Chapter 65
Chapter 65
suka bisa a baya. Ummy na ganin haka ta rarrafo ta dawo inda Jamal d'in ke tsugunne ta rungumesa, murya chan k'asa yace "Kwance ni Wife" A tsorace ta kalleshi ya gyad'a mata kai, batare da b'ata lokaci ba ta soma kwance sa, hannun ta kwance dakyar sannan ya kwance k'afan da kansa. Hannayensa ya bud'e mata yana kallanta, dasauri ta fad'a jikinsa tana kuka. Ya lumshe ido yana shafa suman kanta da duk ya b'aci da k'asa "I'm Sorry Wife" K'ofar d'akin aka banko, suka d'ago suna kallan k'ofan, ba shiri suka mik'e dukansu suna bin k'ofar da kallo. Cikin takun k'asaita ta k'araso cikin d'akin Oga da yaransa na mara mata baya, cikin tashin hankali Jamal yace "Au..Aunty Faty!" Dariya tayi mai sauti sannan ta juya tana kallan bakin k'ofan, Mami ya gani sanye da bak'in dogon riga tasha No respect a fuska tana taunar chewing gum. Suma neh kawai Jamal baiyi bah, idanunsa kuwa kamar zasu fad'o saboda firgici. Ta k'araso gabansa ta tsaya tana kallansa da murmushi "Kana Mamaki koh, sai dai ba abin mamaki baneh dan wannan kad'an kenan daga aikin da mutum kan iyayi" Kuka Jamal ya fashe dashi tana cigaba da kallanta "Meyasa kikayi Haka Mami? Mena miki? Me Abbana ya miki" Ta fashe da wani irin dariya tace "Ban tab'a san Mahaifinka bah, haka kai. Ni nan daka gani na auri Mahaifinka neh kawai dan dukiyarsa. Ganin sanda yake nuna maka yasa abin ya soma damuna shine nasa aka tura maka aljanu dan su hanaka jin dadi ko soyaiyar dake tsakanin ku zai ragu" Ummy sai rarraba ido take cike da mamaki haka jikinta sai rawa yake jin maganganun dake fita daga bakin Mamin. Aunty Faty ta karb'e da cewa "Mun dad'e muna san kawar dakai dan muci dukiyar Mahaifinka saidai kuma hakan bazai yuwu bah in ba mun fara kawar da mahaifin naka bah" Ba shiri Ummy ta sulale k'asa guiwayu biyu ta fashe da kuka jin maganar da Aunty Faty keyi, haka shima Jamal kukan yake daga tsaye yana kallansu da tsananin firgita. Rai b'ace Mami ta nuna Ummy dake tsugunne tana sharb'ar kuka "Tun danake a duniya ban taba tsanar wani kamar yanda na tsaneki bah, dan ke kika fara rusa min plan d'ina. Ban tab'a tunanin kawo ki zai shafi abinda nasa agaba bah." Wani zuciya ne ya ciyo Jamal yayi kan Aunty Faty dasauri Yaran Ogan suka rik'esa yanata k'okarin kwacewa yana kuka "Kun cuceni Mami bazan tab'a yafemuku kashemin mahaifi da kukayi ba da kuma cutar dani da matata da kukayi" Mami da Aunty Faty suka kyalkyalle da dariya, wasu documents ta d'auko cikin wani envelop tare da biro tana cewa "Gidaje guda uku a cikin garin Abuja wanda kowanne yakai darajar Million Ashirin da biyar, Filaye Guda biyar a garin kaduna da kuma gidan gona dake garin Shika. Hannu kawai nakeso kasamin a nan dan na mallaki ab..." Yayi saurin katseta da cewa "Bazan sa ba ko kasheni zakuyi bazan sa bah" Ummy ta sake fashewa da kuka tana kallansu, Mami ta kyalkyale da dariya tana mik'a masa takardan "Kasa min hannu tun muna shiri nida kai" Rai b'ace yace "Bazan sa bah" Ogan ta kalla, yama yaransa alama, duka suka soma kaima Jamal d'in tako ina yanata ihu. Ummy sai kuka take tana daga gefe dan wasu cikin yaran sun zagaye tah. Mami ta tsayar dasu sannan ta mik'a masa takardan "Jamaludeen kasa min hannu a takardan nan" Ya d'ago fuskanshi dake zubar da jini yana kallanta "Bazan sa bah" Aunty Faty tace "Bai horu baneh dakyau har yanzu" Sanda Mami ta d'auka dake gefenta ta matso inda Ummy ke zaune tana kallanta, Yaran suka d'agata tsaye tanata san kwacewa tana kuka. Duka Mamin takai Ma Ummy a ciki da k'arfi, wani k'ara ta saki ta sulale wayan. Jamal ya saki wani irin k'ara ya fizge daga rik'on da suka masa ya k'arasa wajan da Ummyn ke kwance yana kuka. Yawo Mifzal da sauran tawagar su suketayi a cikin k'auyen tare da yima mazauna k'auyan tambayoyi anma ba wani labari. Har sun cire rai zasu koma suka hango motar Mami ta wuce a guje. Dasauri Mifzal yayi reverse yama sauran 'yan sandan Alama akan su dakata, binta ya soma shida Ram a baya ta yanda bazasu san binsu ake bah. Tafiya sukayi sosai, tayi wata kwana wata babbar mota ta fito itama daga kwanar dole suka tsaya har saida motar ta wuce sannan suka suka shiga. Abin haushi basu ga motarta bah. Mifzal ya daki steiring motan yana tsaki. Parking yayi gefen Hanya Ram ya fito yana duduba wajan, shima Mifzal ya fito, shedan tayan motan Ram ya gani ya nunama Mifzal, dasauri suka soma bin shedan suna ta tafiya a hankali suna cigaba da bi. Sauran 'yan sandan yama waya tare da musu kwatancen inda suke suma suka biyo bayan motar Mifzal d'in. Mami ta saki Lallausan Murmushi tana cewa "Idan baka samin hannu bah, zan kashe Ummy na kashe abinda ke cikinta" Cikin wani irin kuka yace "Me na miki a rayuwa Mami? Kefa Uwace a gareni, kinyi min komai a rayuwa kin bani tarbiya, ban chanchanci haka daga gareki bah." Ta saki dariya tace "Ni ba Uwarka bace, ban tab'a sanka bah Jamal. Duk abinda kaga inayi yana cikin Plan d'ina neh. Da kuma ganin idon mahaifinka" Ta mik'a masa takardan "Karb'a kasa min hannu" Ya girgiza kai tare da maida dubansa ga Ummy dake kwance bata numfashi, kanta ya d'aga ya d'aura kan cinyarsa yana kuka sosai. Hannu ta mik'ama Oga ya saka mata bindiga, ta saita Ummyn dashi rai b'ace tace "Ko ka Sa min hannu ko na kashe Ummy" Yasake rushewa da kuka, he has no choice ya amsa takardan yana kuka ya soma signing hawaye na d'iga jikin Papern. Yana gamawa ya mik'a mata ta amsa ta duba sannan ta maida dubanta ga Oga. "Ya cika aikinsa sai kuma ku cika naku" Oga ya saki dariya ya amsa bindigan daga hannunta yana cewa "An gama ranki ya dad'e yau wasu zasuyi kwanan lahira" K'ofar d'akin aka banko a tsorace duka suke bin k'ofar da kallo, 'yan sanda ne sukayi ta shigowa kowannen su da bindiga a hannunsa, Mami ta saki salati haka Aunty Faty suna kallan juna. Mifzal da Ram suka shigo a tare "Drop ur Weapons" cewar Mifzal, ba musu duka yaran Ogan suka aje Bindigogin su. Ram ya k'arasa inda Jamal ke tsugunne yana dubansu da mamaki. Rai b'ace Mifzal yace "Mami kinji kunya" Ta had'e girar sama data k'asa, d'aya daga cikin 'yan sandan yace "Hands Up every Body" Dukansu suka d'aga hannu sama, cikin kuka Jamal yace "Ram Ummyna bata numfashi" Ram ya d'auketa chak, jini Jamal ya gani a inda aka d'agata ya saki k'ara shima ya fadi a wajan. Iya rud'ewa Ram da Mifzal sun rud'e, Dasauri Ram yakai Ummyn Mota sannan ya dawo shida wani d'an sanda suka d'au Jamal d'in. Mami ta fizge Bindiga daga hannun Oga ta saita Jamal d'in zata harbasa taji saukan harsashi a k'afarta. Ta saki Ihu ta fad'i wajan tana kuka dafe da k'afarta, handcop duka akasa musu aka ingiza k'eyarsu, ita kuma wasu 'yan sanda suka d'aukota aka sakata a bayan mota sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82