Skip to content

Chapter 70

Chapter 70

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

k'urama ido sannan ta juya ta kalli Jamal wanda har lokacin Alhaji Ameenu yake kallo. K'ara aka karanto sannan aka umarci Mifzal ya tashi yayi bayani, bayan ya gama Lawyern Alhaji Ameenu wanda d'ansa Areef ya samo masa yayi k'orafi tare da rok'on kotu tabi ma Alhaji Ameenu kadinsa na cin zarafi da aka masa. *A gurguje* Nan kotu tabada umarnin a saki Alhaji Ameenu da Bilal, Ummy dake gefe ta kalli Jamal murya chan k'asa saboda yanda take jin jikinta tace "Ya Jamal kaga wani mai kama dakai" Ya juyaga Areef yana kallansa shima da Mamaki har lokacin gabansa bai daina bugawa bah. Su Mami aka shigo dasu, Ram wanda shine Lawyern Jamal ya mik'e ya soma Jawabi, kasancewar su Mami basu da Lawyer sannan basuyi musu akan laifin da ake tuhumar su ba yasa shari'an baid'au dogon lokaci bah. Mabrookah dake gefe sai kuka take jin Abubuwan da su Mami suka aikata. An d'aga shari'a sai bayan kwana uku sannan a dawo dan Sauraran hukuncin da Za'a yanke ma su Mamin. Mabrookah ta fashe da kuka haka Ummy, Jamal ko hankalinsa ne ya tashi yabar Court d'in dasauri, Mifzal yabi dake k'okarin shiga mota "Mifzal ya duba dan Allah, kada a yanke ma su Mami hukunc...." Mifzal yayi saurin katseshi da cewa "Kana bani mamaki Jamal, matarda batada nufi na alheri a gareka anma kabi ka d'aga hankalinka akanta" Ran Jamal ya b'aci "Wanne irin magana kakeyi Mifzal, kasa...." Mifzal ya shiga mota yaja yabar Haraban Court d'in ransa shima a b'ace. Juyawa yayi a sanyaye ya nufi wajan motansa, yana danna security Mabrookah dake kuka ta bangaje Ummy ta shiga gaba ta zauna. Ummy ta bita da kallo cike da takaici. Har suka isa gida babu wanda yace k'ala, Yana Parking ya fito ya shiga side d'insu daga Ummy har Mabrookah binshi sukayi da kallo. D'akinsa ya shiga ya fad'a kan gado ta fashe da matsanancin kuka kamar k'aramin yaro. Koda Ummy ta haura sama kamar ta shiga d'akinsa sai kuma ta fasa tunawa da tayi itama fushi take. Ya dad'e yana kuka har tsawon wani lokaci, saida yayi mai isarsa sannan yayi shiru ya mik'e ya shiga toilet yayo alwala. Yana fitowa Ya kalli akwatin da ya d'auko ranar daga gidan, sai kallan Akwatin yake ko k'iftawa bayayi, nan ya tuna cewa shine akwatin da Abba ya rubuta masa cewa duk abinda yake san sani game dashi zai samu ciki. Batare da wani b'ata lokaci ba ya janyo jakan ya bud'e a hankali gabansa na fad'uwa. Showel yaci karo dashi da wani overall duk sunyi k'ura, ya d'agasu zai duba sauran abubuwan dake ciki, wasu hotuna nr suka zubo ya sunkuya ya d'auka yana kallo. "Innalillahi wa inna illaihi raj'iun" Shine kalmar daya fad'a yana zare ido duk ilahirin jikinsa na rawa. _Gaisuwa ta musamman ga Jamaludeen Maher_ Ina yinka irin sosai d'in nan. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Wannan shafin Tukuici ce ga *Real Jamaludeen* Ina godiya sosai da bani goyon baya dakake yi, Thank uh so Much Bro Page 87 "Innalillahi wa inna ilaihi raj'iun" Shine kalmar daya fad'a yana zare ido duk ilahirin jikinsa na rawa. Wayansa ya d'auka cikin yanayi na tashin hankali ya soma neman layin Mifzal, saida ya kirasa kusan sau hud'u sannan ya d'auka, dan yayi tunanin zai kirasa ne akan maganan su Mami, cikin muryan kuka Jamal yace "Dan Allah kada ka bari Alhaji Ameenu ya tafi" "Saboda meh" cewar Jamal, Hankali tashe yace "Just do what i said, gani nan zuwa ka jirani a Station" Muryansa ya sake rauni, "Dan Allah karka bari su tafi" Mifzal baice masa komai ba ya kashe kiran sannan ya juya hancin motarsa ya koma Court, bai samesu ba sai 'yan tsurarun motane dake wajan da wasu 'yan sanda, tambayansu yayi a nan d'aya daga cikinsu yake shaida masa yaji suna cewa zasu je Hospital a duba lafiyarsu Alhajin. Jamal kuwa gaba d'aya ya rikice, kaya ya saka ya kinkimi akwatin daya ciro hotunan ya fito, Ummy dake falo ta bisa da kallo da mamaki, ko kallanta baiyi ba ya sauka k'asa yasa kayan cikin mota ya figa a guje yabar gidan. Mifzal ya sake kira ya shaida masa yana Court, direct chan yayi har lokacin hawaye bai daina zuwa daga idonsa bah. Yana isa yayi parking ya fito dasauri "Ka gansu?" Ya girgiza masa kai alamar Aa, Cikin wani irin yanayi Jamal yace "Dole muje Abuja ayau d'in nan Mifzal" Ya kallesa da mamaki, har zai tambayesa dalili sai kuma ya fasa yace "Suna cikin Zaria dan yanzu na tambaya aka shaida min anji suna cewa zasu Asibiti" Jamal najin haka yace "Wat are we waiting for? Mu tafi kawai" Mifzal ya zafga masa harara "Aina zamu fara nemansu" Dai dai nan Ram ya k'araso wajan dan tun d'azu yana cikin Court d'in, Mifzal ne ya masa bayani, Ram yace "Nemansu Abu ne mai sauk'i, na lura d'ansa yanada san asani da kuma nuna isa, Zai iya yuwuwa ABUTH sukaje" Mifzal yayi saurin cewa "Yes u're right" Duk a motar Jamal suka had'u suka d'unguma zuwa asibitin, cikin sa'a suna Parking suka hango su Alhajin sun fito daga asibitin harda Bilal, Jamal ya fita daga motan dasauri ya k'arasa inda suke, "Dan Allah ku tsaya" Dukansu suka juyo suna kallansa, Gaban Alhaji ne ya fad'i ya k'urama Jamal Ido, haka itama Matarsa sai kallansa take ko k'iftawa batayi ga gabanta daketa fad'uwa. Areef d'in Alhaji Ameenu ya juyo a fusace yana kallansa, "Waye kai?, me kakeso" Daidai lokacin Ram da Mifzal suka k'araso wajan, Nan da nan Alhaji Ameenu ya had'e rai haka d'ansa Areef, Areef yana kallansu Mifzal yace "Wai me kukeso damu neh? Inace shari'ar ta k'are? Ko kunzo ne wannan karan ku kamamu duka" Yana maganan yana tada jijiyoyin wuya ransa a b'ace "Na k'yalleku ne kawai saboda Abbana ya hanani d'aukaka k'ara, Ashe haka zama Nigeria yake" Ram ya katsesa da cewa "Babu abinda ya kawo mu, kuma dakake maganar zaman Nigeria, ai babu inda yakaita dad'i ma dan Asalin k'asar. Dan a nan ne kad'ai yake da 'yancin yayi duk abinda yakeso" Jamal yayi saurin d'agama Ram Hannu Alamar yayi shiru, Alhaji Ameenu yace "Ku fad'a mana abinda ke tafe daku dan sauri muke" Jamal ya tsugunna guiwa biyu a k'asa, gaba d'ayansu binshi sukayi da kallo bama kamar Bilal dake gefe yana muzurai, "Sunana Jamaludeen, ku...." Alhaji Ameenu yayi saurin nuna Jamal da yatsa yana cewa "Dama kaine Jamaludeen d"in da ake fad'a?" Ammi dake gefe tace "Shine yayi causing all this Problems" Har Areef ya bud'e baki zaiyi magana Alhaji yayi saurin d'aga masa hannu sannan ya maida dubansa ga Jamal yana cewa "Tunda nake ba'a tab'a cin mutuncina kamar yanda kasa akamin bah" Jamal ya fashe da kuka daga tsugunan dayake, Mifzal sai hararansa yake kamar ya mangaresa. "Abbana ka gafarceni, kayi hak'uri" "Waye Abban naka?" Cewar Areef a fusace Ya d'ago fuska yana kallan Ammi wacce itama tun d'azu shi take kallo "Ammi meyasa kuka kasa rik'eni, kuka zab'i yardani" Babu wanda bai razana a wajan bah, Lokaci d'aya Ammi ta fashe da kuka tana kallan Jamal d'in, Shi

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82