Chapter 66
Chapter 66
kuka take da ihu tana dafe k'afarta. Asibiti Ram da wani d'an sanda sukayi dasu Jamal, ba b'ata lokaci aka amshesu tare da basu taimakon gaggawa. Cikin awa da bai wuce d'aya ba Jamal ya farka tare da mik'ewa zaune. Ram dake kusa dashi yayi saurin rik'esa yana masa sannu "Ram ina Ummyna" Shine Farkon Abinda ya furta, cikin kwantar da hankali yace "Tana lafiya lau, ka kwanta ka huta" Ya fizge jikinsa yana k'okarin mik'ewa "I want to see her Pls" Ya sake maidasa zaune yana lallashinsa "Bazan iya zama batare da naga Wife d'ina bah. Dan Allah ka kaini na ganta hankalina ya kwanta" Hawaye suka cika masa ido, gaba d'aya yanzu tausayi Jamal keba Ram baice komai ba ya mik'e ya kira wata nurse ta cire masa drip d'in hannunsa. Da taimakon Ram d'in yasa takalmi suka fito Ram na rik'e dashi har d'akin da Ummyn take. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:18 AM] +234 706 272 2689: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 81 n 82 Da taimakon Ram yasa takalmi suka fito Ram na rik'e dashi har d'akin da Ummyn ke take. Duk da yanda yake ganin jiri hakan bai hanasa sakin Ram ba ya murd'a kofan d'akin ya shiga. Kwance ya sameta kan gadon marasa lafiya tana bacci, hannunta sanye da canular ana mata k'arin jini. Ya k'arasa ya zauna bakin gadon yana kallanta hawaye cike a idonsa, sai yanzu abubuwan da suka faru suka dawo masa. Hawaye ya soma kansa k'asa har lokacin bai bar mamakin Mami da Aunty Faty bah. Yana nan zaune kusa da ita har bayan minti talatin, Ram da Mifzal suka shigo d'akin a tare. Hannu Mifzal ya mik'a masa sukayi musabaha sannan ya tambayesa ya jikinsa. "Dasauk'i. Nagode Mifzal" Ya juya ya kalli Ram yace "Nagode Ramadhan" Mifzal yayi murmushi yana d'an bubuga kafad'ar Jamal "Mu dakai ba godiya" D'an motsawa Ummyn tayi gaba d'aya hankalinsu ya koma kanta, ta b'ata fuska ta sake juya kwanciyanta. Duk idanunsu nakanta, juye juye ta soma tana rik'e da maranta tana kuka a hankali har lokacin idanunta a lumshe. A rud'e ya rik'o hannunta "Open ur eyes Wife, ni neh, Jamal ne" Kasa bud'e idon tayi har lokacin tana juye juye, Ram ya fita dasauri chan sai gashi shida Dr da wasu nurses. Rok'onsu Likitan yayi akan su bashi waje, dakyar Jamal ya saki hanunta suka fita daga d'akin har lokacin bai daina hawaye bah. Sun d'an dau mintina sannan suka fito, Jamal ya k'arasa inda likitan yake tsaye "Dr hw is she" Da murmushi yace "Komai Lafiya lau, munyi nasarar ba cikin jikinta kariya, yana lafiya ba wani abu. Jinnin data zubar da kuma buguwan data samu a maranta ne yake haddasa mata ciwo a maranta. But data farka zata dawo normal" Jamal ya mik'a masa hannu cike da murna, sukayi musabaha ya wuce. Ba yanda ba'ayi da Jamal ya koma d'akinsa bah dan shima yana under observation anma yaki, dole aka d'auko wani gadon aka sa a d'akin da Ummyn take suna karb'an medication tare. K'arfe takwas da rabi na dare lokacin Ram da Mifzal sun wuce bayan sun aje mai duk abinda yake buk'ata, tashi yayi daga kan gadonsa ya zauna kan kujeran dake kusada Gadon Ummy tare da d'aura kansa kan gadon. Nan da nan bacci mai nauyi da dad'i ya d'aukesa cike da mafarkai kala kala. A Police Station kuwa, Har aka kai Mami bata daina Ihu bah dan ji take kamar k'afar ya guntule ne gaba d'aya, tana kuka Aunty Faty nayi na danasani. Wani likita cikin 'yan sandan ne ya cire mata bullet d'in kafar nata tare da Treating wajan aka turasu a ceil itada Aunty Faty. Kan kace me dambe ya kaure tsakanin su wannan tace laifin wannan neh, wannan ma tace Laifin wannan neh. Babu wanda ya tankasu cikin 'yansandan, Mami ko taci duka wajan Aunty Faty dan ta kasa kwatan kanta saboda k'afarta dake mata zugi dan ko takawa bata iyawa. Iyalen Alhaji Ameenu ne suka zo garin Abuja dan labarin ya riskesu, Hankalinsu a tashe sukazo Police station d'in. Matarsa na ganinsa ta fashe da kuka "Alhaji haka ka koma? Garin yaya haka ta faru" Kasa magana Alhaji Ameenu yayi sboda tsananin b'acin rai, d'ansa kuwa ransa idan yayi dubu ya b'aci, kallo d'aya yama Abban nasa ya fita daga Station d'in. Duk yanda Matar Alhaji Ameenu taso a bada bailing mijinta da Bilal k'i sukayi kan cewa basu gama bincike akansu bah. Ba yanda ta iya hakanan ta hak'ura tabar Station d'in tana kuka. Wayan d'anta mai suna Areef ta soma kira har ya katse bai d'aga ba kuma ga motarda sukazo dashi a parke a k'ofar station d'in. Cikin motar ta zauna tana cigaba da hawaye na tausayin Mijin nata. Tana nan zaune ta hangosa ya sauka a Napeep shida wani sun shiga Station d'in. Ta fito ta bisa da sauri "Areef!" Ta kira sunansa, ya juyo tare da amsawa ransa a b'ace "Ina kaje inata nemanka" Ba tare da wani tunani ba yace "Naje Court ne nakai k'ara" Da mamaki ta kallesa "Kasan me kake fad'a kuwa" Kamar zaiyi kuka yace "Haba Ammi ki dubi abinda akama Abbana fah akan abinda baiji ba bai gani bah, nidai bazan tab'a yarda bah" Bai jira mai zatace ba ya shiga cikin station d'in. Mifzal na Office d'insa takardan sanmacin da Areef ya kawo ya samesa, bayan ya karanta ya saki lallausan Murmushi tare da duba date d'in da za'a shiga Kotun, ya sake yin murmushi "Allah ya kaimu! Ayita ta k'are" ••••••• Bud'e ido tayi a hankali tana bin d'akin da kallo cike da mamaki, tad'an juya gefenta na dama, Jamal ta gani ya d'aura kansa a gadon da take yana bacci bil hak'i da gaskiya. Tayi murmushi tare da cusa hannunta cikin suman kanshi tana d'an masa waiwayi, ya bud'e idonsa dakyar dan bacci ne fal a idonsa, murmushi ta masa ya bud'e ido dasauri tare da mik'ewa zaune. Hannu ta bud'e masa tana masa murmushi dan yanzu gaba d'aya tausayi yake bata, ba musu ta fad'a jikinta suka rungume juna sai hawaye na tausayin junansu, sun dad'e a haka sannan ya janye jikinsa yana kallan fuskanta hawaye na cigaba da gangara daga idonsa "Kiyi hak'uri Wife, nasan komai was my Fault, Laifi na neh ya sh..." Tayi saurin rufe masa baki tana girgiza masa kai, "Ba laifinka baneh My Prince haka Allah yaso" Sosai yaji dad'in sunan data kirasa dashi, ya langwabar dakai gwanin tausayi "Karki danne gaskiya Wife, laifina neh, nine na kasa baki kulawa data dace a matsayina na Mijinki. Ban kasance miji na gari a gareki bah" Ta b'ata fuska tare da juyawa tana kallan wani gefen, cikin shagwab'a tace "Nidai zamu b'ata idan kana wannan maganan. Kaddara ce haka Allah yaso" Ya sake rungumeta yana mai tsananin farinciki. Kula ya soma bata na musamman, shi da kansa yake jinyar abarsa, cikin kwana uku aka sallamesu Ram ya d'aukesu suka dawo gida. Direct Part d'insu sukayi yana d'auke da ita, Palour ya ajeta ya shiga d'akinta ya gyara tsaf sannan ya d'auketa ya kaita sai turo baki take wai ita ya barta tayi tafiya da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82