Skip to content

Chapter 63

Chapter 63

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

from no where. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:16 AM] ‪+234 706 272 2689‬: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 74 n 75 Gabas da yanma, kudu da arewa ya duba baiga kowa ba sannan ya aje gefen wani bishiya, ya juya ya koma wajan motarsa. K'aran Harbin bindiga yaji from no where. Wani tsale ya doka ya shiga mota dasauri yana haki duk yabi ya tsure, reverse yayi kamin ya juya wata bak'ar mota tasha gabansa. Dam! Gabansa ya fad'i ya soma karato duk addu'ar datazo bakinsa, mutanen nan ne dai masu bak'aken kaya suka tunkaro sa, kiran sunan Allah ya cigaba, d'aya daga cikinsu ya finciko sa daga motan tare da saka masa wani farin yadi a hanci. Luuuu yayi zai fad'i, daya daga cikinsu ya d'aukesa yayi motan dashi, daya ya dau jakan kud'in suka shiga motan suka tada. Mifzal da Ram na tsaye inda ya barsu, Mifzal ya soma kiran Office d'insu dan a turo mai 'yan sanda, bai gama wayan ba yaji k'aran harbin bindiga, ai a d'ari da tamanin suka shiga cikin motan suka bi bayan Jamal d'in. Daga Ram har Mifzal d'in a rud'e suke sai zazzare idanu suke, daga chan nesa suka hango motarsa murfin k'ofan a bud'e. Cikin tashin hankali Ram yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Sun tafi dashi" Baiyi kwakwaran Parking ba ya fito suka k'arasa wajan dukansu jikinsu na rawa. Kuka ne kawai dukansu basu yi bah, Mifzal ya daki Tyre motan Jamal d'in "Damn it!" Dai dai nan sauran 'yan sandan suka k'araso wajan, hotan Motan aka dadd'auka sannan Mifzal ya ciro wajan Jamal d'in dake cikin Motan yana duba last call d'insa duk hankalinsa a tashe. Bari mu koma Gidan Alhaji Surajo. Da safiyar ranar Mami da kanta ta shiga Kitchen ta had'a ma Jamal abin karyawa, koda ta isa side d'in Mabrookah ta samu tana k'okarin fitowa "Aa Mami kece da kanki" Da murmushi Mami tace "Ni ce, Ina Jamal d'in ga Breakfast na masa dan jiya ba abinda yaci" Mabrookah ta amsa Trayn Hannun Mamin tana tab'e baki "Tun Sassafe ya fita inata masa magana bai kulani bah" A rud'e Mami tace "Ya fita kuma? Allah dai yasa ba kiransa sukayi yaje ya samesu bah" Nan da nan Itama Mabrookah ta rud'e jikinta ya soma rawa, lokaci d'aya ta fashe da kuka "Wayyo Mami Allah ya kare Ya Jamal, banaso na rasa shi ina sonshi" Hankalin Mami idan yayi dubu ya tashi, fita tayi a guje ta koma side d'inta, Aunty Faty dake k'okarin saukowa tace "Lafiya dai Maimunatu kika shigo a hargitse haka" Batace mata komai ba ta d'au wayanta ta soma neman layin Jamal d'in, ta kira yafi sau goma bai d'aga bah. Bata ko kalli Aunty Faty ba ta haura sama ta d'auko Hijab da keyn mota ta sauko "Yaya Faty muje, wai meke faruwa?" Cikin k'osawa tace "Kedai Muje" Ba musu tabi bayanta dan akwai mayafi a hannunta. Sukaci karo da Mabrookah tanata musu magana basu tankata bah suka shiga mota suka bar gidan. **** Duk kiran da Mami takeyi wayan na hannun Mifzal kasa d'auka yayi dan baisan mai zaice mata bah. Station d'insu suka koma, ran Mifzal idan yayi dubu ya b'aci, inda Bilal ke kulle ya shiga da kulkinsa a hannu "Wannan shi zai zama warning na k'arshe kuma tambayar k'arshe da zan maka, ina kuka kai Ummy" Gaba d'aya Bilal ya rud'e ganin Kulkin dake hannun Mifzal, ya mik'e daga zaunan dayake dasauri "Wallahi Billahi lazi banga Ummy bah, rabon dana ganta tun kamin a kaita gidan mijinta" Duka Mifzal ya soma kai masa tako ina sai ihu yake yana magiya, Alhaji Ameenu dake Ceil d'in dake kusa dana Bilal gaba d'aya yasha jinin Jikinsa duk ya tsure. Ganin Bilal d'in zai b'ata masa lokaci yasa ya kyallesa ya fito rai b'ace. Ram ya kira suka nufi state CID dasauri. Inda aka aje Barr Ishaq aka kaisu tare da basu report d'in abubuwan daya fad'a musu. Iya rud'ewa Mifzal ya rude bayan ya karanta report d'in, tare da Ram suka shiga d'akin suka samesa zaune. "Barr. Ishaq ashe za'a iya had'a baki dakai ayi irin wannan ta'addancin" Cikin wani irin murya na nadama yace "Dan Allah kuyi hak'uri kumin rai banasan sunanan ya b'aci a idon duniya" Ram ya saki wani malalacin Murmushi "Sunanka ai ya riga ya gama b'aci Barr. Ishaq" Gaba d'aya jikin Barr. Rawa yake yana kallansu. Bud'e kofan d'akin akayi aka shigo da wani dattijo da wasu irin kod'addun kaya. (Saida na k'ura masa ido sannan na gane ashe Alhaji Tijjani neh) Dattijon ya soma kuka yana kama k'asan wandon Mifzal "Dan Allah kuyi min rai Wallahi sharin shed'an neh da kuma talauci. Rud'a na da kud'i sukayi" Takaici ne ya hana Ram da Mifzal magana sai binsu da ido suke. Wani dogon tsaki Mifzal yayi ya fita daga d'akin Ram yabi bayansa. Wayan Jamal d'in ya ciro yana k'ara duba kiran da aka masa k'arshe kafin na Mami, Wife ya gani a rubuce, dasauri ya ciro wayansa ya kira MTN office ya basu numbern dan su duba masa Location d'in wayan. •••• D'akin da Ummy take suka jefa Jamal, tana ganinsa ta sake fashewa da kuka duk da baya fita saboda dishewan da muryanta yayi da kuma tsuman dake rufe da bakinta. Dariya suka soma suna kallanta "Ga mijinki nan sai muga yanda za'ayi ku fita daga hannun mu" D'aya daga cikinsu yace "Ohhh Poor Girl, ji yanda take kuka gwanin ban sha'awa" Jan jiki ta soma har ta k'arasa inda Jamal d'in ke yashe tana cigaba da kuka tana kallansa. Fita sukayi suka barsu a wajan, chan kuma suka dawo shima suka d'auresa kamar yanda suka d'aureta. Jamal bai farka ba sai wuraren k'arfe hud'u na yanma, Sautin kukan Wife d'insa ya ne ya soma shiga kunnensa. Manage This Pls Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:17 AM] ‪+234 706 272 2689‬: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 76 n 77 Jamal bai farka ba sai wuraren k'arfe hud'u na yanma, Sautin kukan Wife d'insa ne ya soma shiga kunnensa. Ba shiri ya mik'e zaune yana kallanta, K'afansa ya kalla yaga an d'auresa haka hannuwansa da bakinsa, girgiza mata kai ya soma alamar ta daina kuka, ya ja jiki ya matsa kusa da ita yana cigaba da girgiza mata kai. Wani kukan ta sake fashewa dashi tana kallansa ganin yanda duk ya rame ya fita haiyacinsa haka itama. Kallan juna suka soma, wasu hawaye suka gangaro masa ganin irin wulak'ancin da akama matarsa ta sunnah. Suna nan manne da juna duk da a d'aure suke hakan bai hanasa lallashinta bah har yasamu tayi shiru. Wuraren k'arfe takwas da rabi na dare aka kawo musu abinci, gabansu ya tura abincin sannan ya fita, mutane biyu suka k'ara shigowa d'akin d'aya ya bud'e ma Jamal baki d'aya ya kwance ma Ummy sannan suka kwance musu hannu. Ogan da kansa ne ya shigo cikin takunsa na iza, Jamal yayi yunk'urin tashi a fusace Wad'an nan mutanen suka ririk'eshi. Ummy ko ta sake fashewa da kuka dan yanzu ya zamar mata kamar ibada. Cikin fad'a Jamal ya

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82