Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

kika fara zuwa har Mabrookah ta hanaki shiga" Sai a sannan Ummy ta shedata tad'anyi murmushi tace "Na tuna" Dattijuwar tace "Sunana talatu, tun ranar dana ganki naji kin kwanta min a rai ganin sauk'in kanki da kuma tarbiyarki. Lallai kin chanchanci aikin da aka saki" Laurat tace "Mama Talatu anma Hajiyar nan batada hankali ina aka tab'a ba yar aiki gyaran d'akin miji" "Kull 'yar nan, kinsan dai irin gidan da kike. Ki kama bakinki kisa masa lunzami" Turo baki Laurat tayi ta cigaba da aikinta, Mama talatu ta kalli Ummy tace "Wannan wani aiki neh babba Ummy, ki kula ki tsare gaskiya. Kinsan zuciya batada k'ashi, kiyi taka tsantsan da duk wani abu da kika gani, kada ki zama mai yawan bincike. Ki tsaya a matsayinki inda aka ajeki, banda shishigi akan alamuran gidan nan kinaji" Kai Ummy ta gyad'a tace "Nagode Mama Talatu Insha Allahu zan kiyaye" Mama talatu tace "Sannan duk abinda baki ganeh ba ki tambayeni, ni ina b'angaren masu share share neh kinji" Ummy ta k'ara gyad'a kai, Mama talatu ta masu sallama tabar wajan. Laurat ta aje wuk'art hannunta tace "Aike Ummy kakarki ta yanke sak'a, kinsan su masu kud'in nan wani lokacin mantawa suke da kud'i idan suka aje" Ta juya ta kalli gabas da yanma ta waigo tana kallan Ummyn "Karki dai manta dani, idan kin samu ina nan" Dariya Ummy tayi ta mik'e tace "Laurat kenan kinada matsala, barin dawo zamuyi magana" Sama ta haura b'angaren d'akinsu Hajiya, d'akuna ne wajan guda shidda, biyun farko na Hajiya ne da Mabrookah, k'ugu ta rik'e tana kallan d'akunan, na kusada na Hajiyan ta hannun hagu ta saka keyn, murd'awa taitayi yakiyi ta zare tareda murd'a kofan d'akin, take ya bud'e tad'an tab'e baki ta tura ta shiga. Wani sanyi neh da k'anshi ya dakan mata hanci, a hankali ta shiga tana b'in d'akin da kallo, sosai d'akin ya burgeta komai na d'akin blue hatta labulen d'akin blue neh, d'aga ido da zatayi ta hango mutum zaune kan wheell chair yana facing windown d'akin. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:23 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 11 A rud'e tabar dak'in jikinta na rawa, bak'in k'ofan ta tsaya tana kallan cikin d'akin, har lokacin yana kallan windown bai juyo bah. Jim tayi wani zufa ya karyo mata, sad'af sad'af ta k'ara shiga d'akin jikinta na cigaba da rawa, ta zagaya gabanshi tana kallan fuskarsa. Kyakyyawan saurayi ne wanda a k'alla zaikai shekara ashirin da biyar ko fi, fari ne daidai misali dan baya sahun bak'ake, kuma baza'a kirashi wankan tarwad'a bah dan yanada haske. Gashin kansa nada yawa mai tsayi yayi curl sai shek'i yake. Saje ne kwance kan kyakyawar fuskrsa wanda ya k'ara masa kyau da kwarjini. Idanunsa yan madaidaita masu kyawun gaske, hancinsa ma ba dogo baneh sosai saidai yayi daidai cikin 'yar fuskarsa mai d'an tsayi. Bakinsa irin light red d'in nan neh madaidaici cikin fuskar tasa. Lumshe ido Ummy tayi ta bud'e tana cigaba da kallanshi, har lokacin idanunshi na kallan windown ko kyaftawa baiyi ba balle yasan da mutum a wajan. Hannu tasa tad'anyi motsi wajan idanunsa anma ko gezau beyi bah, kurrri tamai gabanta na cigaba da fad'uwa anya wannan mutum nada rai kuwa. Jim tad'anyi na wani lokaci sannan ta fita daga d'akin tana waiwayonsa. Sosai alamarinsa yabata mamaki, a sanyaye ta bibi duka sauran d'akunan tasa keyn anma beyi bah, k'asa ta koma ta samu Laurat tana aikace aikacenta, zama tayi duk jikinta a mace, Laurat ta matso tana kallanta "Yadai Ummy meh aka samo mana neh" Maganan Laurat dariya ya bata tad'anyi murmushi tace "Laurat knan, maganarki yana bani mamaki, rik'on amana na d'aya daga cikin abinda ke sa a k'ara yarda da kuma san mutum." Ta mik'e tana murmushi tareda dafa Laurat "Banida ra'ayin abinda kike fad'i, burina na kasance mai kiyaye duk wani doka da aka shimfid'a min, banasan wuce gona da iri akan lamuran dabai shafeni bah" Laurat tayi jim tana gyad'a kai "Gaskiya kika fad'a Ummy" Taja hannunta suka zauna ta kalli Ummy tace "Ni y'ar garin kaduna ce a anguwar tudunwada, na taso bansan iyayena bah ina hannun kakata wacce itama ta tsufa. Na tashi cikin talauci da matsin rayuwa saboda itama kakar tawa batada k'arfi, Iyayena y'an garin kano neh so d'aya ta tab'a kaini wajansu, suma basuda k'arfin da zamu iya rik'eni. Hawaye ne suka gangaro mata tasa bayan hannu ta share tace "Wanchan shekaran kakar tawa ta rasu, nan na koma hannun wata dilalliya dake nan mak'otan mu saboda banida kowa, shine ta d'auko ni ta kawoni nan, yanxu kimanin watana takwas knan a nan" Ummy ta tausaya mata sosai, tasa hannu tana share mata hawaye "Ki daina kuka Allah yana tare dake, insha Allahu rayuwarki zan inganta nan gaba" Gyad'a kai Laurat tayi ta mik'e ta cigaba da aikinta, Ummy tace "Banfa gyara d'akin bah" "Meyasa?" Laurat ta tambayeta Ummy ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni duk d'akunan dake sama ba wanda ban sa keyn ba baiyi bah, kinma san wani abu kuwa?" "Aa meya faru?" Laurat ta tambaya, Ummy tace "Wani d'aki na shiga naga wani mutum zaune a kujeran guragu gashin nan dai kamar baida rai" Murmushi Laurat tayi tace "Sau d'aya na tab'a ganinshi tunda nazo gidan nan, nima yanda kika ganshi haka na ganshi" Da damuwa Ummy tace "Tho shi wanene?" Laurat tace "Ance d'an su Hajiya neh" Kai Ummy ta gyad'a ta kauda maganan. Hajiya bata dawo gidan ba sai bayan magriba, bayan ta huta Ummy ta sameta a falo ta gaidata tareda shida mata bata gane d'akin bah. Murmushi Hajiya tayi tace "Ummy kenan, ba a nan b'angaren d'akin Alhaji yake bah, b'angaren dake kusada nan nan neh b'angarensa, bakiga makullin falo baneh" Sai a sannan Ummy ta duba tagani, Hajiya tace "Gobe in Allah ya kaimu ki tabbatar kin gyara" "Tho" Ummy tace ta mik'e ta mata saida safe ta tafi d'akinta. Washe gari kamar kullum tana gama gyara d'akin Hajiya dana Mabrookah ta wuce b'angaren Alhaji, Sakin baki tayi ganin Aljannar duniya, nesa ba kusaba b'angaren Alhaji yafi nasu Hajiya kyau duk da suma nasu ba baya yake ba. Gyara tayi sosai dan b'angaren yayi datti dayawa. Haka kullum take aikinta, ta gyara d'akin Hajiya dana Mabrooka ta kuma gyara na Alhaji, tun daga ranar bata k'ara ganin mara lafiyan nan ba duk da kullum idan ta hau sama gyara saita kalli d'akin, yanzu ta gane abinda likitocin nan keyi kullum a gidan. Yau wankin Inner wears d'in Mabrookahn ta kwaso dan ta mayarda ita kamar jaka. wankin kayanta itace duk da akwai washing machine dake gidan, Guga, da duk wasu sauran ayuka duk ita take mata. K'asa ta sauka zuwa bayan gidan inda ta saba wankin itada Laurat suna hira, Tsohon nan maiba flower ruwa ne ya k'araso wajan yazo cire tiyo daga jikin famfo, Gaidashi Ummy tayi ya amsa da fara'a dan yanzu sun saba dashi sosai, so dayawa idan tazo wanki sukan had'u wani lokacin suyita hira dashi. Itama Laurat ta gaidashi ya amsa yana cewa " 'yata wanki akeyi neh" "Eh Baba, ya aiki" Ya amsa da lapia lau, har zai wuce

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82