Chapter 26
Chapter 26
baisa yayi nadama akan abinda yayi bah. Bayan kwana biyu ya sake komawa gidansu Ummy, wannan karan ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwarsa, maganan ranan ya sake d'auko mata, nan tayi kicin kicin darai "Na fad'a maka bazan iya aurenka ba Ya Jamal, yakamata ka cire wannan maganan a ranka indai baso kake ka b'ata shirin dake tsakanin mu bah" Kurri ya mata yama kasa cewa komai, ya sauke ajiyar zuciya idanunsa cikeda kwalla "Shikenan Ummy, na bar maganan kuma insha Allahu bazan k'ara tadoshi bah. Saidai inaso ki sa a ranki ni mai k'aunar ki ne koda yaushe" Jikinta ne yayi sanyi ta zuba masa narkakun idanunta tana kallansa, mik'ewa yayi yamata sallama ya fito daga gidan dan dama a falo suke. Bai sake waiwayo wa ba har ya shiga motarsa ya tada yabar k'ofar gidan a guje. Bin motar nasa tayi da kallo hawaye na gangara a idonta, tanajin wani abu gameda Jamal tun ba yau ba sai dai bazata iya k'arya alk'awarin data d'aukar wa Bilal bah. Gida ta koma ta tarar da Mama a falo fuskanta a had'e "Yanzu abinda kikayi ya dace Ummy? Keda yakamata ki rufama kanki asiri ki aureshi tunda yana sanki. Shi Bilal d'in da kike mawa baya duniya, babban abinda zaki masa yanzu bai wuce Addu'a ba. Ki so Jamal bazaki tab'a danasani bah" Shiru Ummy tayi tana nazarin maganan Mama "Mama kiyi hak'uri, bazan iya auren Ya Jamal bah. Ko ba dan shi ba kinga Iyayensa da k'anwarsa basa sona." "To ai badasu zaki zauna bah. Ni nasan har yanzu Maganan Bilal ne a ranki kuma yakamata ki cire shi tunda baya raye. Yau da Bilal na raye Jamal yazo bazan tab'a yarda ki auri Jamal ba sai Bilal, to k'addara ta riga fata, kawai sai muce Allah ya sa haka shi yafi alheri" Kuka Ummyn ta fashe dashi ta shige d'akinta. *Bayan sati d'aya* Hurama Abba wuta Mami tayi dole aka saka ranar bikin Jamal da Mabrookah wata d'aya, ranar karka so kaga Jamal sai ya baka tausayi, abin duniya ya taru ya masa yawa, ga sa ranan sa da Mabrookah ga Abinda ya faru tsakaninsa da Ummy. Dan tun daga ranar bai sake taka k'afarsa gidan bah. Wanda hakan sosai ya damu Ummyn dan tasan fushi yayi. Ranar juma'a da daddare Jamal ya shirya cikin farar yadi sai baza k'anshi yake, keyn motarsa ya d'auka bai zame ko ina ba sai gidansu Ummy. Yana isa k'ofar gidan yaga Wasu matasa run fito daga gidan d'auke da Baba Ummy ba biye dasu tana kuka, a rud'e ya k'arasa yana tambayan abinda ya faru, Mama ce tayi k'arfin halin sanar dashi ciwon sa ne ya tashi. Da taimakon sa aka sakashi a motarsa, Ummy da Mama suka shiga dukansu suna kuka, direct shika yayi dashi, nan likitoci suka duk'ufa kansa, cikin y'an mintoci Baba Ya cika. Innalillahi wa inna ilaihi raijun! Karku so kuga Ummy a lokacin, rikid'ewa tayi kamar mai hauka, Mama ko suma tayi saboda tsananin firgita, shima Jamal kuka ne ya sub'uce masa na tausayin halinda Ummy da Mama suka shiga, Ambulance ya biya suka d'auko gawan Baba aka mai doshi gida. Washe gari da safe aka masa sallah, ciki harda Abba da Ramadhan da sauran 'yan uwa da abokan arziki. Ummy ta koma abin tausayi, tun tana kuka sautin na fitowa har muryanta ya dishe, fuskanta ya kumbura yayi sintim gwanin ban tausayi. Abba da kansa ya ingizo k'eyar Mami dasu Aunty Faty harda Twins da Mabrookah sukazo sukayi gaisuwa sunata yatsine yatsine, dan ranar da aka sanar dashi abinda ya faru na koran Ummy, ranar yayi fad'a sosai kamar ya ari baki, Ranar saida kowa na gidan ya gane kuransa saboda yanda ran Abban ya b'aci. Sadakan kayan Abinci Abba yasa aka kawo, tun daga kan Shinkafa, masara, taliya, wake da sauran kayan masarufi dan yaji dad'in zama da Ummy nad'an kad'an bah. Ranar Uku Yannin Baba su biyu sukazo daga k'auyen wudil, kallansu Ummy take cikeda takaici, tunda aka haifeta bata tab'a ganin sunzo gidansu ba saidai su Ummyn suje, anma yanzu daya rasu gashi sun d'auko k'afa suna kukan munafinci. Bayan anyi addu'an uku kowa ya watse, Baba Sallau ya shigo falo inda mata suke ya kalli Mama yace "Dije fito muna san magana dake" Bah musu ta mik'e ta fito tareda tsugunnawa "Dama akan maganan Ummy neh, yarinya gand'ediya kamar wannan ku tasata gaba kuna kallo" Baba Tanko yace "Da a k'auye take ai da yanzu tanada 'yaya shidda" Itadai Mama batace komai ba kanta k'asa, Baba Sallau yace "Ina yarinyar take, kira min ita nan dan na yanke hukuncin aura mata d'ana Iliya" Dam! Gaban Mama ya fad'i ta d'ago tad'an kallesu "Wai ina Ummyn take ne" Mama ta mik'e ta kirata, tazo itama ta tsugunna kamar yanda taga Mama tayi, "Munyi shawara nida Tanko mun yanke hukuncin aurar dake ga d'ana Iliya nan da kwana hud'u, ma'ana ranar bakwai ana gama addu'an bakwai za'a daura auren ku" Ba shiri Ummy ta saki kuka tana kallan Mama "Haba Yaya Sallau yakamata ku fara tambayan yarinyan nan kuji idan tanada wanda takeso" "Iyeh! Lallai Dije, ke har kin isa ki fad'a mana abinda zamu yanke muda 'yarmu" Nan Baba Sallau ya soma sababi, Mama bata sake cewa komai bah kanta k'asa, Ummy ko sai kuka take. Bayan sun k'ulle a d'aki Mama ta zauna kusada Ummy wacce har lokacin take kuka "Ummy kiyi hak'uri ki daina kukan nan, ki tsaya ki saurareni" Hawayen idanunta ta share tana kallan Mama "Mai zai hana kima Jamal magana, kice ya turo magabatansa kamin lokacin, kinga da ki auri Iliya wanda ko ilimin addini bashida shi gwara kin auri Jamal, wata rana inda rai Mamarsa zata soki" Ummy ta girgiza kai tana hawaye "Mama ki kyallesu kawai su aura min Iliyan" Ta sake rushewa da kuka "Ni kuma haka Allah yayi dani..." Mama tasa hannu ta rufe mata baki dasauri "Kul! Karna k'ara ji, kibi shawara ta k'ila a dace, dan ni ban isa in hanasu abinda sukayi niyya bah dan a yanzu sun fini iko dake" Shiru Ummy tayi batace komai bah, duk yanda Mami taso ta fad'akar da ita k'i tayi haka ta hak'ura ta kyalleta, duk da tausayin 'yar nata dake cike a ranta. Jamal bai samu dawowa washe gari ba sai ranan da akayi biyar, gidan ya shigo kamar yanda ya saba, Ummyn ya samu makure waje d'aya tana tunani, zama yayi kusada ita na kusan minti goma anma har lokacin batasan yazo ba. Saida yad'an tafa hannunsa sannan ta d'ago a razane tana kallansa "Dan Allah ki cire tunani a ranki Ummy, Addu'a yakamata kiyita masa ba wannan dogon tunanin bah" Ta rushe da kuka tana kallansa k'asa k'asa, hankalinsa ne ya tashi ya zuba mata ido yana kallanta da mamaki "Menene damuwarki? Fad'amin me aka miki?" Kai ta kawar gefe tana cigaba da kuka "Pls Ummy, bana iya jure ganin damuwarki" Dakyar ya shawo kanta ta sanar dashi abinda ke faruwa. Ba k'aramin tashi hankalinsa yayi bah, dakyar ya iya mata sallama ya nufi gida. Dakinshi ya shiga ya soma safa da marwa cikin tunani, sai zufa yake kamar wanda yake filin daga. Waya ya d'auka ya soma neman
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82