Chapter 4
Chapter 4
daina ya dawo" Hawaye suka gangaro ma Mama na tausayin y'ar nata, dama tasan dole za'ayi haka, kuka sosai Ummy keyi tana k'okarin sauka daga kan gadon "Mama d'an Allah ki sakeni zanje na nemo Ya Bilal ince ya dawo nida Inna muna kewarsa" Rik'eta Mama tayi "Haba Ummy kin tab'ajin anyi wasa da mutuwa?" Baba ne ya shigo d'akin yana jejefa sandarsa yana laluban waje, saida ya laluba waji tabarma sannan ya zauna, inda yake jiyo kukan Ummy ya maida fuskanci yace "Ummy Rayuwa da mutuwa duk ta Allah ce, Allah ya fimu sanshi shiyasa ya d'aukeshi. Kuma Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i. Kiyi hak'uri ki mik'a lamuranki ga Allah, muma duk zaman jiranta muke, shida ya rigamu baiyi sauri ba mu kuma da muka rage bamuyi jinkiri ba, kiyi hak'uri uwata Allah yana tare damu." Duk'ar da kai kawai tayi tana kuka sosai, Haka suka cigaba da lallashinta anma sam Ummy tak'i daina kuka. Kullum sai ta shiga gidansu Bilal itada Mama, ba abinda take daga kuka sai kuka, Inna tayi tayi Ummy ta daina kuka anma ina. Cikin kwana biyu duk ta rame ta zafge kamar ba Ummy ba, sam ta daina cin abinci, Mama tayi fad'an harta gaji. Haka Inna itama tun tana binta da lallama harta soma fad'a anma Ummy taki. Haka aka gama zaman makoki kowa ya watse ya bar gidajen biyu cikin kewa da damuwa. Idan kaga Ummy saika tausaya mata yanda ta koma lokaci guda, sosai abin ke damun Mama musamman yanzu yanda ta daina magana saidai ta kur'ama abu idanu tayita kallanshi kamar tab'abb'a.. Bayan Wata Shidda Ummy tad'an sake kad'an bakaman da bah saidai yanzu ta koma shiru shiru batada yawan magana, har yanzu dai bata daina kukan Rashin Yayanta kuma masoyinta Bilal ba, Inna na tausayama Ummy sosai halinda take ciki. Yanzu Masa suka komayi da Safe da yanma kuma ba laifi suna d'an ciniki. Dashi suka dogara, duk riban da aka samu a rana dashi ake cin abinci a ranan. Bahar ko tuni ya koma yana a inda Ya Bilal yake aiki d'ah dan ya taimaki kanshi da Mahaifiyarshi.. Yau tun dare ciwon Baba ya tashi, Ummy nachan d'akinta tana bacci bayan ta gama kukanta wanda kullum sai tayishi kafin ta kwanta. A daddafe suka kai Asubah, Mama ce ta fara fitowa jin kiraye kirayen sallah, Kwankwasa kofan Ummy tayi itama ta fito "Sannu Mama" "Yauwa Sannu Ummy, jiya bamuyi bacci ba jikin Mallan" Idanun Ummy ne ya ciko da k'walla "Meya sameshi Mama?" "Ciwon nan ne dai nashi ya tashi" D'akin Ummy ta lek'a ta samu yana bacci, ajiyan zuciya ta sauke ta fito tayi alwala. Da gari yayi haske tana k'okarin fita da kayan sana'arta Jikin Baba yayi zafi sosai sai tari yake akai akai, d'akin ta shiga ta samu Mama kusa dashi tanamai sannu, Tari Mai K'arfi ya k'arayi saiga jini. Kuka Ummy ta saki ta d'aura hannayenta a kai "jini kuma? Innalillahi wa inna ilaihi raj'iun mun shiga uku" Kamin kace me Baba ya fita hayyacin shi, Ummy da Mama ba abinda sukeyi sai kuka, da gudu Ummy ta fita ta samu mai napep suka d'au Baban suka sakashi sukai asibiti dashi.. Saida suka isa Mama tace "Ummy yanzu da muka d'auko Mallan muka kawoshi Asibiti da wani kud'in zamu biya" Hawaye ta share da bayan hannu "Insha Allahu Mama zamu samu abinda zamu abinda zamu biya, mu fara bada y'an kud'in dake wajanmu" An k'arbi Baba an bashi gado, kud'in hannunsu kwata kwata dubu d'aya ne da d'ari hud'u gashi sun kashe d'ari biyu wajan zuwa asibiti. Suna nan zaune aka likitan ya fito ya mik'ama Mama wata takarda "Muna buk'atar wad'an nan magungunan yanzu kuyi sauri" Kallan kallo suka tsaya yi da Ummy, jiki ba k'wari Ummy ta amsa takardan ta nufi pharmacy, Calculating aka musu kud'in dubu bakwai da d'ari biyar, ai nurse d'in bata gama fad'aba Ummy ta saki kuka mai k'arfi. Wata hajiya ce ta shigo wajan cikin takun k'asaita ta k'araso wajan tareda mik'a takardan dake hannunta, ganin Ummy a gefe rakub'e tana kuka yasa ta k'arasa wajanta ta tsaya tana k'are mata kallo Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 11:38 PM] +234 806 215 4020: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 6 Wata hajiyace ta shigo wajan cikin takun k'asaita ta k'araso wajan tareda mik'a takardan dake hannunta, ganin Ummy a gefe rakub'e tana kuka yasa ta k'arasa wajan ta tsaya tana k'are mata kallo "Y'an mata lapia dai wani naki ne ya rasu" D'agowa tayi idanunt cikeda hawaye "Aa Babana aka kwantar kuma bamuda kud'in da zamu biya na magani" Takardan Hannun Ummy ta amsa ta duba sannan ta mik'ama nurse d'in "Gashi ki basu magungunan, da kud'in gado na sati d'aya sai kiyi min total harda nawa" Ummy najin haka ta tsugunna guiwa biyu tana godiya sosai, hannu biyu hajiyan tasa ta d'agota tana share mata hawaye "Aa ki daina mini godiya, Allah ya bashi lapia" "Ameen" tace tana cigaba da godiya kanta k'asa, nurse d'in ta miko mata magungunan ta tafi tana waiwayen hajiyan har ta bar pharmacyn. Bata b'oyema Mama ba ta sanar da ita duk yanda sukayi da hajiyan, Itama tayi godiya tareda ma hajiyan addu'oi na fatan alheri. Cikin ikon Allah kwanan Baba shidda aka sallameshi, suka dawo gida bayan likita ya jajja musu kunne akan kula da maganin Baban da kula gudun abinda zai rink'a bata mai rai saboda ciwon zuciya dake damunshi.. Koda suka dawo gida d'aki Ummy ta shiga ta zauna tana tunanin ciwon Babanta, dole ta nemi kud'i dan cigaba da siyamai magani. Tana cikin tunanin Mama ta shigo d'akin da sallama, Ummy ta amsa tareda Gyara xama "Ummy nazo ne muyi wata shawara dake" "Shawaran meh kuma Mama" Saida Mama ta nisa sannan tace "Shekaranki Goma sha takwas yanzu ya kamata ache kin bar soye soye a k'ofar gida. Babban burina yanzu Ummy bai wuce ace kinyi aure bah anma nasan komai lokaci neh, fatana kawai Allah ya baki miji na gari" Duk'ar da kai Ummy tayi tana murmushi "Dama cewa nayi mai zai hana mu koma sana'a ta cikin gda" "Tho Mama wace sana'a kike ganin zamu koma yi na cikin gda? Ni wallahi babban tashin hankalina ma magungunan Baba inda zamu rink'a samun dubu uku na magani" Ajiyan zuciya Mama ta sauke "Dama ni cewa nayi naga gidajen bayanmu suna neman masu wankau ko shi zamu koma yi ana kawo mana munayi ana biyan mu" Jim Ummy tayi tana nazarin maganan Mama, sam batasan taga iyayenta sun wahala. Wankau aikine mai wahala tabbas kuma gashi Mama ta girma "Tho Ummy mai kikace" Maganan dilalliya ne ya fad'o mata a rai, wani lallausan murmushi ta sauke "Kwanaki chan na tab'ajin dilalliya na cigiyan y'an aiki wai wasu sun bata sautun a sama musu, shine nace mai zai hana naje idan har yanzu ana nema sai nayi kuma na tabbatar za'a samu alheri" Jim Mama tayi tana nazari "Anya kuwa Ummy aikatau kuma?" "Mama dan Allah karkice Aa, ki bari nayi wannan hanyan tamafi sauk'i kinga duk karshen wata mutun nada albashi" "Banak'i bane Ummy ina tunanin Mallan neh" Hannun Mama ta saka a nata "Indai kin amince
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82