Chapter 10
Chapter 10
Camrey wanda Turawa masu aikin Jamal d'in ke ciki. Cikin ABU suka shiga suka d'an zazaga sannan suka fito suka tafi wani park. Ummy sai raba ido take dan sunan tana zaria neh kawai anma tunda take bata tab'a shiga cikin ABU bah. Bayan sunyi parking motocinsu Hajiya ta fito tareda shimfid'a k'aton carpet a k'asa, turawan suka kamoshi aka d'aurashi kan wheel chair d'insa. Kusa dashi Hajiya ta zauna tana kallanshi idanunta cikeda kwalla "Allah ya baka lapia Jamal, Ina kewarka sosai, Allah ya tashi..." Kasa k'arasa maganan tayi ta tushe da kuka, Ummy hawaye ya cika mata ido ta rarrafo kusada Hajiyar tana cewa "Kiyi hak'uri Hajiya, Addu'a yakamata ki rink'a masa ba kuka bah" Hajiya ta juyo ta kalleta tareda share hawayen fuskanta, wani malalacin Murmushi tayi tace "Bakisan yanda nakeji ba Ummy, Inasan Jamal fiyeda komai a duniya, da kud'i zaisa Jamal ya warke da tuni ya warke, banida wani buri yanzu daya wuce naga koda murmushin Jamal koda bazai bud'i baki yayi magana bah" Hawaye suka gangaro ma Ummy tace "Kiyi hak'uri Hajiya, kid'au hakan jarabawa ce a gareku gaba d'aya. Kiyi ta masa addu'a insha Allahu zai warke ya dawo yanda yake dah" Wani kukan Hajiya ta fashe dashi "Na cire wannan tsamanin Ummy, shekaran Jamal Uku a zaune a wannan kujeran, baya magana, baya motsi" Hijab d'in jikinta tasa tana sharema Hajiyan hawaye. "Duk mumini baya cire rai daga rahamar Allah, kiyi hak'uri wata rana sai labari. Insha Allahu wata rana sai kin gaji idan ya fara miki surutu" Sosai maganan Ummy yaba Hajiya dariya, tad'anyi murmushi tana duban Jamal d'in dake zaune kamar gunki kan keke. Kayan ciye ciye Hajiya ta siya musu sukaci suka sha, dama shi Jamal yana sanye da NG tube ta hancinsa dan baya iya tauna abinci saidai a d'ura masa abu mai ruwa ruwa ta hancinsa. Maltina Hajiya taba d'aya daga cikin masu kula dashi ta bashi, ta syringe ta soma zuk'a tana d'ura masa ta tube d'in, ganin yanda ake basa abincin tausayi yasa Ummy fashewa da kuka mara sauti ta kauda kanta gefe. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:25 AM] +234 806 215 4020: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 13 Tausayi yasa Ummy fashewa da kuka mara sauti ta kauda kanta gefe. Ji tayi duk kayan ciye ciyen sun isheta ta turasu gefe ta d'ago idanunta tana kallan Jamal d'in. Hajiya ta nisa tace "Ina jin dad'in zama dake Ummy, kinda Hankali da tarbiya ga natsuwa" Murmushi Ummyn tayi ta duk'ar da kanta k'asa "Inaso ki d'aukeni a matsayin Uwa a gareki, kada kiji tsoro ko shakkan sanar dani damuwarki kinji?" Gyad'a kai tayi sannan tace cikin sanyin Murya "Nagode Hajiya" Murmushi Hajiya tayi tace "Ki rink'a kirana da Mami kamar yanda Mabrookah take kirana. Ke da ita duk d'aya na d'aukeku" Godiya Ummy ta mata sosai, sun jima sannan suka d'au hanyan gida. A wani boutique suka tsaya Mami tace Ummy ta biyota ciki, kaya Mami keta d'auka na maza ga dukan alamu na Jamal neh, sai kuma wasu data d'auka na mata itadai Ummy sai binta take a baya, juyowa tayi suka had'a ido tace "Ki d'auka duk abinda kikeso" Ware ido Ummy tayi tana kallan Hajiyar, kasa d'aukan komai tayi ganin tak'i d'auka yasa Mami ta d'aukan mata dogaren riguna da ready made atamfofi wanda zasu mata. Sun biya Ummy ta d'au ledojin suka nufi mota suka wuce gida. Saida takaima Hajiyar kayan d'aki sannan ta sauko ta koma d'akinta ta sauya kayan jikinta zuwa uniform ta nufi kicin wajan Laurat, koda taje ta sameta ta cika tayi fam saura kad'an ta fashe. Kallo d'aya Ummy ta mata ta kyalkyalle da dariya "Hajiya Laurat, yadai meya faru?" Laurat ta k'ara turo baki ta kauda kai, dariya Ummy ta k'arayi tace "Ahaf karkiyi maganan, ai gobe ina gida abuna maga da wanda zakiyi" Jin haka yasa ta juyo dasauri tana yatsine fuska "Ai kece kin cika abin haushi, ba inda ban nemeki ba a gidan nan ban ganki bah" "Tho maida wuk'ar, mun fita ne da Hajiya d'azu" Da mamaki Laurat tace "Dah Hajiya?" Ummy ta gyad'a kai tareda zama kusada ita ta soma bata labarin fitar nasu. Hannunta Laurat ta kama tana murmushin farinciki "Ummy kin shigo gidan nan da k'afar dama, lallai kinada sa'a" Ummy tai dariya kawai batace komai bah. Washe gari misalin k'arfe goma Ummy ta fito daga kicin dan tasan a wannan lokacin ya isa ace su Hajiyan sun tashi, sama ta haura tayi knocking d'akin Hajiya, izini Hajiyan ta bata ta shiga da sallama, zaune ta sameta kan stool tana shafa cleanzer a fuskanta, har k'asa ta tsugunna ta gaidata ta amsa tana kallanta da murmushi "Barin baki guri kiyi aikinki" Tashi Hajiyan tayi har takai bakin k'ofa sai kuma ta dawo tace "Jiya shine kika ajemin kayan nan a d'akina? Ai na saya miki neh ki d'auka ki cigaba da anfani dasu." Ta nuna mata k'aton ledan dake kusada bedside tana cewa "Gashi chan ki d'auka" Godiya Ummy ta shiga mata tai saurin girgiza mata kai tana cewa "Ba godiya a tsakanin mu Ummy, kin wuce haka a wurina" Bata jira mai zatace ba tabar d'akin, aikinta ta shiga yi ta gyara ko ina tasa turaren wuta mai k'anshi ta fito bayan ta d'au ledan kayan. K'asa ta sauka ta kai ledan d'aki sannan ta dawo ta shiga d'akin Mabrookah, saida ta gama mata wulak'anci da zagi sannan ta fito ta bata waje. Dama kuka baima Ummy wuya, saida tayi mai isarta sannan ta gyara d'akin ta fito. Yau ko k'ofar d'akin Jamal bata kalla ba ta sauko k'asa ta koma d'akinta. Kayan da Mami tasai mata ta bud'e ta duduba, kaya ne masu kyan gaske da tsada, set biyu wanda tasan zaima Mamanta ta d'auka tasa a leda sannan ta sauya kaya cikin wanda Mamin tasai mata, dogon riga neh pink swait mai stones a k'irji, sosai kayan suka amsheta tayi kyau sosai, dama Ummyn ba banza ba akwai diri. Farin hijab tasa ta fito zuwa falo, Mami tama sallama wannan karon driver akasa ya kaita gida. Iyayenta sunyi farinciki da zuwanta, ranar kusan raba dare sukayi suna hira, a nan Ummy ke fad'a musu matsalan Jamal, sunyi alhini tareda mai addu'an samun Lapia. Washe gari saida ta musu girki da duk wani abu da suke buk'ata sannan ta taho, wannan karan bata shiga gidansu Bilal bah dan wannan satin a kuraren lokaci tazo. D'akinta ta shiga ta sauya kayanta sannan ta haura sama zuwa d'akin Mami ta shaida mata dawowanta, kicin ta shiga ta samu mutuniyar nata na gyaran alaiyahu, ta gaida sauran mutanen kicin d'in sanan ta zauna kusada Laurat tace "Sannu da aiki" "Yauwa, anma fah yau kin dad'e baki dawoba" Ummy ta saki murmushi tana hararanta da wasa "Keko ina tsakiyar Baba da Mama mai zai kaini dawowa yanzu" Murmushin k'arfin hali Laurat tayi, idanunta suka ciko da kwalla tunawa da Kakarta dan ita batasan dad'in Iyayeba saboda tana k'arama suka rasu. Ummy tai saurin kauda zancen da cewa "Mama na gaishe ki, har y'ar tsaraba ta bani na kawo miki" Da fara'a Laurat ta d'ago tace "Kai dan Allah dagaske?" Ummy ta gyad'a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82