Chapter 43
Chapter 43
wajan dake da kansa dake jini, kuka take tana kallansa ba halin taimaka masa. Ummy har lokacin tana hannun d'aya daga cikinsu tana kuka tana fifizgewa. Wani daga cikin b'arayin ya shigo yama Ogan magana a kunne ya fita, chan ya d'aga kai ya dubi agogo sannan ya tako har inda Abban yake tsugunne yace "Kamar yanda na fad'a maka a baya, bama buk'atar kud'inka. Ranka kawai mukazo d'auka" Abba ya zaro ido, Haka Mami dake kusa dashi "Dan Allah kuyi hak'uri kar ku kashe min mijina na rok'e ku" Rarrafowa tayi ta kama k'afan Ogan, yayi kicking nata gefe, Ba Tausayi bare tsoron Allah ya saita Bindigar Hannunshi ya harbi Abban Har sau biyu a ciki. Wani ihu Jamal yayi ya mik'e yana ganin jiri yayi wajan Abban yana kuka sosai, Ummy kuwa luuuuu tayi ta fad'i sumamiya a Wajan. Da gudu b'arayin suka bar gidan suka shishiga motocin su suka gudu. Duk da yanda kan Jamal d'in ke jini ga kuma Jiri dake d'ibansa bai hanasa rungumo Abban ba zuwa jikinsa yana kuka yana girgiza sah. Dakyar Abban Ya iya bud'e idonsa yace "Ka...ka..k..ka Gafar...ce ni d'ana" Ummy Abduol✍🏻 [3/29, 8:36 AM] +234 701 141 1639: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Wannan Page tukuici ce gareku Jamaludeen Fans a ko ina kuke a fad'in duniya* Gaskiya ina matuk'ar jin dadin yanda kuke so na kuma kuke san novel d'ina. Allah yabar zumunci Ameen Page 47 to 49 Dakyar Abban Ya iya bud'e idonsa yace "Ka...ka..k..ka Gafar...ce ni d'ana" Idanun sa suka rufe lufff, wani razananen Ihu Mami ta saki ta k'arasa tareda fashewa da kuka. Tuni Jamal ya fad'i jikin Abban shima ya some Mami duk tabi ta rud'e, Abba da Jamal kawai take jijigawa tana kuka da k'arfin gaske. Kan kace gidan ya cika dank'am da mutane, lokaci guda 'yan sanda suka cika layin. Abulance d'in ABUTH ne sukazo suka d'au Abba da Jamal da kuma Ummy, Mabrookah da Mami suka bisu sai kuka suke dukansu. Masu Aikin gidan babu wanda bai zubar da kwalla bah ganin yanda aka fita da Abba da Jamal. Cikin mintina kad'an suka iso asibitin, direct Emergency akayi dasu, nan likitoci suka duk'ufa akan Abba saidai Ina Rai ya ruga yayi halinsa. Shima Jamal sunyi treating d'insa, tareda suturing wajan saboda kan nasa ba k'aramin fashewa yayi bah. Mami da Mabrookah da kuma sauran mak'ota. Suna bakin k'ofar d'akin cirko cirko, Mami da Mabrookah sun rungume juna sai kuka suke, wasu daga cikinsu na lallashinsu. Jamal aka soma fitowa dashi, kansa nan nad'e da bandeji, Mami tayi kanshi tana tambayan Nurses d'in. Daya daga cikinsu ne ta juyo tace "Yana lafiya lau da ransa" Wani d'aki suka kaisa, sannan suka dawo suka fito da Ummy itama suka kaita d'akin. D'aya daga cikin likitocin ya fito yana cire gloves d'in hannunsa "Doctor yaya mijina, wani hali yake ciki yanzu" Ajiyar zuciya ya sauke ya d'an girgiza kai yace "I'm sorry to say..." Wani chafka Mami ta kaima kwalarsa "No Doctor kar kace min ya mutu" Bai iya cewa komai bah sai kura mata ido dayayi, ta sake fashewa da kuka, Mabrookah ta rungumeta tana kuka sosai, dakyar ta zama hannayenta daga rigan likitan ta fashe da kuka "Allah ya isa tsakanin mu daku, bazan tab'a yafe muku kashe min mijina da kukayi bah" Duk wanda yake wajan sai daya tausaya ma Mami, haka Mak'ota da sukazo tare suka d'au gawan Abba aka maida shi gida. Nan da nan gida ya d'auka da koke koke, Mami duk tabi ta zauce kamar ba ita bah. A cikin daren aka masa wanka. Washe gari kan kace meh gida ya d'auka, daga wurare daban daban sai bulbulowa ake janaiza. Jamal kuwa yana chan kwance har lokacin bai farfad'o bah, haka itama Ummyn. Nurses ne ke tare dasu suna kula dasu. K'arfe Tara na safe Ummy ta farfad'o da kuka, Nurse d'in dake tare dasu ta soma lallashinta, Jamal ta kalla dake kusada gadonta ta sake fashewa da kuka tana kallansa "Ya Jamal! Ya Jamal!!" Jin shiru yasa ta sake fashewa da kuka. Wajan nurse din ta juya "Ina Abba yake?" Saida Nurse d'in tad'anyi Jim sannan tace "Allah ya masa rasuwa" Karaf akan kunnen Jamal lokacin daya farka daga dogon suman dayayi. Ba shiri ya mik'e idanunsa cike da kwalla "Ina Abbana? Ina yake" Ummy ta rungumesa tana kuka "Abba ya rasu" Tureta yayi yace "Nooo!" Ya fad'i wajan guyawu biyu ya fashe da kuka. Daidai lokacin Ramadhan ya shigo d'akin wujiga wujiga, Jamal na ganinsa ya sake fashewa da kuka "Sun kashe min Abbana Ram, sun kashe shi" Duk yanda Ram yaso ga daurewa kasawa yayi ya fashe shima da kuka ta tsugunna kusada Jamal d'in, had'a goshi sukayi suna kuka mai ban tausayi. Ummy dake chan gefe itaba ba abinda take sai kukan. Dakyar Nurse d'in ta lallashe su ta fita dan ta kira likita. Jamal idanunsa na zubar da kwalla yace "An kaisa neh" Ram yace "Aa sai sha d'aya" Agogon d'akin ya kalla yaga goma da kwata, mikewa yayi dasauri ta tumb'uke Drip d'in dake hannunsa "Muje Ram, muje naga Abbana kafin a tafi dashi" Tausayin sa ne ke ratsa Ummy, duk hankalinta na kansa, ba musu Ram ya mik'e ya rik'e hannun Jamal d'in suka fito d'akin Ummy na binsu a baya. Suna shiga layin suka soma hango dandazon mutane, dakyar suka samu aka mamatsa musu suka shiga da motar cikin gida saboda kayan dake jikin Ummyn. Ganin cikin gidan dank'am da mutane yasa Jamal k'ara fashewa da kuka. Dasauri ya fito daga cikin motan, mutanen dake haraban gidan sai kallansa suke, direct side d'in Abban ya nufa yana kuka kamar ransa. A Falon sama ya hango gawansa, Mami da sauran 'yan uwa a gabansa suna kuka wasu na masa addu'a. Wani jiri ne ya d'ebesa yayi baya zai fad'i, Ram dake bayanshi yayi saurin rik'eshi. Har gaban gawan Abban ya kaisa ya zaunar dashi. Kuka kam Jamal yayi shi kamar ba gobe a gaban Abban, mutanen dake wajan ne keta basa baki, dakyar ya iya tsagaitawa ya d'aga hannu biyu yana masa Addu'a hawaye na cigaba da kwaranya daga idonsa. Ya dade yana masa addu'an, ya sake kallansa murya chan k'asa yace "Tafiyan dakace zakayi kenan Abba! Meyasa ka zab'i ka tafi ka barni" Mami ta fashe da kuka jin maganar da Jamal keyi. Dakyar aka d'agasa aka fita dashi daga falon, Ram ya d'iban masa ruwan Alwala ya tasa shi a gaba, kasa yi yayi, Ram da kansa ya masa alwalan ya d'agasa suka koma waje wajan jama'a. Ummy na chan side d'insu tana kuka bayan ta sauya kayan jikinta zuwa dogon rigan atampha. Kuka kam itama tayi har ta gode Allah na tausayin Rayuwarta da kuma na mijinta. Saida tayi mai isarta sannan tasa hijab ta fito zuwa side d'in Abban. Daga chan nesa da gawan ta tsugunna tana kuka tana masa Addu'a. Sai a lokacin ta lura da har su Twins dasu Aunty Faty da Zainab sun iso. Kamar yanda aka fad'a, karfe sha d'aya aka fito da gawan Abba, Aka masa sallah, Sannan aka tafi dashi zuwa gidansa na gaskiya. ``` A daidai nan gab'ar inaso naja hankulan mu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82