Chapter 58
Chapter 58
tab'a bashi ajiya. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 68 Ba shiri ya mik'e tunawa da Jakar da Abba ya tab'a bashi ajiya. Yana tafe yana ganin jiri har ya k'arasa side d'insu, da kyar ya iya hawa saman har ya k'arasa d'akinsa. Direct wajan wardrobe d'in yayi ya bud'e ya ciro Jakan. Kan gado ya zauna ba b'ata lokaci yaja zip d'in ya bud'e, Tulin takardu ya gani ciki, ya soma fito da takardun yana ajewa gefe batare da ya duba bah. Wani k'aton diary ya gani a k'asan jakan, ya d'ago ya duba ya mayar ya aje. Idanunsa ne ya cika da kwalla ganin babu kud'i a cikin jakan. Ya dafe kansa da duka hannayensa yana kuka ahankali, ya dad'e a haka sannan ya mik'e a sanyaye. Chak ya tsaya ya juyo yana kallan diaryn dake cikin Jakan. Zuciyarsa ce ta dunga ingizasa ya duba diaryn, har lokacin yana tsaye bai daina kallon jakan bah. Ya koma ya zauna tare da d'aukan diaryn ya bud'e a hankali. Abinda ya fara cin karo dashi shine " *I'M SO SORRY JAMALUDEEN* " Gabansa yayi mummunan fad'uwa, ya sake bud'e page na gaba nan yaga dogon rubutu kamar haka. _Surajo Kadiri shine cikakken sunana, ni d'an asalin K'asar Niger ne. Na taso cikin matsi da wahalar rayuwa saboda mahaifana duk sun rasu, saboda hakan yasa na fara almajiranci har zuwa lokacin da wani Alhaji ya d'aukeni ya maidani gidansa ina masa aiki._ _Dad'i na rayuwa babu wanda banaji a gidan dan ya d'aukeni kamar d'ansa shida matarsa dan bai tab'a haihuwa bah. Nayi primary sannan na zarce secondry daga nan ya sakani a jami'a. Ina ajina na biyu a jami'a Allah ya masa rasuwa, bayan ya rasuwansa da wata biyu matarsa ta gaza rik'eni dole na bar gidan na koma sana'ar hannu dan taimakon kaina akan karatuna._ _Da wahala da matsi na rayuwa na samu na kammala karatuna. A nan Allah ya had'ani da matata Jamila, inda mukayi auren soyaiya muna zaune lafiya. Rashi yasa dole muka tattara muka komo Nigeria dan muyi cirani mu koma._ Hawaye suka gangaro daga idon Jamal jin irin wahalan da Abbansa yasha a rayuwa. Ya cigaba da karantawa kamar haka: *12 August 1990* _Ranar da muka iso Nigeria bamu sauka ko ina ba sai k'asar zaria. Inda mai motanmu ya saukemu bakin wani masallaci a cikin zaria city, a nan muka zauna har akayi sallahn Isha'i, Limamin masallacin ya nema mana taimako muka d'an samu 'yan kudi muka sayi abinci. Watan gaririya muka soma cikin anguwan da muke gashi dare nata yi bamu samu wajan saka hak'arkarin bah. Kwatsam......_ Wayan Jamal ne ya soma ruri ya d'auka ya duba dasauri, sunan Mifzal ya gani a screen d'in ya d'auka a sanyaye ya kara a kunnensa "Kana ina neh Jamal ka fito mun samu wani information" Ai ba shiri yayi wurgi da diaryn hannunsa ya fito dasauri, a haraban gidan ya samesu tsaitsaye, ya k'arasa inda Mifzal ke tsaye yana waya yace "Ya ake ciki pls fad'amin" Yanda yake maganan cikin k'osawa yasa Mifzal d'an bubbuga masa kafad'a "Come down Friend! Yanzu muka samu information d'in Alhaji Ameenu da Bilal suna cikin garin Zaria, saidai babban takaicin na shine bamu gane location d'in da akayi wayan nan ba d'azu" "I'm very sure indai yana Zaria to zaije gida wajan Family d'insa" cewar Jamal Mifzal yace "Yes u're Right, wanan shine hanya mafi sauk'i da zamu bi dan kamasa" A tare suka fita da rakiyar wasu 'yan sanda, suna cikin Tafiya aka k'ara kiran Jamal da wani numbern, baiyi wata wata ba ya d'auka tare da karawa a kunnensa "Na lura baka damu da Matar nan taka bah, To bari kaji mun baka daga nan zuwa gobe, idan baka turo mana k'udin nan ba, zamu maka kwatancen inda zaka zo ka d'auki gawar matarka" "No! Dan Allah kuyi hak'uri karku kashemin matata, Wallahi zan turo muku k....." Dif suka kashe wayan, ya jinginar da kansa a seat d'in motan yana hawaye a hankali, Mifzal dai baice komai ba dan yaji duk abinda sukace ma Jamal d'in. "Why!" "Why Bilal, meyasa kakesan tarwatsa rayuwata? Meyasa kakesan cutar min da matata. This Battle bana Ummy bane nida kai yakamata muyi" Ya sauke kansa k'asa ya fashe da kuka. Mifzal kasa cewa komai yayi, sai kallan titi dayake yana driving a hankali ransa a jagule. Police station d'inda case d'in yake suka koma, suka kwashi 'yansanda suka shiga cikin zaria city. Lab'ewa sukayi wurare daban daban, Jamal da Mifzal suna xaune cikin mota chan nesa da gidansu Bilal d'in har bayan Isha'i suna wajan ko zasu kanshi. Wuraren k'arfe tara har sun cire rai sukaga wani Jeep bak'i yayi parking a k'ofar gidan, Bilal ne ya fito ya zagaya ya bud'e ma Alhajin ya fito shima suka shiga cikin gidan. Mifzal yayi ma sauran 'yan sandan signal, suka zagaye gidan gaba d'aya, Sun d'an jima sannan suka fito, Ram Mifzal yama Bilal, daya daga cikin 'yan sandan ya kama Alhajin, Jamal na ganin Haka ya fito daga mota dasauri ta k'araso inda Bilal d'in yake tsaye ya chakume mai kwala "Ina kakai min Matata" Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 10:54 AM] Ayshaaaaaa: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 69 n 70 Mifzal ya kama Bilal, d'aya daga cikin 'yan sandan kuma ya kama Alhajin, Jamal na ganin haka ya fito daga mota dasauri ya k'araso inda Bilal d'in yake tsaye ya chakume mai kwala "Ina kakai min Matata" Duk da yanda Bilal d'in ya rud'e hakan bai hanasa kallan Jamal da raini "Ka bani ajiyanta neh?" Wani wawan naushi Jamal yakai mai har saida hancinsa ya fashe, idanunsa sunyi ja sosai ya sake kama kwalar shi "Ina kakai min matata nace, ka fito min da ita" Wasu 'yansanda sukayi saurin janye Jamal dakyar, cikin motan 'yansanda aka sakasu dakyar Mifzal yaja Jamal ya sakashi cikin mota suka bi bayan motan 'yansandan. Suna isa police station kamin Mifzal ya gyara parking Jamal ya fito hat saida ya kusan fad'uwa. Station d'in ya shiga bai ko kalli inda yansandan suke ba ya k'arasa bakin canther inda su Bilal ke zaune a k'asa ya sake chakume kwallarsa ya mik'ar dashi tsaye "Bilal were is my Wife? Ina kakai min Ummy? Meyasa ka kashe min Matata" Mifzal ya k'araso ya janye Jamal d'in "Come down friend" Gaba d'aya Jamal ya fita haiyacinsa idanunsa suna kad'a sunyi ja saboda b'acin rai. Alhaji Ameenu yace "Wannan wane iri abu neh haka? Kamar ni a kamani a kawo ni police station me na muku" Har Jamal ya bud'e baki zai mayar masa Mifzal ya janyesa dasauri ya fita dashi, mota ya turasa sai turjewa yake shima ya shiga yaja suka bar station d'in. Gida ya kaisa har gaban Mami ya tsaya ya kwantar musu da hankali ya tafi. Babu yanda Mami batayi da Jamal ba akan yaci abinci yak'i, sai kuka daya soma Mabrookah na tayashi. Ya mik'e dakyar ya koma side d'in Abba ya fad'a kan gado ya kwanta tare da runtse ido. Wayansa yayi k'ara yayi saurin d'auka, bak'uwar Number ya gani ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82