Skip to content

Chapter 71

Chapter 71

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

kansa Alhaju Ameenun Yanayin fuskansa ne ya sauya, anma ya dake yace l "Wani irin magana kakeyi neh?, me kake nufi" Ammi tayi saurin cewa "Areef kaine?" Areef ya zaro ido yana kallan Ammi da mamaki, Ram wanda ya gane inda maganar tasu ta dosa ya k'araso yana cewa "Wannan maganan ba'a nan yakamat ayita bah, ya kamata a natsa sai a zauna a tattauna" Ya mik'ar da Jamal tsaye, Mifzal yace "Alhaji ku shiga mota kubi bayanmu muje a tattauna a gida" Ba musu suka shishiga mota Jamal ya shiga nasa motan, Ram ne ke driving har zuwa gidansu Jamal. Suna isa Jamal ya musu Jagora zuwa side d'in Abba. Bayan an zazzauna ya koma cikin mota ya d'auko akwatin nan ya shigo dashi d'akin, Ammi na gani ta mik'e tsaye dasauri tana bin akwatin da kallo. Haka shima Alhaji zazzare ido yayi yana kallan akwatin, Areef da Bilal da kuma su Mifzal gaba d'aya bin su Abban suke da kallon Mamaki, Alhaji yayi k'arfin halin cewa "Ina ka samu akwatin nan" Jamal bai b'oye musu komai ba dangane ga abinda ya sani, Ammi ta fashe da kuka tana cewa "Na dad'e ina burin ganin wannan ranar gashi Allah ya kawoshi" Areef ya kalleta da Mamaki "Ammi kun sakani a duhu meke faruwa neh" Alhaji wanda shima k'walla ke zuba a idonsa yace yana nuna Jamal "Wannan yayanka neh, mu muka haifesa, sunansa kaci bayan mun rasa shi da muka haifeka muka maida maka da sunansa" Jamal dake gefe shima yana hawaye yace "Ammi meyasa kuka yar dani, baku damu da halin dazan shiga bah, baku damu da mai zai iya samu na a daran da kuka yardani bah" Ya fashe da kuka sannan ya cigaba da cewa "Ance tsakanin d'a da uwa akwai wata irin shak'uwa mai tsanani, meyasa Ammi kika yarda aka yardani, kuma baku k'ara waiwayan halinda zan shiga bah" Abba ya girgiza kai yana share hawayen dake gangaro masa "Ba laifin mu baneh Areef, ba laifin mu baneh" Haryanzu binsu da kallo Areef keyi cike da mamaki da kuma kokwanto, Alhaji ya soma magana cikin raunin murya "Sunana Alhaji Ameenu Jibril, ni haifafen Garin karaye ne dake Kano. Na taso cikin gata na iyaye kasancewar mahaifina hamshak'in attajiri ne a wanchan lokacin, nayi ilimin Addini dana boko sosai, ana haka iyayena suka rasu duka, hakan yasa na dawo garin kaduna da zama, inda na had'u da Hajiya zainab na aureta, cikin ikon Allah na fara sana'ar saida gwal da taimakon wani ubangidana danayi zuwana Kaduna" Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa "Harkokin kasuwanci ya cigaba da bud'ewa, ina samun Alkahiri da dama haka ina samun cigaba a harkata, har nakaiga inacin gashin kaina nima inada yara, tunda sauran mutanen da muka fara sana'ar tare sukaga haka suka soma mini bak'in ciki, a haka na cigaba da sana'ata, na tara k'addara masu yawa, na gina gida na gani na fad'a. Ana haka matata ta haifeka inda muka saka maka suna Areef" Areef dake gefe ya zaro ido yana kallan Alhajin, Bilal ko k'uri ya musu shida Jamal tabbas ga kama nan da sukeyi da juna, haka kuma suna yanayi da Alhajin, ya cigaba da cewa "Ina sanka Areef fiyeda yanda nakesan kaina, dan kai ka zamo mini a matsayin 'yan uwana dana rasa, duk wani kula da jin dad'i nida matata munayi maka, ana haka wata rana da daddare wuraren k'arfe biyu na dare, mukajiyo shigowan b'arayi gidan, Sosai mukaji tsoro, Matata banda kuka babu abinda take, sunyi sunyi na bud'e k'ofa nak'i, a nan suke shaida min ba kud'i suke nema ba raina dana Matata dana d"ana suke nema, inajin mata jikina dana matata ya soma rawa, da kaina na sakaka a akwati na saka dukiya mai yawa a ciki, na mik'ama matata nace su gudu, ta k'ofar baya suka gudu ni kuma na sadak'ar nazo na bud'e musu k'ofan. Ganin ba iyalina yasa ransu ya b'aci suka sakar min harbi Allah ya taimakeni a Hannu neh, suna ganin na fad'i sukayi tafiyarsu" Ammi na kuka ta d'aura da cewa "Mun fita nayita gudu ina kuka, har Allah ya had'ani da wani mai mota inda ya sanar dani Zaria yayi, ba yanda na iya hakanan na bisa ya saukeni a wani anguwa nayi ta masa godiya dan bai amsa ko sisina bah, haka na kwana a wajan wani bola har washe gari da safe, na yini banci komai bah, da daddare yunwa ya addabeni dole na maidakai cikin akwatin dan bazan iya d'aukanka saboda jikina daba k'arfi, a nan na barka na tafi neman abinci, kafin na dawo an d'aukeka a wajan" Ta k'are maganan cikin kuka, Ram dake gefe yace "To ya akayi kuka had'u da mijinki" Ta share hawayen fuskanta tace "Nayi rayuwa a zaria na kusan shekara d'aya inayi ma wata mai abinci bauta, sannan daga baya na koma Kaduna wajan Iyayena inda anan na sake had'uwa da Mijina ashe yanada sauran kwana" Mifzal dake gefe ya tab'e dan gaba d'aya labarin akwai ganganci da rashin dabara a cikinsa. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 88 Mifzal dake gefe ya tab'e baki dan gaba d'aya labarin akwai ganganci da rashin dabara a cikinsa. Alhaji Ameenu ya zamo daga kan kujeran dayake ya xauna a k'asa yana kuka a hankali "Tun dawowar Zainab danaji labarin b'atanka daga wajanta, babu irin kukan da bamuyi bah da nemenka anma babu wani labari, Wallahi Areef dakai kullum nake kwana a raina har Yau, kullum ina addu'ar ganinka dan a kullum inaji a jikina kanada Rai" Ammi cikin kuka tace "Ka gafarce mu Areef sam bamu yarda kai bah" A hankali ya rarrafa shima yana kuka ya rungume Abba yana kuka a hankali "Ka daina kuka Abbana, bakumin komai bah." Ya juya zuwaga Ammi itama ya rungumeta ya saki wani kuka mai sauti tare da ajiyar zuciya, Babu wanda baiyi k'walla a wajan bah, Ya saki Ammi da Abba yayi sujada yana mai godiya ga Allah. Hannu ya bud'ema Areef k'arami ya k'arasa ya rungumesa ya saki kuka yana cewa "I'm so sorry Bro been so Rude" Jamal ya girgiza masa kai yana share masa hawaye "Its Ok" Mifzal yayi gyaran murya yace "To Alhamdulillah Allah muna godiya daka kawomu wannan rana" Ya kalli Jamal yace "Ina tayaka Farinciki da ganin wannan rana, ranar da kaga Iyayenka na asali." Jamal ya mik'e zumbur yace "Ina zuwa pls" Bai jira mai zasuce ba yabar Falon dasauri, side d'inshi ya shiga ya samu Mabrookah zaune ta zabga tagumi, ya k'arasa tare da kamo hannunta, firgigit tayi ta d'ago tana kallansa, murmushi ya mata itama ta mayar masa "D'auko Hijabinki ina zuwa" Ya haura dasauri zuwa sama, d'aki ya samu Ummy tana bacci wanda yanzu ya zaman mata k'aida kullum da rana sai tayishi, hura mata iska yayi a kunne tare da kai mata kiss a bakinta, tad'an bud'e ido a hankali tana kallansa "Baeby tashi kiji" Ta turo baki ta k'ara lumshe ido "Bacci fa nakeyi" Shima ya shagwab'e fuska yana tura baki "Yanada mahimmanci neh" Dakyar ya lallab'ata ta tashi ya d'auko mata hijab tasa suka fito, Mabrookah na nan falonta tana

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82