Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

Ummyn ta soma kwallama kira ta fito tana turo baki "Wani Jamaludeen neh" A shagwab'e tace "Wanda nake aiki gidansu" Daga d'aki Baba yace "Maza kije k'ila an aiko shi ne wajanki" Hijab ta shiga d'aki tasa ta fita tana turo baki, tsaye ta samesa tsaye jikin mota yana sanye da bak'in trouser da farar Tshirt mai mara kauri dan ana Iya Hango singlet d'in jikinshi saboda hasken bulb d'in dake wajan. Kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki ta k'araso wajan ta tsaya chan nesa dashi "Barka da fitowa" yace yana kallanta "Ina wuni" tace kamar ansata dole Murmushi yad'anyi ya amsa mata yana cigaba da kallanta "Nasan zakiyi mamakin zuwana, and nasan zakice na dameki" "Ya Jamal ka fahimceni, inaso na tsiratar da kaina da kuma iyayena daga wulak'anci" Ta d'ago ta kallesa tace "Kayi hak'uri ka daina bibiyata in har kanasan na cigaba da zama a gidanku" Ta nuna kanta tace "Ni nan daka ganni banda k'awa ko aboki, nikad'ai nake rayuwata tun bayan na rasa.... Yayi saurin d'aga mata hannu ranshi b'ace "Ki fad'amin waye ya hanaki huld'a dani? Tel me mana" "Kayi hak'uri bazan iya fad'ama bah" Baice mata komai ba ya zagaya ya shiga motarsa yabar k'ofar gidan a guje. Ummy ta dad'e tsaye a bakin kofan tana bin hanyan da kallo sannan ta shiga gida jiki a sanyaye. Kwanakin da aka bata na cika ta dawo bakin aikinta. Aikin da takeyi da ta cigaba dayi, wani abu daya bata mamaki shine tunda ta dawo gidan magana bai tab'a had'ata da Jamal ba, ko sau d'aya idan ta gaida shi baya amsawa. Hakan baima Ummy dad'i kwata kwata dan cikin wata d'ayan nan ta saba da hiranshi da damunta dayake yawan yi. har saida Laurat ta tambayeta tace bakomai. **** Kimanin wata biyu kenan, yau tana gyara d'akin Mabrookah da safe aka turo k'ofar d'akin, d'an juyowa tayi suka had'a ido da Jamal fuskan nan babu walwala. Aikinda takeyi ta cigaba ya zauna kan bedside dake kusada ita "Ummy abinda kikeyi ya dace kenan" Batace komai ba haka bata juyo ta kalleshi ba "We cant continue like dis, baxan iya jurewa bah. Munyi saba sosai" gyaran d'akin ta cigaba har ta gama yanata binta da kallo "Ummy magana nake kinyi banza dani" Ta juyo ta kalleshi tace "To me kakeso nacema Ya Jamal? Yanda kayi shine daidai" Ya mik'e tsaye ya soma takowa zuwa inda take, gabanta ya tsaya har numfashinta na sauka a goshinta "Nayi miki abinda kikeso saidai na gwada naga bazan iya bah" Kokarin barin wajan take yayi saurin rik'o hannunta, dai dai nan Mabrookah ta shigo d'akin dasauri dan tayi mantuwan littafinta akab gado. Mutuwar tsaye tayi yana kallansu d'aya bayan d'aya shiko gogan ko a jikinsa, kokarin kwacewa Ummy ketayi ta kasa dakyar ta samu ta kwace ta bar d'akin dasauri. Basarwa yayi yace "Sis lapia kika dawo" Dakyar ta iya cewa "Mantuwan littafi nayi" Ya gyad'a kai tareda saka hannunshi cikin pockets ya fita daga d'akin. Da kuka Mabrookah ta d'au waya ta soma neman layin Mami, tana d'auka ta soma fad'a mata tana kuka sosai. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:30 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Ina kuke Masoya Littafin JAMALUDEEN wannan shafi sadaukarwa ce gareku a ko ina kuke. Ina matuk'ar godiya da yanda kuke nuna min k'auna. Allah ya barmu tare Ameen* Page 23 Da kuka Mabrookah ta d'au waya ta soma neman layin Mami, tana d'auka ta soma fad'a mata tana kuka. Fasa zuwa makarantan tayi ta zauna a d'aki tanata kuka cikeda takaici. Da daddare bayan Abba ya dawo Mami ta sanar da Abba abinda Mabrookah ta fad'a mata, murmushi yayi yace "To menene Abin tada hankali Maimuna, karki manta Jamal kowa nasa neh, baida girman kai" "Anma Alhaji yakamata ace an masa magana, ka tuna fah akwai alkawari akansa tunda ya samu lapia sai ayi magana" Jim Abba yayi yana tunani, Mabrookah ta shigo falon fuska ba walwala ta zauna sannan ta gaida shi. Ya amsa yana kallanta da murmushi. Waya ya d'auka ya soma neman layin Jamal, yana d'auka ya sanar dashi yana san ganinshi. Cikin mintina kad'an ya iso falon da sallama ya samu guri ya zauna ya gaida su. Abba ne ya soma cewa "Tambayanka nakeso nayi kuma inaso ka fad'amin gaskiya" Jamal ya d'an d'ago sannan ya maida kai "Menene tsakanin ka da yarinyan nan Ummy" Dam! Gabanshi ya fad'i, ya d'ago suka had'a ido da Mami yayi saurin maida kai ganin yanda take kallanshi "Ba abinda ke tsakanina da ita, kawai mutunci neh" "To mutuncin shima na hana daga yau" cewar Mami tana kallansa rai b'ace "Haba Maimuna, wai meyasa kike haka neh? Menene to dan sunyi mutunci" Mami ta k'ara tsuke fuska tace "Nidai banaso Alhaji, kasan shi talaka bai iya samun guri bah." In banda hararan Mabrookah ba abinda Jamal yakeyi dan yasan ita kad'aice zata kai wannan gulman. "Wannan duk ba magana baneh Maimuna, menene to dan sunyi mutunci a tsakaninsu?" Abba ya girgiza kai ya maida dubansa ga Jamal daketa Hararan Mabrookah ranshi a b'ace "Jamal lokaci yayi daya kamata ka koma bakin aikinka, companyn nan na buk'atar jajirtace kamar kah dan haka har na gama magana monday mai zuwa zaka fara zuwa aikin" "Tho Abba insha Allahu Nagode" Mami ta hard'e hannayenta biyu tace "Tho Alhaji Maganan Alkawarin da akayi wanchan lokacin fah" Abba ya kalli Jamal da Mabrookah "Ku tashi kuje" A tare suka mik'e suka bar falon, Abba yace "Maimuna kina bani mamaki wani lokacin, bai kamata kina irin wad'an nan maganganun bah" "To Alhaji kayi hak'uri bazan sake bah" "Yauwa koke fah, sannan kaganan Alkawarin da kike ki bari sai nan gaba, komai ana binshi ne a hankali" Ta gyad'a kai suka cigaba da hira. Jamal na fita ya shak'e Mabrookah fuskan nan nashi a had'e "Ni kike kai k'ara koh?" "Dan Allah Ya Jamal kayi hak'uri ka sakeni bazan k'ara bah" Kanta ya buga da bango ta saki kuka, yayi saurin sa yatsanshi a lips d'inshi "Shhhh! Karki cika mana kunne, and idan har na k'arajin wani magana saina karya ki a gidan nan Stupid kawai" Ya saketa yabar wajan rai b'ace. Kuka ta fashe dashi mara sauti ta shige d'akinta ta fad'a kan gado. Washe gari Abba da Mabrookah na kan dinning suna breakfast, Mami ta sauko cikeda murna ta zauna kan dinning d'in tana cewa "Yanzu Fatima ta kirani tace suna nan zuwa yau d'in nan itada Zainab" Wani ihu Mabrookah ta saki cikeda murna "Dan Allah Mami dagaske?" Mami ta gyad'a kai, da gudu Mabrookah ta haura sama tana cewa "Ai yau ba kuma zuwa school sai next week" In banda murmushi ba abinda Abba yake, ya mik'e bayan ya gama yace "Na tafi su kuma Allah kawosu Lapia" Mami ta amsa da amin ya fita. Tana cikin breakfast Ummy ta fito daga d'akinta. Wajan da Mami ke zaune ta k'arasa ta tsugunna har k'asa ta gaidata, ba yabo ba falasa ta amsa tana dubanta "Yau munada bak'i suna nan isowa anjima, d'akunan dake sama zaki gyara guda biyu" Ummy ta amsa mata kanta k'asa "Kada ki sake ki shiga hurumin da banaki bah"

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82