Chapter 31
Chapter 31
it_ Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 9:44 PM] +234 903 823 4806: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 35 Ram ko kamar ya fashe saboda b'acin rai. Harara yaketa wurga ma Taseem har suka bar wajan. Ummy na shiga zauren gidansu Inna ta mik'a ma Laurat kedan tana cewa "Wai kayan dinner da ko menene oho" Amsa Laurat d'in tayi suka k'arasa cikin gidan, Inna ta mik'ama kayan sannan suka bud'e, Gowns ne guda biyu, d'aya Red mai touch d'in yellow, sai Head Bak'i, d'inkin sosai yayi kyau Laurat sai yaba kayan take. Da zumud'i ta d'aga d'ayan gown d'in, shi kuma bak'i neh da Farin Head, sai rafan y'an dubu guda biyu daya fad'o. Inna ta d'auka baki bud'e "Wannan kud'in fah!" "Ina tunanin na manni neh" cewar Laurat Itadai Ummy ko uhumm batace bah saima kauda kai gefe datayi tana kallan kayan ta gefen ido, dan itama sun burgeta sosai. A chan b'angaren Amarya Mabrookah kuwa, shirye shirye ake duk da dukansu babu wanda ransa ke cikin dad'i na maganan Auran Ummy. Bak'i ne cike a gidan daga b'angaren Mami da kuma Abba, itama Aunty Fatyn nata tawagar duk a nan suka yada zango. Su Aunty Zainab duk sun iso, itadai sam batajin dad'in zaman da Aunty Fatyn keyi a gidan Mami, tadaiyi shiru ne dan tasan idan tayi magana zasu iya rabuwa baran baran dan ba hak'uri Aunty Fatyn keda shi bah. Da daddaran ranar Najma da Najwa suka samu Aunty Zainab Umminsu a d'aki, zama sukayi Najma ta soma rok'onta akan ta barsu suje Gidansu Ummy suyi nasu shagalin. Da mamaji Aunty Zainab tace "In banda shashanci irin naku, yaushe ake barin sha'anin gida a tafi na bare" Najwa tace "Ummi kinga fah mu itace k'awarmu, kuma Aunty Mabrookah ba kulamu takeyi bah" Nan suka kwashe duk abinda ya faru lokacin da ta tafi suka sanar da ita. Sosai ta tausaya ma Ummyn "Idan na barku kuka tafi zan jama kaina surutu neh, kuyi hak'uri kawai ku zauna nan" Ga mamakinta sai gani tayi sun fashe da kuka, binsu da ido take tayi da mamaki. Ajiyan zuciya ta sauke sannan tace "Shikenan kuje, anma dan Allah ku kiyaye" Rungumeta sukayi a tare har saida suka fad'a kan gadon datake zaune, duka ta d'aka musu "Tho ku k'arsani ku huta" Suka mik'e suna dariya suka nufi d'akinsu, kaya suka loda suka fito tareda ma Ummin nasu sallama. Ram suka samu ya kaisu lokacin anata kiraye kirayen sallan Magriba, dan dama shima Abba ya aikeshi gidan wajan kawun nan Ummy. A mota Ram ke cewa "D'azu muka dawo daga gidan, sun ce wallima kawai zasuyi" Najma tace "To Ya Ramadhan nawa kuka basu" "50k" yace a takaice "Haba Ya Ramadhan, 50k mai zeyi wallahi yayi kad'an." Murmushi yayi yasa hannu a aljihu ya ciro wani rafan yan d'ari biyar ya mik'a musu "Wannan fah" Najwa tace "Eh to za'ayi managi" Da mamaki ya d'an kuyo ya kalleta "Lallai ma yaran nan" Suka kwashe da dariya daidai lokacin da suka k'arasa gidan. Dasauri suka fito suka shige cikin gidansu Ummyn, a cike suka samu gidan, dakyar suka iya lalubo Mama, bayan sun gaisa take fad'a musu tana chan mak'ota. Rige rigen shiga suka soma yi gidan Inna, Ummy dake zaune tsakar gidan kan kujeran tsuguno zatayi alwala ta mik'e cikeda farinciki ta rungumosu tana dariya. Laurat da Inna suka fito suka musu sannu da zuwa. Sosai Ummy taji dad'i da suka fad'a mata nan zasu zauna ayi biki. Inna ma tayi farincikin zuwansu musamman data lura yaran wayaiyu ne kuma sunada tarbiya. Dakyar suka matsa ma Ummy a daran suka kakkai ma k'awayenta dake layin kati, da kuma maza wad'anda suke abin arziki lokacin da take saida Awara. Laurat ta d'iba taba Bahar dan ya rabama nasa abokanan da kuma 'yan uwa da abokan arziki. Ranar da daddare Ummy ta k'uduri niyan kiran Bilal dan suyi shawaran abinda za'ayi, dan yace mata kada ta k'ara nuna ma kowa bata san auren. Bayan kowa yayi bacci ta lalubo numbern Bilal d'in ta danna kamar yanda Laurat ta koya mata. Ringing biyu ya d'auka, sallama ta masa ya amsa a dak'ile "Ina yini Ya Bilal" "Lafiya lau ya shirye shiryen biki" Ta d'anyi Jim batace komai bah "Na lura duk fad'in sanda kike min k'arya neh. Har yana kawo miki kati kuna rabawa." "Wallahi ba haka baneh Ya Bilal ni..." Yayi saurin katseta da cewa "Ba abinda zaki fad'amin Ummy! Nagode da yaurada ta da kikayi" "Dan Allah ya Bilal kayi hak'uri, wallahi ina sanka karka min haka" "Inda kina sona da baki kai har yau da auransa a kanki bah. Nayi dana sanin baki amanar zuciyata Hrt, ashe bazaki iya amanar da kika d'aukan min bah" Kuka ta fashe dashi ta k'ara rik'e wayan sosai a kunnenta. Shima kukan yake a hankali "Bazan tab'a rayuwa bake bah. Sai na nuna ma Jamaludeen kuskurensa na san abinda nakeso" Kan tayi magana ya kashe kiran. Da kuka ta sake kira anma taji switch off. Kuka ta fashe dashi ta kwanta tana kuka sosai. Haka ta tashi washe gari da kumburaren fuska, Kallo d'aya Inna ta mata ta gane kuka tayi. Fad'a sosai ta mata dan tasan bai wuce akan maganan Bilal. Wuraren k'arfe takwas na safe suka bar gidan, Gyallesu suka nufa gidan Lalle, an rangad'a mata lalle kyan gaske da gyaran jiki, suma k'awayen amaryan an musu mai kyau duk sun fito tsaf abinsu. Twins ne suka biya cikin kud'in da Ram ya basu jiya. Sannan suka zarce Kanuri beauty saloon, nan ma aka gyara musu gashin su, su twins sai santin yawan gashin Ummyn sukeyi. Basu bar wajan Saloon d'in ba sai k'arfe biyu da rabi na rana, dan ma Dinnern k'arfe shidda ne. Kasuwa suka shiga suka sai abubuwan da zasuyi anfani dasu na walimar su sannan suka dawo gida a gajiye. Reedah makeover su twins suka gaiyato ta rangad'a musu kwaliya mai kyan gaske, black gown amarya ta saka, aka d'aura mata White head. Kar kuso kuga Ummy ni kaina sai dana yaba abinka da farar fata sai Gowm d'in ya fito da ita sosai. Su Twins dama sun musu d'inki su da Laurat, suma sunyi kyau cikin Milk Gown da Red head. Kan kace me gidan ya cika da k'awayen Ummy dukan su cikin shirin zuwa dinner. A chan gida kuwa rigima ce ya b'alle tsakanin Jamal da Amaryar tasa Mabrookah. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 9:45 PM] +234 903 823 4806: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 36 A Chan gida kuwa rigima ce ta b'alle tsakanin Jamal da Amaryar tasa Mabrookah, lokacin da taji cewa shi da abokansa ne zamu je d'aukan Ummy Itama kwaliya taci cikin Brown Gown mai tsadar gaske da milk head, tayi kyau itama sosai, k'awayenta kuma suna sanye da red gown suma duk sunyi kyau. Ana gama shiryata ta shiga side d'in Abba dan a nan Jamal d'in yake, ko kallon abokanan angon dake nan falo batayi ba ta shiga bedroom d'insa. Tsaye ta samesa yana sanya agogo, shima yayi matuk'ar kyau, yana sanye da Arsh d'in shadda sai zuba k'amshi yake. "Haba Jamal! Ya za'ayi kace ni
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82