta d'ago suka had'a ido da Jamal, ya harareta yana cewa "Ke baki Iya gaisuwa bah" Fuska ta yatsine ta kauda kai gefe tace "Ina wuni" "Dah ban wuni ba zaki ganni" "Oho kai za'a tambaya" Buge mata baki yayi tasa hannuta na dama ta rik'e bakin tareda fashewa da kuka "Allah ya..." Rank'washin ta yayi a kai ta saki kuka tana sosa inda ya rank'washetan. Fuskansa ya matso dashi kusada nata yana kallan k'wayar idonta "I'm a free guy, kowa nawa neh, but banasan rashin kunya" Yayi murmushi yasa hannu ya shafa gefen fuskanta "Na lura bakida kunya, kuma gashi ni bansan rashin kunya" Ya saki murmushi mai sauti "From
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82