Chapter 57
Chapter 57
tazo mana sallama zata makaranta bah" Kasa basu amsa yayi sai kuka yake da wani irin gunji, iya rud'ewa Mami da Aunty Faty sun rud'e dan ba k'aramin abu kesa Jamal kuka bah. Suna nan cirko cirko suka ji k'aran bud'e gate, ba dad'ewa Mifzal ya shigo gidan cikin kakinsa na 'yansanda tare da wasu 'yansandan. Jikinsa ne yayi sanyi ganin Jamal a wannan halin, durk'usawa yayi kusada Jamal ya d'ago kafad'arsa cike da tausayinsa "Its All right Jamal, ka daina wannan kukan pls" Jamal ya d'ago jajayen idanunsa ya zubasu kan Mifzal "Na daina kuka fa kace Mifzal, kasan yanda Ummy take a cikin raina?" Ya fashe da kuka ya cigaba da cewa "Shes My everything Mifzal, ina santa fiye da kaina" Ya kama hannun Mifzal d'in hawaye na gangara daga idonsa "Pls ku taimakeni kada wani abu ya samu Ummy, wallahi ba lafiya gareta bah, shes 3month pregnant, Plss" Duk da dauriya irin na Aunty Faty saida ta fashe da kuka na tausayin halin da Jamal d'in yake Ciki. Mifzal yace "Insha Allahu zanyi iya k'okarina akan wannan case d'in, Komai zaizo k'arshe" Ya mik'e zai bar falon, Jamal yayi saurin kamo hannunsa yana hawaye "Plssss try ur best Mifzal, banasan wani abu ya sameta Pls" Hawaye suka cika idanun Mifzal, cikin zuciyarsa ko mamakin irin san da abokin nasa kema Ummy yake. Murmushin k'arfin hali Mifzal d'in ya masa yace "Insha Allah" Ya bar falon suka d'au mota suka bar gidan a guje. Falon kuwa Mami kuka, Aunty Faty kuka ga kuma uban gaiya Jamal. Kan kace me zazzab'i mai zafi ya rufesa har lokacin kansa na cinyar Mami, nan ta sake rud'ewa, Aunty Faty ta kira doctor yazo dan ya dubasa. Magunguna aka rubuta masa, Aka aika mai gadi ya siyo. Ba yanda Mami da Aunty Faty basuyi akan Jamal yasha magani ba anma kememe yak'i saima k'udundunewa dayayi yana kukansa bil hak'i da gaskiya. *** Ummy bata farka daga nannauyan baccin da tayi ba sai k'arfe uku na yanma, dakyar ta bud'e idanunta da sukayi ja, ganinta a wani d'aki daba nata ba yasa ta bud'e idonta sosai ta yunk'ura ta mik'e dakyar tare da fashe wa da kuka tana bin d'akin da kallo. Kofan d'akin aka bud'e taja da baya dasauri tana kuka, mutanen nan ne dai da suka d'aukota sai dai wannan karan fuskokin su a bud'e yake. "Kyakkyawa har kin farka" Ya soma matsowa inda take tanaja baya, d'ariya yayi mai sauti yace "Ki bani had'in kai 'yanmata, tun wanchan zuwan danayi nake mugun sha'awarki" Jin haka yasa Ummy sake fashewa da wani kukan tana cigaba da ja da baya yana biyota "Dan Allah kuyi hak'uri, karku kasheni Wallahi ban muku komai bah" Dariya mutumin ya sakeyi yace "Ba'a bamu wannan izinin ba tukun, idan har aka bamu to sunanki gawa" Nan da nan jikinta ya soma rawa, maranta yayi wani irin juyawa har saida ta fad'i ta rik'e wajan ta sake rushewa da kuka. Umarni ya bayar da a d'aureta, ihu ta soma tana k'okarin mik'ewa suka maidata zaune, tanaji tana gani aka had'a kafafunta waje d'aya aka d'aure. Suka d'aure hannayenta ya bayanta. Har lokacin bata daina kuka bah tana kiran sunan Allah, wani kyakkyawan Mari mutumin ya d'auketa dashi har saida Bakinta da Hanci suka fashe "Kiyi min shiru, ba'a kiran sunan Allah a nan wajan" Ba shiri ta rufe bakinta taba cigaba da hawaye, kyalle yasa da kansa ya d'aure mata baki tamau ya mik'e ya fita. Wani marayan kuka ta saki ga maranta dake murd'a mata kamar zata mutu. A b'angaren Mifzal kuwa, a fusace yabar gidan, waya yayi abuja ba wani b'ata lokaci ya bada oder a kama masa Alhaji da Bilal da kuka yaransa. Saidai suna zuwa aka tabbatar musu da basa garin sunyi tafiya. Mifzal najin wannan labarin ya sake tabbatar da Bilal ne yayi wannan d'anyan aikin. 'Yan sanda aka baza a unguwan Iyayen Bilal d'in anma ba cikin kayan 'yan sanda bah. Ran Mifzal idan yayi dubu ya tashi musamman idan ya tuna halin da Jamal ke ciki. Waya yayi ma su Ram dasu Taseen ya fad'a musu abinda ke faruwa sannan ya dawo gida wajan Jamal d'in. Har lokacin yana nan kwance kan kujera gaba d'aya ya fita daga haiyacinsa saboda mugun zazzab'in dake jikinsa. Mabrookah na gefensa tana kuka itama cike da tausayin mijin nata. Mabrookah na ganinsa ta mik'e dasauri cikin kuka tace "An ganta?" Baice mata komai ba dan gaba d'aya hankalinsa na kan Jamal daketa rawar sanyi, Mami itama cikin kuka tace "Dan Allah Mifzal ku taimaka, kada Jamal ya shiga wani hali, shi kad'ai ya ragemin" Ta sake fashewa da kuka, inda Jamal d'in ke kwance ya k'araso ya zauna, wayan Jamal d'in ne ya soma ruri Mifzal ya d'auka ganin bak'uwar number ce yasa ya d'auka daga chan b'angaren akace "Jamaludeen Surajo" Dayake ana d'an jiyo magana yasa Jamal mik'ewa zaune ya amsa wajan dasauri ya kara a kunnensa, "Ina fata ina magana da Jamaludeen Surajo neh" Cikin rawar murya Jamal ya amsa masa, Mifzal ya danna speaker Mami da Aunty Faty suka matso kusa "Matarka abin k'aunarka tana tare damu yanzu haka" "Ina kuka kai min matata, ina take? Dan Allah Bilal karka cutarmin da matata, ka fad'i koma menene kakeso zan maka pls" Ya fashe da kuka, wani dariya mutumin ya saki sannan yace "Kai kasan wani Bilal, idan har kanasan matarka sai ka biyamu kud'in fansa Naira Million Hamsin, sannan cash mukeso" Jamal ya d'aga jajayen idanunsa yana kallan wayan "Ina zan samu Naira Million Hamsin Yanzu? Dan Allah kuyi hak'uri ku rage" Sautin kukan Ummy yaji ya k'ara kara wayan a kunnensa hawaye na gangara daga idonsa "Wife! Wife!! Yimin magana pls" Dakyar ta iya cewa "Wayyo Ya Jamal marana mutuwa zanyi" "Me suka miki, Wife talk to me, me suka miki" Amsar wayan sukayi daga hannunta "Jinkirin kawo kud'in shine dad'ewar matarka a wajanmu" "Dan Allah kuyi hak'uri karku cutarmin da ita, i promise you Yau zan baku kud'in" Ding! Suka kashe kiran, Jamal yabi wayan da kallo ya sake fashewa da kuka, Mifzal ne ya amsa wajan ya shiga record ya sake playing maganan Jamal da mutumin, sannan ya tura a wayansa ya d'au numbern. Mami dake chan gefe tana kuka tace "Yanzu ina zamu samu Million hamsin" Jamal ya mik'e dasauri, baya yayi zai fad'i saboda jiri Mifzal yayi saurin rik'oshi "Ina zaka? Ka zauna" "Bani da sauran zama har sai naga matata ta dawo gareni, pls ka kyalleni" Ba musu ya sakeshi ya fita daga falon yayi side d'in Abba. Yana shiga ya haura sama zuwa d'akin Abban, keyn d'akin dama yana attach da keyn motansa, ya ciro a aljihu ya bud'e ya shiga a hankali. Gaba d'aya d'akin yayi k'ura, ya durk'ushe ya sake fashewa da kuka tunawa da Abbansa. Dakyar ya mik'e ya soma bincike bincike anma baiga komai bah. Batsa batsa yayi da d'akin bai samu komai bah sai wani bandir d'in 'yan d'ari biyar guda hud'u. K'asa ya zauna ya sake fashewa da kuka "I'm so sorry Wife, kiyi hak'uri" Ya dad'e zaune a wajan yana kuka, sautin kukanta kawai yakeji a kunnuwansa. Ba shiri ya mik'e tunawa da Jakar da Abba ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82