Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

kaduna ya nufa direct wajan Ramadhan dan maganar bata waya bace. K'arfe bakwai na safe daidai yayi horn a k'ofar gate d'in gidansu Ramadhan, Mai gadi ne ya bud'e masa ya shiga ya samu guri yayi parking, Ramadhan d'in ya soma nema a waya, cikin muryan bacci ya d'auka Jamal yace "Dallah ka fito ina k'ofar side d'inka" Ba shiri Ramadhan d'in ya mik'e, daga shi sai boxers da singlet ya fito haraban gidan da mamaki "Anma a hanya ka kwana koh" Jamal ya harareshi "Kaifa matsala ce dakai, Aa ka manta tun wachan shekaran nake hanya" Ramadhan ya fashe da dariya yana girgiza kai, side d'in Ramadhan d'in suka Shiga, bayan sunyi breakfast Jamal ya zaiyane wa Ramadhan duk abinda ke faruwa, dan bayada abokin daya wuce shi. Saida Ramadhan ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Tho yanzu kai ya kakeso ayi?" "Bangane ba Ram, Wallahi inasan Ummy so mai tsanani, kai kasani banda wata budurwa balle kace ko yaudaranta zanyi. Ni yanzu abinda nakeso ayi shine muje dakai ko Allah zaisa ta saurareni sai na bata hak'uri" "But Jamal, a yanda na fahimta kamar yarinyan nan bata sanka, meyasa zaka shiga inda ba'a buk'atarka" "She need me Ram, yarinyan da parents d'inta suna buk'atar taimako, Hmm dan baka zauna da ita baneh, Wallahi tayi ta kowane fanni" Ramadhan ya saki dariya yana girgiza kai "Kaifa d'an iska ne Ram, ya ina maka magana kana maidani wani abin dariya" Wani dariyan ya kuma yi, yana cewa "Ai naga abin naka neh naso ya wuce guri, harda wani ta had'u ta kowani fanni" Jamal ya b'ata rai, ganin haka yasa Ramadhan mik'ewa yana cigaba da dariya ya shiga bedroom d'insa. Wanka yayi ya sauyo cikin manyan kaya yana kallan Jamal "Anma dai ba haka zaka gidan sarakan naka ba kawani ci uban zanzaro, ka tashi ka shiga bedroom d'ina akwai kaya kan gado" Saida ya harari Ramadhan d'in sannan ya mik'e ya shiga d'akin ya chanzo zuwa kaftan, sid'e d'in Iyayen Ramadhan d'in suka ya gaida su sannan suka sake d'aukan hanyan zaria. Jamal ne ke driving motan har k'ofar gidansu Ummyn. Shiru dukansu sukayi Jamal ya sauke ajiyar zuciya tareda maida dubansa ga Ramadhan "Ta ina zamu fara?" "Muje mu nemi yaro ya mana sallama da ita" Jamal ya saki malalacin murmushi yana girgiza kai. Ramadhan ya fita daga motan, wani almajiri ya samu ya aikashi ya mai kiranta sannan ya idan ya tambaye shi waye yace Jamal neh. Tana zaune a falo tana tunani Mama na gefenta tana mata fad'an k'in cin abinci datayi, Almajirin ya shigo da sallama ya tsugunna bakin k'ofan ya isar da sako, Ummy tai saurin cewa "Kaje kace bazata zo bah" "Haba Ummy, meyasa haka? Ai ba shi ya miki laifi bah. Kije kiji mai zaice" Ta zunguro baki ta mik'e tad'au hijabinta ta fito, a bakin k'ofar gidan ta toge fuskanta had'e. Kallo d'aya Jamal ya mata yaji gabanshi ya fad'i, jiki a sanyaye ya fito daga motan suka k'arasa shida Ramadhan, "Salamu alaikum" Ramadhan yace yana murmushi Bata amsa ba saima juya fuskanta datayi gefe d'aya "Haba Ummy ai laifin wani baya shafan wani. Ko ba komai yakamata ki amsa sallama nah" Ta sake kauda kai gefe sannan ta amsa "Naji duk abinda ya faru kuma banji dad'i bah. Saidai ina rok'onki karki sa abin a ranki. Kiyi hak'uri da duk abinda ya faru" Hawaye suka cika mata ido tana kallan Ramadhan "Idan kai akayi ma abinda aka min zakaji dad'i? Talauci ba hauka baneh. Tunda nake ban tab'a sata bah haka iyayena, anma aka kirani da iyayena b'arayi" Ta rushe da kuka tasa hijab d'inta ta rufe fuska tana cigaba da kuka. Shidai Jamal ba halin magana saima ransa dake suya "Nasani an miki laifi, anma kiyi hak'uri" Ta d'ago dasauri tana kallanshi "Hak'uri? Inyi hak'uri fa kace?" "Allah muna masa laifi ya yafe mana balle mu y'an adam, karki zama d'aya daga cikin masu bin kururuwan shaid'an. An miki laifi kuma ba'a kyauta miki bah, Anma kiyi hak'uri. Kada ki yanke zumuncin dake tsakanin ki da Jamal Pls" Shiru tayi batace komai ba sai hawaye datake gogewa. Jamal ya d'ago kai yace "Pls Ummy badan niba, nasan harda laifina a ciki, anma kiyi hak'uri." "Shikenan komai ya wuce" Bata jira mai zasu ce ba tayi shigewanta gida. Ramadhan ya mik'ama Jamal hannu sukayi musabaha "Shikenan na gama nawa koh" Kai Jamal d'in ya gyad'a yana murmushi. Ranar a gidan Ramadhan ya kwana washe gari yasa driver ya maida shi gida. A ranar Jamal ya d'au su twins ya kaisu gidan su Ummy, tayi murna sosai da ganinsu dan tasan ba laifinsu cikin abinda aka mata, suma sun bata hak'uri dasu Mama, sun d'an jima a gidan sannan Jamal ya dawo ya d'aukesu Ya maida su gida. Da fad'a Mabrookah ta tari su Twins tana tambayan daga ina suke, Jamal na jinta ko kallanta baiyi ba ya bar wajan zuwa side d'in Abba. Har suka shiga falo tana balbalesu da masifa, Aunty Faty ce ta soma tambayan mai ya faru, Mabrookah ta soma magana tana cewa "Tun d'azu nake neman su ashe sun fita neh da Jamal, kuma bayan na fad'a musu zamuje wani guri dasu" Aunty Faty ta had'e rai tace "Daga ina kuke?" Batare da wani d'ar ba Najma tace "Daga gidansu Ummy, muje bata hak'uri" Wayan Hannun Mabrookah ne ya fad'i ta saki baki tana kallansu "Daga gidansu Ummy? Uban wa ya kaiku" Najwa tace "Ya Jamal" Nan Aunty Faty ta soma masifa, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, Mabrookah ko side d'in Abba ta nufa a fusace, kishingid'e ta sameshi kan kujera idanunsa a lumshe, "Ya Jamal! Jamal!" Bai bud'e idonsa ba saima gyara kwanciya dayayi "Nasan dai kana jina, akan wani dalili zaka d'au Twins ka kaisu gidansu matsiyaciyar yariny...." Marin dataji a kuncinta ne ya hanata k'arasa maganan datayi niya, ya mik'e a fusace yana nunata da yatsa "Kinyi na farko kinyi na k'arshe, wallahi kika sake zagin Ummy sai na lahira ya fiki jin dad'i. Kar kiga kina abinda kika gadama ina saka miki ido, taraki nakeyi, kuma wallahi ko mutuwa zakiyi bazan aureki bah" Ta tushe da kuka tana nuna kanta "Akan wata banza zaka..." Wani marin ya sake d'auketa dashi "Fita! Kafin na la'anta ki" "Wallahi bazan fita ba koda kasheni zakayi, akan wannan yarinyan zata dukeni? Me ta fini dashi? Diri ko meh, ko dan ni bak'a ce. Wallahi saina aureka" Duka ya rufeta dashi dan dama yana ciki da ita, ihu ta dunga yi ba mai kwace ta, haka ya mata ligi ligi yabar side d'in. Saida tayi kuka mai isarta sannan ta koma side dinsu, Mami ta samu a falo itada Aunty Faty, ta shigo ta fad'a jikin Aunty faty tana kuka tareda labarta mata abinda ya faru. Ran Aunty Faty ya sake b'aci tace "Maimuna idan bazaki d'au wani mataki ba zan d'au 'yata nabar miki gidan, akan me d'anki zai kamata yayita jifga kamar ya samu jaka, ai ba shi kad'ai bane Namiji" "Ni Mommy ba inda zani, ina sanshi" Hak'uri Mami ta soma ba Aunty Fatyn dakyar ta samu ta shawo kanta, a ranar Jamal yaga b'acin rai wajan Mami anma hakan

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82