Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

uku taba Mama, yadi da shadda taba Baba yanata murna, da kanta takai musu d'inkin, ta biya kud'in. Bata samu shiga gidansu Bilal ba sai dare, ganin kayan abincin da Ummy ta kawo yasa Umman Bilal fashewa da kuka, lallashinta Ummy ta dungayi har Bahar k'anin Bilal ya shigo gidan yana cewa "Umma wannan shekaran ma na rasa, duk inda nake tunanin samun rancen kud'i naje ban..." Kasa k'arasa maganan dayake yayi ganin Ummy dan sai a lokacin ya lura da ita, duk da ya girme mata hakan bai hanashi gaisheta ba, dan murmushi tamai tana cewa "Ni yakamata na gaisheka bakai bah" Murmushi yayi ta gaida shi ya amsa, atampha ta mik'ama Umma shima ta mik'amai Yadi, nan sukaita zuba godiya kamar sun ari baki har saida tayi hawaye. Tambayanshi tayi ranchan kud'in me yake nema yace yasan ya rubuta jamb neh ya koma makaranta, batareda bata lokaci ba tace ya biyota gida ya amsa. Umma ta sake fashewa da kuka, Ummy itama ta saki kuka ta rungumo Umman tana cewa "Ki daina kuka Umma, duk abinda nake muku bazan tab'a biyan Ya Bilal abinda yamin ba a rayuwa" Sun dade suna kuka, Bahar ne yayita basu baki har sukayi shiru, Umma sai sa mata albarka take ta mata sallama Bahar ya biyota dan amsan kud'in. Bayan ta basa yayi godiya ta rok'eshi alfarman ya amso masu Mama d'inkinsu data bayar nan layin bayansu. Batareda b'ata lokaci ba ya amsa mata bayan ya k'ara mata godiya. Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 8:33 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Xaboorah Hapsert* Wannan shafi kacokan taki ce kyauta. Ina matuk'ar godiya Page 16 Batare da b'ata lokaci ba ya amsa mata bayan ya k'ara mata godiya. Koda ta dawo gida abinci Mama ta zuba mata, Tuwon shinkafa da miyar egusi sai k'anshi yake, nan kan tabarma suka zauna a waje suna shan iska kasancewar lokacin zafi neh. D'ibo tuwon Ummy tayi harta kai saitin bakinta Jamal ya fad'o mata a rai, tunani ta soma dan tasan yanzu lokacin cin abincinsa neh, Allah sarki ta fad'a a hankali, dakyar takai loman ta soma taunawa a hankali kamar tana cin magani. Mama dake gefenta tanaba Baba abinci ta kalleta "Ummy lapia, ko bakij dad'in abincin baneh?" Girgiza kai tayi ta kirkiro murmushi "Aa abincin yayi dad'i sosai, Jamal na tuna nasan ynzu lokacin bashi abinci neh" Baba yace "Allah sarki, Allah kenan shiyasa kullum nake k'ara godema Allah dayasa nake ji nake iya magana, kuma nake sauran Alamura na duk da bana gani" Tausayawa Mahaifin nata tayi tace "Insha Allahu Baba zak warke, zaka cigaba da gani kamar yanda kowa yake gani" Murmushin takaici yayi batare da yace komai bah. Labarin abinda ya faru da Jamal rannan ta basu, Mama tace "Anya kuwa ciwon yaran nan baida nasaba da mutanen b'oye" Baba ya gyad'a kai yace "Maganarki abin dubawa ce, saidai zai iya yuwuwa basu d'in baneh kawai dai ya fad'i neh" Itadai Ummy batace komai ba sai kallansu datake. Mama tace "Anma Mallan wannan alamace ai ta cewa akwai su a tare dashi, kasan su mutanen nan basu san suratul Yasin musamman idan sunyi k'amari" Baba ya gyad'a kai yace "Hakaneh maganarki, koma dai basu d'in bane kamata yayi asama masa na gargajiya inaga zaifi na bature" Ummy tayi murmushi tana kallan Iyayen nata yanda suke hira cikeda sha'awa. Washe gari wuraren azahar ta baro gida ta dawo bakin aikinta, kasancewar lahadi ce a falon k'asa ta had'u da Mami itada wasu bak'i, gaidasu tayi ta bar wajan ta shiga d'akinta. Saida tad'an huta sannan tasa uniform ta fito ta shiga kicin. Sun gaisa da mutanen kicin d'in, Laurat ta tareta da fara'a tana cewa "Oyoyo Nannyn Jamal" Duka ta d'akama Laurat d'in da wasa tana cewa "Bakida kirki wallahi" Dariya sukasa duka, Laurat tace "Kinbar Mami da aiki dan naga daga jiya zuwa yau ita ta chanje ki" Ummy tayi murmushi ta d'aga kai tana duba agogon kitchen d'in "Saura minti talatin lokacin feeding d'insa yayi, barinje zamu had'u anjima" Fita tayi ta haura sama zuwa d'akinsa, Yau kaftan ce a jikinsa, brown yadi mai tsadan gaske da santsi, d'inkin yayi fitting d'inshi kamar a jikinshi aka d'inka, sosai yama Ummy kyau sai kallansa take kyaftawa batayi. Muryan Mami ne ya dawo da ita tana cewa "Yauwa Ummy, gwara da kika dawo da wuri dan fita zanyi" Ummy tayi murmushi tace "Dama nayi tunanin wanda zai rik'e aikin kafin na dawo" Mami tace tana k'okarin fita "Babu kowa niketa d'awainiya, nima ga gajiyar aiki" Bata jira mai Ummyn zatace ba tabar d'akin. Coasterd ta dama ta barshi ya huce sannan tasa madara ta soma zuk'a a syringe tana d'ura masa. Haka tai tayi harta gama ta kwace kayan ta fita dasu, yau bata kaisa waje ba dan gudun magana wajan Mabrookah. Kula sosai Jamal ke samu daga wajan Ummy, har wata yar k'iba yayi, Abba da Mami na matuk'ar jin dad'in yanda Ummyn ke kula dashi. Yauma kamar kullum chan garden d'in gidan ta kaisa, tun bayan fitarsu Mami taganshi wani iri har yanayin idanunshi sun chanza kamar da abinda ke damunsa Jikinta ne yayi sanyi ta zuba masa narkakun idanunta tana kallansa, gashi batada waya balle ta kira Mami ko Mabrookah ta sanar dasu halin da ake ciki. Hannu tasa ta tab'a wuyanshi, zafi taji jikinshi yayi sosai, nan hankalinta ya tashi ta rasa yanda zatayi, kitchen ta shiga ta kira Laurat suka fito waje ta baya "Laurat kamar Jamal bashida lapia" "Bashida Lapia kuma? Shida baya magana ya akai kikan baida lapia" cewar Laurat tana kallan Ummyn Hannunta Ummy ta kama sukazo inda yake zaune a garden ta nuna mata shi tana cewa "Kinga yanda idanunsa suka sauya? Kuma jikinshi ma da zafi" Laurat tayi Jim sannan tace "Tho yanzu meye abinyi? Gashi su Hajiya basu nan kuma ni banga wani mai waya a cikin ma'aikatany gidan nan bah" Shiru sukayi gaba d'aya suna kallansa "Abu mafi sauk'i shine ki kyallesa kawai ko ki maidasa d'aki idan Aunty Mabrookah ta dawo sai ki sameta dan naga tana rigasu dawowa" Kai Ummy ta gyad'a Laurat ta koma kicin bakin aikinta. Rasa abinyi tayi ta sake tab'a jikinsa taji ya k'ara zafi fiyeda d'azu. Hankalinta ya tashi nan da nan hawaye suka cika mata ido. Kallanshi kawai takeyi tana chan kuma tace "Sannu! Sannu!! Allah bakay lapia" Ta k'arasa hannu ta tab'a goshinsa tana cewa "Kayi hak'uri kaga ba kowa da an kaika asibiti, Sannu" Tausayinta ne ya mamaye mata zuciya, saitin kunnensa tasa bakinta, Bismillah tayi sannan ta karanta fatiha ta da Qulhuwallahu, Falaq da Nas. Ta tofa masa a jikinsa gaba d'aya. Wani zufa ne ya soma karyo masa, tasa d'an kwalin riganta tana share masa a hankali, Suratul mulk ta soma rerowa a hankali cikin zazzak'ar muryanta tana cigaba da goge masa zufan dake goshinsa. Wangale gate d'in gidan akayi wata had'adiyar red doddge ta shigo ciki tayi parking a haraban gidan. Kyakyyawan saurayi ne bak'i ya fito daga cikin motar sanye da blue gezina sai hek'i take da d'aukar ido. Direct side d'insu Mami ya shiga sallama ya dinga dokawa a falon k'asa, d'aya daga cikin ma'aikatan gidan ce

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82