Skip to content

Chapter 50

Chapter 50

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,195 words 0 views Progress saved
Download Book

jikinta ta mik'e ta shiga toilet ta saka key. Binta da ido yayi tareda sauke ajiyar zuciya, shi baisan yanda zaiyi ba, sam baya san fushin wife d'insa. Mik'ewa yayi ya fita daga d'akin. D'akinsa ya koma ya cire bedsheet d'in dake kan gadon ya sala cikin washing machine, wani ya d'auko ya shimfid'a ya kwanta cikeda kewa da tunanin Wife d'insa. Mabrookah shiru shiru bata gansa bah, taja tsaki ta rufe ko ina ta haura saman. A hankali ta bud'e k'ofan d'akin, kwance ta samesa idanunsa a rufe, duk a tunaninta bacci yayi, ta kashe wutan d'akin ta k'arasa ta kwanta kusa dashi tana k'okarin shiga jikinsa, cike da takaici yace "Pls Live me alone I'm not in the mood" Ta b'ata fuska "Kai Yaya dan Allah" Tashi yayi ta d'au pillow ya fita daga d'akin ganin tana san b'ata masa rai. Dogon tsaki taja ta kwanta cike da takaici. D'akin Ummy ya murd'a yajishi a rufe, a sanyaye ya hau kan kujeran falon ya kwanta ransa ba dadi. Kiran sallahn farko ya tadasa, ya mik'e ya shiga toilet d'in dake falon yayi alwala ya tafi masallaci. Kamar kullun yauma sai k'arfe bakwai da kwata ya fito daga masallacin, wasu mutane su biyu ya samu a k'ofar gidan tsaye da mai gadi, d'aya sanye da suit bak'i, d'aya kuma magidanci sanye da blue babban riga. D'aya daga cikin masu gadin yace "Yauwa ga Oga nan" Jamal ya k'araso wajan rik'e da chasbaha a hannunsa ya mik'a musu hannu suka gaisa. Mai sanye da suit yace "Sunana Barrister Najib Abubakar, daga Federal High court" Ya nuna dattijon yace "Wannan sunansa Alhaji Tijjani D'an asabe, abokin business ne na Alhaji Surajo. Munzo ne akan bashi dake tsakaninsu kusan shekara uku da suka wuce" Gyad'a kai Jamal yayi yace "Ku mu shiga daga ciki, wannan maganan bana tsaye bane ku shigo daga ciki" Ba musu suka bisa har side d'in Mami, saida suka zauna sannan ya shiga yayo kiran Mami suka fito tare. Bayan sun zauna aka k'ara gaisawa. Barristern ya mik'ama Jamal wani takarda yana cewa "Alhaji Tijjani d'an Asabe na bin Alhaji Surajo kud'i kimanin naira million d'ari da ashirin" Mami ta zaro ido da mamaki tana kallan Barristern "Naira Million d'ari da ashirin fa kace" Sai lokacin Alhaji Tijjani yace "Kwarai da gaske, dan ma ka duba takardan zaka gani a rubuce, harda sa hannunsa dana shaidu" Kurrrri Jamal yayi yana kallan takardar, tabbas ga sa hannun Abba, saidai sauran shaidun ne baisan su waye su bah. Ya mik'ama Mami takardar ta duba tace "Tabbas wannan sa hannun Alhaji ne" Jamal yace "A gaskiya Alhaji, duk shige da fice na mahaifina babu wanda ban sani bah. Duk abinda zaiyi yakan fad'amin, ni bansan da wannan ranchan fa, sannan wad'an nan sunayen na shaidu bansan su bah" Mami tace "Haka neh" Alhaji yace a fusace "Idan kai baka sani ba ai shi Alhajin ya sani, maganan kuma rashin sannin naka ai lokacin kana rashin lafiya." Yanayin yanda Alhajin ke magana yasa ran Jamal ya b'aci, ya mik'e tareda mik'ama Barristern takardar yana cewa "Banida masaniya akan wannan, sannan idan har kunaso mu tabbatar sai ku kawoo shaidun da akayi dasu" Ran Alhaji idan yayi dubu ya b'aci, shima ya mik'e a fusace "Wallahi baku isa bah, ni da hakkina nazo amsa ku cimin mutunci" Uffan Jamal bai sake fad'a ba ya bar falon a fusace. Mami da Aunty Faty ne suka soma basa hak'uri, anma ina sai masifa Alhajin yake har yana cewa zai kai kotu a k'watar masa 'yancin sa. Jamal na shige side d'insa sukayi kicibus da Ummy a bakin k'ofa, kauda fusaka tayi tareda turo baki gaba. Kallanta ya tsaya yi yana murmushi "In kikayi wasa wata rana bakin nan sai yakai kaduna" Duk da yanda take fushi anma hakan bai hanata murmushi ba, ja janyota jikinsa yana murmushi "Pls wife I'm sorry kinji" Yanda yayi magana yasa taji zuciyarta ta sanyaya, taja hancinsa da k'arfi har saida yayi k'ara "Ashhh!" Ta kyalkyale da dariya ta gyara jakan makarantan ta gudu tana dariya. Yau ma kamar jiya side d'in Mami ta shiga, yau ma saida suka zageta tas tareda mata habaici. Makullin motan ta mik'ama Mami, Aunty Faty tayi saurin fisgewa. Haka yau ma ta fito tana hawaye ta shiga mota tabar gidan. D'akinsa ya koma ya shirya ko takan breakfast d'in da Mabrookah ta masa baiyi ba ya fita, side d'in Mami ya shiga, fad'a ta masa sosai akan yanda yama Alhajin nan. Baice komai ba har ta gama ya mik'e ya musu sallama ya fita. A hanya ya dunga neman wayan Lawyern Abba dan yasan shi kad'ai ne zai tabbatar masa da maganan bashin nan da yaga sign d'insa a cikin shaidu. Ajiyar zuciya ya sauke tareda shafa suman kanshi, yanzu ma duk maganan nan da ake, baisan komai game da dukiyar Abban nasa ba sai gidan da suke da kuma Company d'in dayake aiki. Wayan ya soma kira switch off, sosai abin ya basa mamaki dan Lawyers ba kasafai suke chanza number bah. Har yakai wajan aiki bai daina kira ba anma a kashe. Ummy kuwa tun da ta isa makaranta wani zazzab'i ya rufe ta, tasan ba komai ya hadasa mata wannan ba sai rashin baccin da batasamu ba kwana biyu. A daddafe tayi karatu har aka tashi, tana fitowa taga motar Jamal a k'ofar makarantar yana jingine jiki ya hard'e k'afa yana latse latse a wayansa. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Wannan shafin sadaukarwa ce ga * Professor Ibrahim Aliyu Malumfashi Family* Allah ubangiji ya sanya albarka a aurenki ```Swt Meenarh Prof``` Ameen. Page 58 n 59 A daddafe tayi karatun har aka tashi, tana fitowa taga motar Jamal a k'ofar makarantar yana jingine jiki ya hard'e k'afa yana latse latse a wayansa. Da murmushi ta k'arasa inda yake tsaye, kurrri ya mata yana kallanta, ji yayi kamar ya rungumota anma ba hali saboda student d'in dake ta shige da fice a k'ofar gate d'in makarantar. K'arasawa yayi ya amsa jakan hannunta wanda dama ya mata nauyi, gaban motan ya bud'e mata ta shiga yaja suka bar haraban makarantar. Titi take ta kallo tana yatsine fuska sboda yanda takae jin jikinta. Yana driving lokaci lokaci yakan juya ya kalleta, ganin yanda b'ata fuska yasa yace "Yadai Wife, ko bakiyi murnan ganina baneh?" Sake turo baki tayi bata kallesa bah, d'an dariya yayi mara sauti, yau rigima kenan take jin yi. Har suka iso gida bata daina kallan windown tana b'ata fuska bah, yana parking ya fito ya zagaya ya bud'e mata ta fito ta wuce side d'insu. Da kallo ya bita har ta shige ya girgiza kai ya d'auko jakanta dake seat d'in baya yabi bayanta. Mabrookah ya samu zaune a falonta itada wata k'awarta suna hira, k'awar nata na ganinsa ta gaida sa ya amsa yana murmushi "Amarya sannu da gida" Jakan hannunsa take ta kallo tana yatsine fuska, baisake ce mata komai ba ya haura sama abunsa, d'akin Ummy ya nufa ya bud'e a hankali da sallama, kwance ya sameta kan gado ko uniform bata cire ba, ta k'uddun dune waje d'aya idanunta a lumshe sai hawaye dake gangara daga

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82