Chapter 78
Chapter 78
sosai tare da musu godiyan abinda sukayi ma Bilal d'in. Shima Bilal yayi farinciki sosai, A nan Areef ke shaida masa Abba yace ya shirya gobe su koma. Umman Bilal ta soma godiya kamar ta ari baki. Waya daleliya Jamal yaba Mama bayan ya saka mata sim da recharge card, tayi godiya haka Ammi da Ummyn, Ummy ne ta shiga nuna mata yanda ake anfani da wayan da kuma yanda akeyin kira. Sun jima a gidan Ummy kamar karta rabu da Mamanta, da hawaye suka fito gidan sai dai bata bari su Ammi sun gani bah. K'arfe Tara da rabi na dare suka shiga gida, Jamal ya wuce side d'insu ita su kuma suka wuce side d'in Abba. Har Ummyn ta kwanta kusa da Areefah bayan tayi wanka Ammi ta shigo d'akin da sallama "Jaleelah kinyi bacci neh?" Ta mik'e zaune "Aa Ammi idona biyu" Ammi ta zauna tana gefen gadon tana cewa "Tashi kije gun mijinki, kinga gobe zamu d'au hanya sai ki shirya daga nan" A kunyace ta mik'e ta d'aura hijab kan kayan baccin jikinta ta fita kanta k'asa. Koda ta shiga kofar a bud'e sameshi, a hankali ta haura sama zuwa d'akinta. Ga mamakinta d'akin ta samesa kwance yayi ruf da ciki da alama bacci yake. Tausayinsa ne ya kamata ta k'arasa a hankali kan gadon ta zauna kusa da kansa. Idanunsa a lumshe yana sauke numfashi a hankali, suman kanshi ta soma shafawa a hankali. Charap taji ya chafke hannun ta bud'e ido tana kallansa har lokacin idanunsa a rufe suke ta soma kici kicin kwacewa, bata ankara ba ya mik'e tare da birkitota yana kallan fuskanta "Thank uh very much Wife, kin daina sona koh" Ta girgiza masa kai a shagwab'e tana tura baki "Ba wani ki fad'amin gaskiya" Ya kai mata light kiss yana d'an murmushi "Ke da kika yarda akesan rabamu dake" Ya shagwab'e fuska "Kwana nawa kenan baki damu dani bah" Ta fashe masa da kuka mara sauti, lokaci guda ya rude ta kwantota jikinsa yana lallashinta "To I'm sorry, pls ki daina" Ya d'ago kanta ya had'a goshinsu waje d'aya "Menene fad'amin Pls, na miki laifi neh?" Ta girgiza masa kai alamar Aa "Ko na mari kaina?" Nan ma ta sake girgiza masa kai, "Na ciro kaina na baki" Dariya tad'anyi mai had'e da kuka, ya rungumeta sosai a jikinsa yana lallashinta "Kinga zaki wahalar min da babyna, fad'amin pls me kike so na miki da zaisa ki daina kuka" Cikin muryan kuka tace "Babu komai" Ya sake matseta a jikinsa yace "Kawai jin dad'in kukan kike" Ta turo baki, ya kwantar da ita kan gadon ya soma lallubanta yana cewa "To bari kiyi kukan mai dalili" K'okarin k'wacewa takeyi ya rik'eta sosai yana cigaba da abinda yake. Ina ganin haka na tattara 'yan matan k'afana tare da taso k'eyar *Khairat* Ummu Manal mukayo waje. Da Asubah da kansa ya had'a mata kaya tana daga kwance kan gado, zazzab'i taji na neman rufeta na kewar mijinta, saida ya gama tsaf sannan ya d'ago suka had'a ido yana cewa "Banaso kiyi nisa dani Wife, but Ammi ta matsa ba yanda zanyi" Ya k'araso bakin gadon ya rungumota jikinsa, hawaye suka zubo mata wanda yajisu akan kafad'arsa, d'agota yayi yasa hannunsa yana goge mata tare da girgiza mata kai a hankali fuskansa d'auke da damuwa "Its ok kinji, dana gama abinda nakeyi zanzo mu zauna tare har abada" Tad'anyi murmushi, rad'a ya mata tayi saurin gocewa tana dariya tana k'okarin mik'ewa "Kai dan Allah wife, bakya tausayina koh. Kinga zamu dad'e bamu had'u bah" Ta turo baki gaba "Ni..ni nagaji wallahi" Yayi saurin kamota ya had'e bakinsu waje d'aya. (Wannan karan Matan Jamaludeen Fans na koro daga d'akin mukayo waje). Lol K'arfe sha d'aya suka gama shiri tsaf, Tuburewa Areef yayi akan bazai bisu bah, Jamal yace su barshi sai su taho tare. Areef ya d'au akwatin Ummyn ya saka a mota yana cewa "My Aunty Mudai sai munzo" Tad'anyi murmushi tana daga bakin k'ofan side d'in, Abba ya shiga gaba gefen Driver, Ammi ta shiga Baya itada Areefah, har Ummy ta bud'e k'ofan zata shiga Jamal yayi saurin Jan Hannunta suka shiga daga Falon side d'in Abba, d'an zaro ido tayi tana kallansa "Suna jirana fah" Rungumeta yayi batare da yace komai bah, ta sauke ajiyar zuciya tare da k'ara k'ankamesa, ya d'ago fuskanta ya had'e bakinsu waje d'aya bata hanasa bah har yayi mai isarsa ya janye bakinsa a hankali. D'agowa yayi fuskansa kamar mai shirin kuka "Zanyi missing d'inki Wife" Yasa hannunsa cikin riganta yana shafa maranta a hankali "Take care of ur self and my Baby kinji" Ta gyad'a masa kai hawaye cike a idanunta, Knocking sukaji daga bakin k'ofan falon Areef yace "They are still waiting" Tayi saurin janye jikinta ta fita yana binta a baya, Areef ne ya bud'e mata motan ta shiga, kasa k'arasawa Jamal yayi wajan mota daga chan baya yana d'aga musu hannu. Kasa d'aga masa hannu tayi ta fashe da kuka mara sauti tana binsa da ido har suka bar gidan. Hijab d'in datasa taja gaba ta rufe fuskanta tana kuka a hankali, a haka bacci ya d'auketa cike da kewar mijinta. Ba ita ta farka ba sai da suka shigo cikin binnin taraiya, a hankali ta bud'e ido lokacin da suka iso k'ofar gidan. Gate ne k'ato mai kyawun gaske, masu gadi suka bud'e musu suka shiga ciki. Wajan adana motoci drivern yayi parking. Areefah tace "Kin tashi" Ta gyad'a kai tare da d'an murmushi, Drivern ya fita dasauri ya bud'e ma Abban, Ammi ta fito Suma suka fifito. Bin gidan da Kallo kawai Ummy keyi cike da sha'awa, duk da irin tsaruwan gidan da ta baro anma nesa ba kusa ba nasu Ammi ya fisa komai. Areefah ta d'auko Trolleyn Ummyn da nata tana cewa "Aunty Ummy muje" Ba musu ta soma binta abaya har suka shiga cikin falon gidan. Nan Ummy ta saki baki tana ganin Aljannar duniya, d'aki mai kyawun gaske Ammi ta zab'a mata Areefah takai mata trolleynta ciki. Bayan tayi wanka ta fito kiran Jamal ya shigo wayanta, d'auka tayi ta soma masa shagwab'a, cike da damuwa yace "Baby kin tafi kin barini da kewanki" Ta tura baki kamar yana kusa da ita "To ba kak'i ka biyomu bah" "Ina nan zuwa dana gama abubuwan danake zan zo kinji" Ta gyad'a kai tare da amsawa, sun dad'e suna hira yana mata kalamai masu dad'i sannan sukayi sallama. Mama ta kira suka gaisa ta shaida mata sun isa Abujan, Addu'a ta mata sosai tare da jadada mata ta zama mai biyaiya ga 'yan uwan mijinta. Areefah ce ta shigo da sallama tace ta fito suci abinci, ba musu ta fito dinning d'in dake Falon suka zauna itada Areefah sukaci abinci suna hira gwanin ban shawa'awa. Bayan sun gama Areefah ta zagaya da ita taga ciki da wajen gidan, sosai gidan ya burge Ummy dan nesa ba kusa ba yafi nasu Mami tsaruwa. Da daddare Bilal ya iso dan ya shaida ma Abba zai taho daga baya, d'akinsa na daga chan bq shi kad'ai. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Ummy najin dad'in zaman gidan sosai, kullum sai sunyi waya da Jamal fiye da sau biyar, yakan fad'a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82