Chapter 41
Chapter 41
takeji. "Ni dai tashi muje kiyi serving d'ina, yunwa nakeji inyaso idan muka dawo sai mu cigaba da karatun tunda naga kinfi fahimtarsa sosai" Kafa ta soma bubugawa a k'asa tana kukan shagawb'a "Ni dai wallahi banaso" Hannunta ya kama yana 'yar dariya suka fito falonta, da kansa yaja mata kujera ta zauna tana cigaba da turo baki. Shi da kansa yayi serving dinsu dan yasan bataci komai ba tana jiransa. Kamar yanda suka saba 'yan watanin nan shi da kansa yake bata a baki har ta k'oshi. Yauma hakan neh, duk abinda sukeyi Mabrookah na hangensu ta wajan staircase tana kallansu. Wani kululun bakin ciki ne ya tsaya mata a wuya, lokaci guda kuma ta fashe da kuka ta sauka k'asa ta koma d'akinta. Bayan sun gama cin abincin, Ummy ta tattara kayan takai kitchen ta wanke ta dawo, A falo ta hangoshi zaune yana kallo, k'arasawa yayi ta zauna tana cewa "Yau bamu je mun gaida Abba bah" "Ai yau a wajansa zan yini harda gobe" Ummy ta jinjina kai ta maida dubanta ga Tv. Wayansa dake hannunsa tayi k'ara ganin suna Abba ne yasa ya d'auka dasauri tareda karawa a kunne "Barka da safiya Abba, to gani nan zuwa" Ya kashe ya maida dubansa ga Ummy "Barinje Abba na kirana" Ta mik'e tana cewa "Yau fa bamuje mun gaida su bah" Ya tako a hankali ya k'araso inda take, k'ugunta ya rik'e da d'an murmushi yace "Nagode da yanda kike nuna damuwarki akan iyayena. I love uh so much" Murmushi ta masa, ya kai bakinsa kusada nata, tayi saurin kuccewa tana dariya "Allah zaki sai Wife" Gwalo ta masa yayo kanta ta gudu zuwa d'aki tana dariya. Kwafa yayi ya sauka k'asa, dakin Mabrookah ya leka ya sameta kwance kan gado tana kuka a hankali, har ya juya sai kuma ya dawo ya k'arasa kan gadon ya zauna tareda d'agota ya had'ata da k'irjinsa "Kukan menene kuma?" Sake rushewa tayi da kuka ta k'ara mak'aleshi sosai "Ya Jamal ina sanka sosai, banasan naga wata na rab'anka. Hakan na damuna. Dan Allah ka soni Wallahi ina sanka" Ya d'ago fuskanta yana share mata hawaye "Haba k'anwata, bar kukan ai duk abinda ke faruwa ke kikaja. Meyasa bakya jin magana nah" Ta turo baki, hancinta ya lakata 'yar murmushi "Its Ok ya isa haka, barin dawo sai muyi magana kinji" Ta gyad'a masa kai ya mik'e ya fita. Ihu ta saki ta fad'a kan gado tana murna, ko ba komai yau ya rungumeta. Waya ta d'auka ta soma kiran layin Aunty Faty, bugu d'aya ta d'auka ta saki k'ara "Shiyasa nake sanki Ummata, wallahi yau har rungumeni yayi" Daga chan b'angaren Aunty Faty tace "Ai bakiga komai bah, indai Jamal ne kin kusa samunsa har abada. Akwai wani magani dana amso wajan wani malami. Kina saka masa a abinci angama" "To Mommy yaushe zaki kawo min" "Ina nan zuwa musamman na kawo miki. Kedai kawai a yanzu ki cigaba da bin shawarata" "Tho Mommy" Hira suka cigaba, Aunty Faty nata kitsa mata abubuwa iri iri na yanda zata janyo hankalin Oga Jamal. *** Da sallama ya shiga d'akin Abban, zaune ya samesa kan gado ya d'aura system a cinyarsa yana wasu ayuka. Kusada shi ya zauna ya gaida shi ya amsa yana kallansa "Abbana gani" Suman kanshi Abba ya shafa yana murmushi "Ina jin dad'in yanda kake tafiyar da aiki a companyn nan, Allah ya maka Albarka" Da Murmushi a fuskansa yace "Ameen Abbana" Abba ya aje System d'in dake cinyarsa ya cire medicated glass d'in fuskansa yace "Na kiraka ne dan muyi wata muhimmiyar magana dakai" Ummy Abduol✍🏻 [3/29, 8:36 AM] +234 701 141 1639: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 45 n 46 "Na kiraka ne dan muyi wata muhimmiyar magana dakai" Gyara zama Jamal yayi yace "To Abba" Abba ya cigaba da cewa "Har yau bazan fasa fad'a maka kayi adalci a tsakanin Matanka bah. Rik'on mata biyu abu ne mai wahalar gaske, saboda kok'arin sauke hak'i. Nasani Mabrookah ba zab'inka baneh, hakan kuma kada ya tab'a saka ka wulak'anta tah." Ya sauke ajiyar zuciya yace "Duk wuya duk rintsi karka rabu da Mabrookah, sannan kayi k'okari ka rik'esu Amana. Karka manta dukansu Marayu ne, babu mai mahaifi a cikinsu" Jamal ya gyad'a kai ya sake sunkuyar da kai k'asa. "Jaleelah yarinya ce ta gari, bani fatan naga abinda zai wulak'antata a rayuwa, saboda 'yar halak ce. Ka rik'eta amana Jamal" "To Abba insha Allahu" Wani Jaka mai kama dana system Abba ya d'auko ya aje a gabanshi yana cewa "Inasan ka ajiye min wannan jakan a wajanka, akwai abubuwa muhimmai a ciki. Dan ina ganin kwanan nan zanyi wani tafiya" Kallan jakan Jamal ketayi ko k'iftawa bayayi "Amana ce tsakanina dakai. Idan Allah ya dawo dani daga tafiyar zan amsa sannan na maka k'arin bayani" "To Abba, anma ina zaka haka" Saida Yayi murmushi sannan yace "Chan wani guri zani, idan lokacin yayi zakaji" Jamal ya jinjina kai tareda jawo jakan gabansa ya ajiye. "Tashi kaje Allah ya maka albarka" Ba musu ya mik'e yama Abba sallama ya koma side d'inshi. D'akinsa yakai jakar ya aje cikin wardrobe ya saka key ya kulle. Yinin ranar Abba da Jamal suna tare, hatta abinci tare suka ci na rana dana dare. Washe gari ma haka, tare sukaje asubah, tare sukayi breakfast. Sosai Jamal yayi enjoying moments d'in, dan Nasihohi sosai ya dunga masa da nunaswa through out the day. Uwargida Ummy tana fito wanka kenan da bayan isha'i Jamal ya shigo d'akin bayan sun dawo sallan Isha'i da Abba, sam bata lura dashi ba sboda towel d'in dake fuskanta tana goge kanta dashi. Karo taji tayi da mutum, ba shiri ta matsa gefe a tsorace. Janyota yayi jikinsa yana k'are mata kallo. Cikin sanyin murya yace "Wife kina horani dayawa. Bakya tausayina koh" Baki ta turo tana kok'arin kwacewa "Dan Allah ka bari" Ya sake janyota jikinsa yana shin shina wuyanta "I badly need uh Wife, Plsss" Bai jira mai zatace ba ya soma kissing d'inta a hankali, biye masa tayi dan tana enjoying duk sanda yake kissing nata. Ganin haka yasa ya janyota suka fad'a kan gado, har lokacin bakinshi na had'e da nata. Hannu yasa yana kok'arin janye towel d'in jikinta tayi saurin rik'e towel d'in tana girgiza masa kai "Plsss...Wife..." Yayi saurin janye towel d'in ta runtse ido hawaye ya gangaro mata, nan da nan ya rud'e ya soma wasa da ita son ranshi. Ba abinda Ummy keyi sai hawaye. K'aran buga k'ofan d'akin neh ya dakatar dashi daga abinda yake. A harzuk'e yace "Wai Waye" Muryan Mabrookah yaji tana cewa "Ya Jamal Mami na kira, gatanan a falo" Ji dayayi Mami ce yasa ya janye jikinsa daga nata, tayi saurin jan Bedsheet ta rufe jikinta tana cigaba da kuka. Gefen fuskanta ya shafa yana murmushi "Ki jirayeni anjima" Ya mik'e dakyar ya fita yana rik'e da gefen maranshi. Mami ya hango a falon a tsaye, Mabrookah na gefenta zaune tana juye juye, a fusace Mamin ta juyo jin tafiyarsa a bayanta "To shanyaye, k'arfe takwas har ka shige d'aki, Jiba nan" Ta nuna masa Mabrookah dake gefenta tanata murd'a murd'e rik'e da cikinta tana kuka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82